Daidai ne mulkin ƙasa ya koma Kudu a 2023 -Zulum

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnan Jihar Barno, Babagana Zulum, ya jaddada kiransa kan batun miƙa mulkin ƙasa ga kudancin ƙasar nan wanda hakan ya nuna goyon bayan gwamnan ga gwamnonin Kudu waɗanda suka haɗe kansu wuri guda suna neman mulkin Nijeriya ya faɗo yankinsu ya zuwa 2023.

A ranar Litinin da ta gabata gwamnonin Kudun suka yi wani taro a Legas inda suka cim ma matsayar cewa idan da adalci da kuma raba dai-dai ya kamata su ma a bari yankinsu ya ɗana shugabancin Nijeriya a 2023 lamarin da Zulum ya ce haka ya kamata.

Zulum ya ce, “Na sha faɗa da kuma nanata cewa, ni Farfesa Babagana Zulum, ina ra’ayin mulkin ƙasa ya koma yankin Kudu 2023 saboda haɗin kan ƙasarmu abu ne mai muhimmancin gaske.”

Zulum ya bayyana haka ne a lokacin da ake tattaunawa da shi yayin wani shirin hantsi a tashar ChannelsTV a Larabar da ta gabata.

Ƙarin dalilai da Zulum ya bayar na cancantar miƙa mulkin ƙasa ga yankin Kudu, sun haɗa da tafiya tare na da muhimmanci a tsarin siyasa, tare da cewa shi ɗan APC ne kuma shekaru 6 ko 7 da suka gabata APC ta amince mulki ya koma Kudu a 2023, don haka ya kamata shugabanci ya koma Kudu.

Gwamna Zulum ya ce gwamnonin Kudun na da ‘yancin su nemi mulki ya koma yankinsu, sai dai ya ce ba daidai ba ne yadda wasunsu ke ra’ayin cewa dole ne shugaban ƙasa na gaba ya fito daga yankin.

“Wannan fa siyasa ce. Kamata ya yi mu haɗu mu zauna a tattauna wannan batu a tsakaninmu,” in ji Zulum.

Daga nan ya yi kira da kada a matsa lamba kan sha’anin shugabancin ƙasa. Yana mai nuna rashin gamsuwarsa dangane da yadda wasu ke wajabta cewa dole mulki ya koma Kudu a 2023.