Dabarar kawar da matsala sun nuna yadda ake samun ƙauna tsakanin al’umma

Daga BELLO WANG

Nan da ‘yan kwanaki za a ƙaddamar da wasannin Olympics ajin nakasassu na lokacin hunturu a birnin Beijing na ƙasar Sin, inda ƙasar ta ɗau niyyar samar da wani yanayi na kawar da duk matsaloli ga dukkan ‘yan wasa nakasassu na ƙasashe daban-daban.

A cikin wuraren cin abinci da aka gina wa ‘yan wasan, ana iya daidaita tsayin teburori, ta yadda ‘yan wasa masu yin amfani da keken guragu za su iya debo abinci, da cinsu cikin sauƙi. Sa’an nan a ɗakunan kwanansu, an daidaita tsare-tsaren kayayyaki, ta yadda makafi ba za ci karo da wani abu su ji raunuka ba.

Ba don wasannin Olympics kawai ake samar da waɗannan tsare-tsare na musamman ba. Idan ka kewaya a titunan Beijing, za a ga kayayyakin na musamman na sauƙaƙa wa nakasassu. Misali, hanyar da aka keɓe wa makafi, da fitilun da suke iya samar da murya don taimakon makafi tsallake hanya, da dai sauransu.

Ban da kayayyaki, don samar da wani yanayi na kawar da matsala ga nakasassu, ana buƙatar samun taimako daga gwamnati da sassan al’umma. Misali, a nan birnin Beijing, hukuma ta haɗa aikin samar da guraben aikin yi ga nakasassu, da kare fasahohin al’adun gargajiya a waje guda. Inda na ga wasu dimbin nakasassu da suka kama ayyukan sarrafa kayayyakin al’adu da hannu. Ban da wannan kuma, na ga wani nau’in sinima da aka buɗe wa makafi, inda ake yi musu bayani yayin da ake haska fina-finai. Duk waɗannan abubuwa daban-daban suna taka muhimmiyar rawa, a ƙoƙarin samar da wani muhalli na kawar da matsalar zaman rayuwa ga nakasassu.

Na kan tuna da wata tambaya: Shin nakasassu ne kaɗai suke buƙatar wani muhalli mai sauki? Haƙiƙa duk wani mutum daga cikin mu na iya fuskantar wata matsala. Misali, bayan da muka tsufa, ko kuma lokacin da muka ji rauni, mu kan buƙaci samun taimako daga sauran mutane. Saboda haka, aikin nan na samar da wani muhalli maras matsala, wani ƙoƙari ne na kyautata ayyukan kula da al’umma, ta yadda dukkan mutane za su samu sauƙin zama, da jin daɗin zaman rayuwa. Wannan aiki yana ba da tabbaci ga zaman rayuwar nakasassu, gami da tabbatar da ci gaban al’ummar ɗan Adam.