Daga ƙarshe, matatar Ɗangote ta bayyana farashin manta

Daga BELLO A. BABAJI

Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da farashin fetur ɗinta wanda ta ce za ta ke sayar da kowacce lita a Naira 990 ga motoci yayin da jiragen ruwa kuma za a ke ba su a N960.

Hakan na zuwa ne bayan da ƙungiyar ƴan kasuwar fetur ta Nijeriya (IPMAN) da takwarata ta masu wuraren sayar da fetur ta Nijeriya (PETROAN) suka ce su na shigo da fetur daga waje a farashi mai sauƙi idan an kwatanta da na Ɗangote inda suka nemi da ya tattauna da masu-ruwa-da-tsaki.

Saidai, matatar ta yi martani da cewa, waɗanda ake shigowa da su ba su kai wanda ta ke samarwa ba inganci.

Jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin man, Anthony Chiejina, acikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce farashin nasu ya ta’allaƙa ne da na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL.

Kuma ya na sayarwa a ƙasa da na NNPCL ga jiragen ruwa wanda ke sayarwa a N971.

Ya kuma ce za su cigaba da ƙoƙarin samar da fetur mai inganci da rahusa wa Nijeriya.

Sannan, ya yi kira ga al’umma da su ƙaurace wa duk wani labari mai ruɗarwa da wasu ke yaɗawa waɗanda suka zaɓi cigaba da fitar da ayyuka tare da gayyato talauci a Nijeriya.