Da ruwan ciki akan ja na rijiya

Daga SAMINU ALHASSAN

Sanin kowa ne cewa, duk wani ci gaba da duk wata ƙasa za ta samu, yana yin tasiri ne idan ƙasar ta iya cimma nasarar wanzar da rayuwar alummun ta, musamman ta fannin samar da abinci da tsaro, kafin duk wani mataki na inganta rayuwar alumma.

A baya-bayan nan, ɗaya daga muhimman batutuwa dake jan hankulan masharhanta, shi ne yadda yankin kahon Afirka ke fuskantar kamfar abinci, sakamakon fari mai tsanani dake addabar yankin wanda ya haifar da ƙarancin yabanya a gonaki, da kuma farin ɗango da suka addabi yankin a wasu lokuta.

A cewar shirin samar da abinci na duniya WFP, bisa ƙiyasi, mutane miliyan 13 na fama da yunwa a ƙasashen Habasha, da Kenya da Somaliya, yayin da yankin na ƙahon Afrika ke fama da matsanancin rashin ruwan sama mafi muni da yankin ya fuskanta, tun bayan shekarar 1981.

Alƙaluma sun nuna yadda wannan yanki ya fuskanci damina 3 a jere, ba tare da isasshen ruwan sama ba, inda girbin amfanin gona ya yi ƙasa da kaso 70 bisa ɗari idan an kwatanta da na shekarun baya.

Wannan matsala dai na ci gaba da haifar da ta’azarar mutuwar dabbobi, da ƙarancin amfanin gona ga alummu mazauna yankunan da ibtilain ya fi shafa. Tuni kuma shirin na WFP ya fara azamar samar da tallafin abinci mai gina jiki ga ɗumbin alummun yankin.

Yayin da WFP ke shirin ba da tallafi, a ɗaya hannun, akwai buƙatar ƙara mayar da hankali kan matakan daƙile sauyin yanayi, a matakai na ƙasa da ƙasa da na shiyya shiyya.

Ya kamata ƙasashen duniya, musamman masu ƙarfin tattalin arziki su ƙara azama, wajen sauke nauyin dake wuyan su, na tallafa wa ƙasashe masu tasowa, musamman na nahiyar Afirka, da tallafin kuɗaɗen kare muhalli, da muhallin halittu, da daƙile kwararar hamada. Kaza lika su ƙara ɗaukar matakan rage fitar da nauo’in hayaƙi mai gurɓata muhalli. Waɗannan da ma sauran matakai dake ƙunshe cikin yarjejeniyar kare muhalli ta Paris, za su taimaka matuƙa, wajen ingiza nasarar taƙaita mummunan tasirin sauyin yanayi dake addabar sassa daban-daban na duniya, ciki har da yankin na ƙahon Afirka.

A cikin nahiyar Afirka kuwa, kamata ya yi mahukunta sun gaggauta haɗa ƙarfi da ƙarfi, wajen aiwatar da matakan kariya ga muhalli, da dazuzzuka, da ruwaye, da kyautata ingancin iskar. Kafa ganuwar bishiyoyi ta hanyar dashen itatuwa ma, na cikin muhimman matakai da masana ke cewa zai taimaka wa nahiyar Afirka, wajen shawo kan mummunan tasirin sauyin yanayi.

Bugu da ƙari, kamar yadda ƙasar Sin ta sha tallafa wa ƙasashen nahiyar da shawarwarin ƙwararu, da dabarun noma na zamani, da ilimin shuka tsirrai masu buƙatar ruwan sama ƙalilan, kamata ya yi sauran manyan ƙasashen duniya ma dake da kwarewa a wannan fage su bi sahu, wajen ba da gudunmawar su ga ci gaban noman zamani a Afirka, duba da cewa, duk wani ci gaba da nahiyar za ta samu, zai biyo bayan samar da isasshen abinci ne, kamar dai yadda Bahaushe kan ce Da ruwan ciki akan ja na rijiya.