Da ni za a riƙa fita farautar ‘yan ta’adda idan na zama Gwamnan Katsina, inji Dikko Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin Jam’iyyar APC Dr. Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa idan ya zama gwamnan jihar Katsina da shi za a dinga fita farautar ɓarayin daji dake kai hare-haren ta’addanci a jihar.

Raɗɗa ya bayyana haka ne cikin wata hira ta musamman da BBC Hausa ke yi da ‘yan takara a matakai daban-daban na siyasa gabanin zaɓen shekara 2023.

“In an yi vuruntu zan fito a tafi ai ɓuruntu da ni,” inji ɗan kararar.

Ya kuma ce akwai abu uku da zai mayar da hankali akan shi wajen shawo kan matsalar tsaro a jihar.

A cewar sa zai ɗauki matasan jihar a kuma basu horo gami da samar masu da kayan aiki don yaƙar ‘yan bindigar da suka addabi jihar.

“A matsayinka na shugaban masu bada tsaro na Katsina, abin da ya kamata mu yi shi ne dole sai mun yi abubuwa guda uku.

“Na farko za mu nemi bayanan sirri daga mutanen da suke zama a inda ake wannan ta’addancin sannan sai mun yi amfani da mutanen mu, ta yadda za mu basu aiki mu horar da su mu siyo musu makamai, saboda za ka ga matasa na neman aikin soji kuma daga yankunan da ake wannan ta’addancin amma ba a ɗaukarsu,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa. “za mu haɗa su da sojoji da ‘yan sanda su yi aiki, za mu siyo musu motoci masu silke za mu ba ma’aikata irin aikin da ya kamata a ba su.”

Raɗɗa wanda tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina ne, tsohon shugaban hukumar bunƙasa manya, ƙanana da matsaikaitan masana’antu na ƙasa kuma tsohon shugaban ƙaramar hukuma ya bayyana cewa ya fito takarar gwamnan jihar Katsina ne saboda tausayawa al’ummar jihar da yake yi don haka ne ya yi alƙawarin fitar da su daga halin rashin tsaro da suka tsinci kan su idan ya zama gwamnan jihar.