
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar a yanzun nan, ya bayyana cewa, a yanzu haka dakarun tsaro na can a dajin Paula/ dake zango, suna fafatawa da masu garkuwa da mutane, da su ka kai hari, wata makarantar sakandire da ke Kankara a jihar Katsina.
Mai magana da yawun shugaban kasar, ya bayyana cewa an samu nasarar gano inda suke ne, bayan da jirgin rundunar mayakan sama ya yi wani shawagi a dajin. Tuni dai an sanar da shugaban kasa halin da ake ciki a yanzu.
Leave a Reply