Dakarun tsaro sun hallaka wani gungun masu garkuwa da mutane a Kaduna

Gamayya rundunonin mayakan sama da na yan sanda sun kai wani samame kan masu garkuwa da mutane a dajin Kuduru da ke jihar Kaduna. An dai bayyana cewa, an kai samamen ne a jiya, in da sojojin saman, su ka kai wa yan sandan dauki ta sama, a yayin da su kuma yan sandan suka shiga ta kasa, bayan an samu wasu bayanan sirri na mafakar masu garkuwa da mutanen da su ka yi sansani a Kofa da ke cikin dajin.

Samamen da aka kai ta sama, ya yi nasara ne, bayan an tabbatar da bayanan da aka samu na sirri, wanda ke nuni da cewa, wani gungun masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai, sun kafa wani sansani a cikin dajin. Dama dai ana zargin wannan gungun na da hannu a harin da aka kai wa wata tawagar jami’an tsaro a Ngede Allah a kwanakin baya.

Wannan ne ya sanya, bayan samun bayanan da tabbatar da sahihancinsu, ba mu yi kasa a guiwa ba, muka shirya wannan samame na hadin guiwa. Mu ka aika da jirgi guda domin ya kai wannan hari, yayin da runudunar yan sandan ta tashi daga garin Sarkin Pawa, suka bi ta kauyen Tawalli zuwa Kofa in da su ka kai samamen ta kasa. Harin da muka kai, ya yi nasarar hallaka da yawa daga cikin masu garkuwa da mutanen, kuma mun lalata makamansu da dama.  Cewar Manjo Janaral John Eneche, wanda shine jagoran samamen.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*