Da marubuta na da haɗin kai matsalarsu za ta yi sauƙi – Shamsiya Kaduna

“Ba inda muryar rubutu ba ta iya shiga”

Daga AISHA ASAS

Marubuta mata na daga cikin ƙashin bayan duk wani cigaba da aka samu a duniyar rubutun litattafan adabin Kano. Jajircewa da sanin abin da makaranta ke buƙata ya sa suka yiwa maza marubuta da dama zarra, har ta kai ko maza ‘yan uwansu sun fi karɓar rubutun na mata fiye da nasu. Duk da an tabbatar mazan ma ba wai an bar su a baya ba ne, kusan za mu iya cewa, marubuta mata tsintar dami suka yi a kale, kasancewar littafan da aka fi karantawa na rayuwar yau da kullum ne, wadda ta fi yawa cikin gida da zamantakewar aure, kuma za mu iya cewa, mata ne malamai a wannan ɓangaren. Hakan ba zai hana a gwarzanta su ba tare da jinjina wa namijin ƙoƙarin su a duniyar rubutu ba, wadda ba don su ba, da tuni an yi bankwana da ita. Shafin adabi na wannan satin, ya zaƙulo  ma ku ɗaya daga cikin waɗannan marubuta, wadda ta taka muhimmiyar rawa wurin nishaɗantarwa tare da wanzar da tarbiyya a Ƙasar Hausa. Masu karatu, idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Shamsiyya Yusuf Kaduna:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihinki.
SHAMSIYYA: Sunana Shamsiya Yusuf Kaduna. An haifeni a garin Kaduna, kuma na yi makaranta a garin Kaduna.

Wacce shekara kika fara rubutu?
Na fara rubutu a shekarar dubu biyu da tara 2009.

Zuwa yanzu kina da littafai nawa?
Na rubuta littafai guda shida. Su ne; ‘Rayuwar Khadija’, ‘wahalar rayuwa’, ‘Haɗin zumunci’, ‘Safinatu baiwar Allah’, ‘Mummunar fahimta’, ‘Duk abinda yai farko’.

Ya yanayin kasuwancin littafai ta ke a lokacin da kika fitar da littafinki na farko?
A gaskiya lokacin da na fara rubutu rayuwa tana da sauƙi, komai yana tafiya yadda ya kamata, ba kamar yanzu ba, abin dai sai godiyar Allah.

A fahimtarki, me ya janyo mutuwar kasuwar adabin Kano?
Ni dai a tawa fahimtar, zuwan ‘Social Media’ shi ne ya ƙara ruguza kasuwarmu, tun da a da makaranci kai-tsaye zai wuce kasuwa, ya siya, inba nan ba babu inda zai samu, to amma yanzu fa, kana daga kwance za a tura ma ka da kuɗinka ƙalilan, wani ma kyauta ne. Kin ga kuwa dole mu marubuta koda mu na son rubutun dole mu haƙura, idan ba haka ba, ba za ka samu yadda ka ke so ba.

Shin ana gadon baiwar rubutu?
Eh to, zan iya ce mi ki ae, zan kuma ce mi ki a’a, domin shi rubutu baiwa ce, saboda na ga wanda iyayensu marubuta ne, amma kuma ‘ya’yansu babu wanda ya gajesu, shiyasa na ce mi ki baiwa ce.

Wane ne za a iya kira marubuci?
Marubuci shi ne, wanda zai ƙirƙira abu da ƙwaƙwalwar sa, don ya amfanar da kansa da al’umma bakiɗaya, kuma ta hanyar rubutu mutum zai iya isar da saƙo ya je har inda yake buƙata ba tare da wani shamaki ba. A taƙaice, muryar rubutu ba bangon da ba ta fasawa ta shiga.

A marubuta ki na da gwana?
Ai ni duk wanda zai zauna ya ƙirƙiri wani abinda zai amfani al’umma, to ni ya zama gwanina, saboda haka duk wata marubuciya gwanata ce.

Me ya sa ki sha’awar fara rubutu?
Abinda ya sani sha’awar rubutu shi ne; ganin ina da saƙon da zan isar, amma kuma ba ni da hanyar da saƙon zai je, shi ne na ga ya kamata ni ma in ga na dage, na iya rubutun, kuma Allah ya ba ni basirar hakan, don haka ina ma Allah godiya.

Wasu na ganin kamar rashin haɗin kan marubuta ne ya jefa rubutu a wannan kwazazzaben da ya ke ciki. Ko akwai gaskiya a wannan zancen?
Zai iya yiwuwar hakan, inda kai a haɗe yake tun farko, to gaskiya koda za a samu matsala ba za ta kai haka ba, kin san kowa da irin matsalolin sa da suka sha masa kai, sai dai Allah yai mana jagora bakiɗaya.

Ta ya kike samun jigon labari idan za ki yi rubutu?
Ina zama ne, inyi nazari, inga abubuwan da ke faruwa, sai na ɗaura labari a kan hakan.

Wane irin labari kika fi sha’awar rubutawa?
Na fi sha’awar labarin da ya shafi talauci da yadda aka ɗauki talaka ba a bakin komai ba, sai kuma a gaba ya zama komai, domin kuwa Allah shi ne mai azirtawa ga wanda ya so.

Bangon littafin ‘Wahalar Rayuwa’ wanda Shamsiyya Yusuf ta rubuta

Me ya fi ba ki wahala a rubutu?
Abin da ya fi ba ni wahala a rubutu shi ne, bitar sa, kuma wannan ya zama dole, domin mutum ya gyara kura-kuran sa da ya yi. Don haka wannan ne kawai mai ɗan ba ni wahala a sha’anin rubutu.

Wane lokaci ki ka fi sha’awar yin rubutu?
Na fi sha’awar rubutu da daddare, sai kuma bayan sallar asuba, idan na gama karatun Alƙur’ani, sai na ɗan taɓa kaɗan kafin na shiga ayyukan yau da kullum.

Waɗanne nasarori ki ka samu?
Ai babbar nasara a rayuwa itace jama’a, kuma alhamdu lillahi, na samu, kuma an samu abubuwa da dama tafannin rubutu, don haka ba abin da zan ce kan harkar rubutu sai na gode Allah. Abin da kawai ya rage fatan na gama lafiya.

Ƙalubale fa?
Kowacce nasara tana tare da ƙalubale, shi ne ginshiƙin nasara.

Wace shawara za ki ba wa matasan marubuta?
Shawarar da zan ba da Ita ce; a yi haƙuri da juna, a zama tsintsiya maɗaurinta ɗaya. Haƙuri shi ne matakin nasara, sannan kuma a riƙa rubutu mai ma’ana, domin amfanin kai da kuma al’umma bakiɗaya. Alƙalami aka ce ya fi takobi, da shi za ka rubuta alkairi ko sharri. Fatana Allah Ya sada mu da alkairi bakiɗaya.

Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *