Da maganin ɓera na N100 na kashe Hanifa, inji Abdulmalik Tanko

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ranar Asabar, 4 ga watan Disamban 2021 ne aka sace Hanifa ‘yar shekara biyar a unguwar Kawaji da ke birnin Kano.

Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku da aka fi sani da a-daidaita-sahu, inda ta kwana 47 a wajensu.

Iyayen Hanifa sun ce mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.

Marigayiya Hanifa

“Babu nisa tsakanin makarantar da gidansu (Hanifa), saboda haka yaran sun saba zuwa da ƙafarsu,” a cewar Suraj Zubair, kawun Hanifa.

“Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce ɓarayin sun zo ne a cikin a-daidaita-sahu kuma suka ce za su kai su gida.

Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita.”

To sai dai kuma duk da karɓar wani bangare na Naira miliyan 6 da suka nema a matsayin kuɗin fansa, waɗanda suka yi garkuwa da Hanifa Abubakar sun kashe ta.

Kawun ta, Suraj Suleiman, ya tabbatar da cewa an kashe ta, inda suka gano gawar ta a wata makaranta mai zaman kanta ta naman kaza da ke Tudunwada a ƙaramar hukumar Nasarawa a Kano.

A cewarsa, wanda ya sace ta ya fara kai ta wurin matarsa inda ta yi sati biyu, amma matar daga baya ta ƙi ci gaba da riƙe ta.

“Bayan matarsa ​​ta ƙi ci gaba da riƙe Hanifa, sai ya kai ta Tudunwada inda yake gudanar da wata makarantar mai zaman kanta, sannan ya haɗa mata shayi tare da sanya mata gubar maganin ɓera,” in ji shi.

Abubakar Tanko wanda shi ne shugaban Makarantar NOBLE KIDS kuma wanda ya sace yarinyar ya kuma kashe, ya ce ya ” Na sayo maganin ɓera ne na zuba mata a ragowar shayin da na sha sai na ba ta cikin ɗan lokaci kaɗan ta mutu”

Makashin Hanifa, Abdulmalik Tanko

Tanko da kansa ya shaida wa manema labarai cewa Hanifa ta gane shi ne don haka ya shayar da ita guba ta mutu sannan ya sa wani mai suna Hashim Isyaku ya ɗauki gawar yarinyar ya kai ta harabar makarantar ya binne.

Majiya daga gidan su yarinyar ta bayyana cewa malamin na daga mutanen farko da su ka je jajanta mu su kan sace Hanifa ya na mai zubar da hawaye.

Tuni dai aka tono gawar Hanifa daga inda aka turbuɗe ta aka kai ta asibiti inda likita ya tabbatar rai ya yi halin sa, daga nan aka miƙa ta wajen iyayenta don yi mata jana’iza kamar yadda Shari’ar Musulunci ta tanadar. ‘Yan sanda sun ce bayan kammala bincike za a gurfanar da Tanko gaban kotu.

A halin da ake ciki yanzu dai an cafke Abdulmalik Tanko da abokan tafiyarsa a kusa da titin Zariya a Kano a daren Alhamis da ta gabata, a lokacin da suke ƙoƙarin karɓar kaso na biyu na kuɗin fansa.

Al’ummar da dama a Kano da ƙasa na nuna alhininsu da ɓacin ransu a kan wannan aika-aika. Haka nan a shafukan sada zumunta ma ba a bar su a baya ba, inda ake ta kiraye-kirayen da lallai a ɗauki matakin gaggawa a kan wannan lamari mai cike da rashin mutumtaka, lamarin da ya haifar da samar da maudu’in soshiyal midiya mai taken #JusticeForHanifa.