Da ni za a yi gwagwarmayar kamfen ɗin Tinubu har sai mun kai ga nasara – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya lashi takobin ganin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya kai ga nasara a zaɓen da ke tafe.

Buhari ya bayyana haka a wajen taron kamfen ɗin Jam’iyyar APC da aka yi a garin Jos, Jihar Filato.

A cewarsa, Shugaba Buhari ya bayyana wa miliyoyin magoya bayan Jam’iyyar APC cewa bai zo garin Jos don ya karanta dogon jawabi ba, ”Na zo ne domin in miƙa tutar APC ga ɗan takarar shugaban ƙasar mu, wanda zai gaje ni, wato Bola Tinubu.

”Jam’iyyar mu ta ɗauki matsaya kuma matsayar ita ce, Tinubu, saboda haka dukkan mu za mu dunƙule mu yi aiki tuƙuru don ganin Tinubu da Jam’iyyar APC sun kai ga nasara. Wannan tafiya ta mu ce duka kuma babu gudu ba ja da bawa, nasara ce kawai a gaban mu kuma ita muke biɗa.”

A jawabinsa, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Adamu Abdullahi ya shaida cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya zarce alƙawuran da ya ɗauka a lokacin da yake neman takarar shugaban cin Nijeria.

”Duka alƙawuran da Buhari ya ɗauka ya cika su cif-cif har ya zar ce yadda ake tsammani.