Dakin da babu mai iya zaman minti 45 cikinsa

Daga Umar Mohammed Gombe a Abuja

Duk da cewa kusan kowane dan Adam yana buqatar wurin da babu hayaniya don debe kewa ko samun hutu ko nishadi, amma labarin ya kan sauya da zarar mutum ya shiga cikin wani daki, wanda aka yi ittifaqin ya fi kowane daki shiru a Duniya.

Dakin mafi ban al’ajabi da ake masa laqabi da ‘Anechoic Chamber’ ya kasance ne a birnin Minnesota na Qasar Amurka, wanda wani attajiri Steven Orfield ya gina don aiwatar da gwaje-gwajen fasahar software.

Jaridar Daily Mail ta Amurka, ta ruwaito cewa tsananin shirun dakin ya kai miqdarin maganadisun ma’aunin dBA da ya gaza -9.4, wanda a tarihi har kawo yanzu babu wanda ya taba zama cikinsa fiye da minti 45.

Dakin an gina shi ne da sinadaran da suke kare dukkan wata qara ta duniya ba zata iya kaiwa cikin dakin ba, sannan babu amsa-kuwa, babu kowane irin motsi, don haka idan mutum ya shiga dakin zai riqa jin sautin gudun jinin jikinsa da bugun zuciyarsa da qugin ‘ya’yan hanjinsa da qarar qasusuwan jikinsa idan ya na tafiya saboda tsananin shirun dakin.

“Mun qalubalanci mutane da su zauna cikin dakin na tsawon minti 45, amma babu wanda ya taba iya yin hakan sai mutum daya tal. Saboda kasancewar babu wata qara a dakin, don haka sai kai ne zaka zama qarar, duk abinda yake faruwa a halittarka zaka riqa jinsa kuma da qarfin gaske, saboda haka sai tsoro ya kama mutum ya ruga waje.” in ji Steven Orfield.

Ya ce ba wai ana shigar da mutane don a lallasa su ba ne, an qirqiri dakin ne don yin gwaje-gwajen na’urorin fasaha da nazarin duniyoyi. Haka kuma ya ce kwamfanoni da yawa suna hayar dakin don yin gwajin abubuwan da suka qera.

“Da zarar ka shiga cikin dakin, anan take zaka fara jin sabon al’amari wanda zai yi matuqar wahala ka iya fayyace yanayin. Mafi yawan mutane sukan tsinci kansu a yanayin rudu saboda yadda kunnuwansu ya saba da qararrakin duniya barkatai, amma da yake babu sautin komai a dakin sai qarar jikinka ya dame ka.” in ji Orfield.