Daga BELLO A. BABAJI
Yayin da aka yi wa ministocin shugaban ƙasa garambawul a kwanaki kaɗan da suka gabata, Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya tabbatar da tsige Ministar Jinƙai, Betta Edu daga muƙaminta.
Kakakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na ‘channels’, inda ya ce an maye gurbinta ne da wani ɗan Filato.
Ya ce, Edu ba ta da gurbi yanzu acikin ministocin Shugaba Tinubu, ya na mai cewa ta yiwa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati (EFCC) ne ta bada bayanai akan ta da ke tabbatar da rashin cantatar ta a kujerar.
A ranar Alhamis ne Tinubu ya naɗa wani Lakcara daga Jami’ar Harkar Noma ta Makurɗi da ke Jihar Benue mai suna Nentawe Yilwatda, inda tuni aka miƙa suanansa da na wasu mutum shida ga Majalisar Dattijai don tantancewa.
A watan Janairun 2024 ne Tinubu ya dakatar Betta Edu kan zargin ta da hannu a tabbatar da cire wasu kuɗaɗe da sanya su a wani asusun kai-da-kai da adadinsu ya kai miliyan N585,198,500.
A baya ne dai Shugaba Tinubu ya yi ta samun kiraye-kiraye na cewa ya tsige wasu daga cikin ministocinsa da suka gaza waje gudanar da ayyukansu yadda suka dace.