Dakarun NDLEA sun kama ƙwayoyin Turamol 294,440 a jihohin Bauchi da Delta

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Dakarun Hukumar Yaƙi da Sha da Fatauci da Miyagun Ƙwayopyi (NDLEA) sun cafke ƙwayoyi masu yawan 294, 440 na Tramadol, Diazepam, Swinol, Rohyphnol da Exol-5, haɗe kuma da wasu muggan ƙwayoyin daban a samamen da suka yi a jihohin Delta da Bauchi da kuma filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Ikeja ta Legas.

Jimlar mutanen da ake zargi 41 da ta’ammali da ƙwayoyin aka cafke a yayin farmakin daban-daban, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar,  Femi Babafemi ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi da ta gabata.

Ya ce a jihar Delta, an cafke wani mai suna Christian Onah ɗan shekara 42 a mahaxar Isele zuwa Azagba da ƙwayoyi kimanin 23,160 na Swinol, da 66,000 na Rohypnol waɗanda suke da nauyin kilo 71.6 yayin da suke yin safarar ƙwayoyin daga garuruwan Benin da Edo zuwa Onitsha ta jihar Anambra.

A wani farmakin kuma, an cafke wata motar haya da ta taso daga Onitsha zuwa Ibadan a mahaɗar Abraka ta Asaba a ranar Laraba 2 ga watan Maris da ƙwayoyin tiramadol guda 78,000 da Diazepam guda 5,000 da kuma Exol-5 guda 97,500, tare da wanda ake zargi yana safarar su, Olaniyan Sunday mai shekaru 42 da haihuwa.

“Kana mace da ake zargi cikin wannan badaƙala, Patricia Saduwa, ‘yar shekara 42 an damƙe ta da tabar wiwi mai nauyin kilo 233.7 a yayin farmaki a ƙauyen Orogun kusa da garin Abbi a cikin qaramar hukumar Kwale ta jihar Delta a ranar Juma’a, 4 ga watan Maris. Farmakin, ya kuma cimma wani gida inda aka ƙwace tabar wiwi mai nauyin kilo 123.7 yayin da har yanzu ake ta neman mai wannan kaya na maye.

“A Bauchi kuwa, Dakarun na NDLE, biyo bayan samun wasu bayanan sirri, sun kai farmaki a wata ma’ajiya dake ƙauyen Gadar Maiwa a cikin ƙaramar hukumar Ningi inda aka gano tabar wiwi mai nauyin kilo 542.5 da ƙwayoyin Diazepam guda 6,800, haɗi dana Exol-5 kimanin guda12,400 a ranar Laraba 2 ga watan Maris,” a cewar Babafemi.

Ya ƙara da cewar, a ranar Alhamis 3 ga watan Maris an cafke wani mai suna Olalekan Wasiu Ayinde a rumfar kasuwancin sa da ƙwayoyin Tiramadol guda 4,980, ƙwayoyin Rahypnol guda 600, haɗi da wasu makamantan ƙwayoyi ƙunshe a cikin wake, aka kuma haɗa a cikin kayayyakin abinci da za a yi safarar su zuwa Afurka ta Kudu.

Babafemi ya kuma bayyana cewar, an cafke waɗansu da ake zargi mutum 30 a Unguwar Malali ta cikin garin Kaduna lokacin da dakarun hukumar suke rugurguza rumfunan ta’ammali da kasuwancin muggan qwayoyi a sassan jihar Kaduna.

“Wani mai laifi, Usman Dahiru an cafke shi da tabar wiwi mai nauyin kilo 24 da ya ƙunshe a cikin wasu tsumma, a ranar Alhamis 3 ga watan Maris, akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna,” inji jami’in sadarwar.

Da yake jinjina wa dakarun bisa wannan ƙoƙari, Shugaban Hukumar NDLEA na Ƙasa, Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) ya hore su, da ɗaukacin abokan aikin su da ke sassa daban-daban na ƙasar nan da su cigaba da lura, haɗi da kai farmaki har zuwa lokacin da za a rugurguza duk wata gamayya ko haɗaka ta ta’ammali da safarar muggan ƙwayoyi a dukkan sassan ƙasar nan.