Dakataccen Kwamishinan Zaɓe, Hudu, zai san matsayinsa ba da daɗewa ba – INEC

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa, dakataccen Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, zai san matsayinsa nan ba da daɗewa ba.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Festus Okoye, shi ne ya sanar da hakan yayin wani shiri da aka yi da shi a tashar Channels Television ranar Alhamis.

Okoye ya ce ‘yan sanda sun kammala bincikensu kan batun, kuma INEC tana da tarin hujjoji gamsassu wanda za ta yi amfani da su a kan Yunusa-Ari a gaban shari’a.

“Ina sane cewa ‘yan sanda sun kammala bincike, haka nan ina sane nan da ‘yan makonni za a sanar da ‘yan Nijeriya abin da zai faru,” in ji Kwamishinan.

Ya ƙara da cewa, doka ta yarje wa INEC ta hukunta shi (Ari) muddin aka same shi da laifi.

Yunusa-Ari ya haifar da ruɗani ne a yayin zaɓen cike gurbin da aka gudanar a Adamawa a ranar 15 ga Afrilu, 2023, bayan da ya sanar da Aisha ‘Binani’ Dahiru ta Jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen alhali ana tsaka da tattara sakamakon zaɓe.

Lamarin da INEC ta ce ba ta yarda da shi ba, tare kuma ɗaukar matakin dakatar da Yunusa-Ari a wancan lokaci, sannan Shugaban Ƙasa na wancan lokaci, Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *