Daga kamfanin Ɗangote muka sayi fetur – Martanin NNPCL kan cewa suna sayar da maras inganci

Daga BELLO A. BABAJI

Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL, ya musanta batun da ke yawo na cewa ya na sayar da fetur mara inganci ga al’umma a farashi mai tsada.

A wata sanarwa da Kakakinsa, Olufemi Soneye ya fitar, kamfanin ya ce ya magantu ne kan wani faifan bidiyo da ke yawo, wanda ke nuna cewa man da ya ke sayarwa ba ya jimawa a yayin amfani da shi.

Rahotonni sun bayyana yadda wani ɗan soshiyal mediya ya yi ikirarin cewa ya sayi lita guda na kamfanin Ɗangote a gidan man MRS a N925 a Alapere dake Jihar Legas da kuma iri ɗaya a NNPC a Ojodu Berger akan N945.

Ya ce, ya gano haka ne a lokacin da ya zuba man a janareta biyu mabanbanta, inda na NNPC ya ƙare a minti 17 yayin da na Ɗangote kuma ya kai minti 33.

Saidai, duk da haka, NNPCL ya ce fetur ɗin da ya ke sayarwa, daga matatar Ɗangote ya sayo shi, ya na mai ƙaryata batun da bayyana hakan a matsayin rashin zurfafa bincike ne ya kai ga haka.

Ya ƙara da cewa, lallai mai da ya ke sayarwa yana da inganci kuma abin karɓa ne ga kwastomominsa, ya na mai kira ga al’umma da su ƙauce wa ire-iren waɗannan zantuka na ƙarya.