Da Ɗumi-Ɗumi: An sako duka fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Daga BASHIR ISAH

A ranar Laraba aka sako ragowar mutum 23 da ke hannun ‘yan bindiga waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.

Kwamitin Shugaban Ƙasa mai mambobi bakwai ƙarƙashin kulawar Shugaban Rundunar Tsaro, Janar LEO Irabor, shi ne ya shige gaba wajen kuɓutar da fasinjojin.

Cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren kwamitin CDSAC, Farfesa Usman Yusuf, kwamitin ya ce ya cimma wannan nasara ne saboda cikakken goyon bayan da ya samu daga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Kwamitin ya yaba da gudunmawar da ya samu daga dukkanin hukumomin tsaron da lamarin ya shafa da sauran masu ruwa-da-tsaki, sa’ilin da yake ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora masa.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 28 ga Maris, 2022, ‘yan bindiga suka kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu kana aka yi garkuwa da wasu da dama.