Dako za a yi ko limanci?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ai duk makon nan a cike ya ke da batun Imam Nuru Khalid na masallacin Juma’a na ZONE E a rukunin gidajen ‘yan majalisa a Abuja. Lamarin ya fara daga kan dakatar da shi daga limanci zuwa sallamar sa daga limancin da kwamitin masallacin ya yi. Bari mu duba dalilan da su ka jawo waɗannan matakan da su ka taho da sauri. Huɗubar da Sheikh Nuru Khalid ya gabatar a masallacin ya na mai kafa sharaɗi a madadin talakawa ko jama’ar ƙasa cewa ko gwamnati ta gyara tsaro a fito zaɓen 2023 ko in ta gaza ba za a fito zaɓen ba.

Malamin ya ɗora kalaman na sa kan harin da ɓarayin daji su ka kai kan jirgin ƙasa daga Abuja zuwa kaduna inda a ka samu asarar rayuka da ma sace wasu fasinjoji. Farko kwamitin masallaci ƙarƙashin jagorancin tsohon sanata Sa’idu Dansadau ya dakatar da Khalid don abin da Alhaji Dansadau ya zayyana da kalaman da za a iya kawo fitina a ƙasa musamman kan batun kin fitowa zaɓe. A tabaron Ɗansadau rashin fitowa zaɓe mummunan lamari ne da zai kawo illa mai girma ga ƙasa. Ɗansadau ya ce sun dakatar da Khalid ne da ya ke ambata da irin harshen sa ‘HALID’ don sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. Nauyin ya shafi hana zuga jama’a su aikata abun da bai dace ba. Ɗansadau ya ce ya lura Halid na da magoya baya da hakan ya sa maganar sa za ta zama mai tasiri, don haka hana maganar ƙara ƙarfi da sanyawa har ta yi tasiri aiki ne da ya dace a tsaya tsayin daka a kan sa.Tsohon sanatan ya ce ko kaɗan bai damu da sukar da mutane ke yi ma sa a kafafen yanar gizo don ɗaukar matakin ba. Hasalima shi ba ya dau matakin ko ya na aiki ne don mutane su ji daɗi ba amma in har Allah ya amshi aikinsa shikenan.

Yanzu dai ba mu sani ko Allah ya karɓi matsayar Ɗansadau ko kuwa a’a kuma ko hakan ya dace da tanadin shari’ar Islama? Ko ma me za mu ce shi ma Ɗansadau da kan gabatar da darasi a daya daga masallatan anguwar da ma yin limanci wani lokaci, ya kan bayyana a matsayin malami don ya ce har aya ya jaw a Halid a baya don jan hankalinsa kan irin kalaman da ya ke ganin ya na yi da su ka saɓa da usulubin da ya kamata.

Shin dama kwamitin na da niyyar dawo da Sheikh Khalid bayan dakatarwar ko ma dama kwamitin ya gaji da ɗabi’un sa ba za mu iya ɗorarwa ba. Abin da dai ya fito fili shi ne korar Khalid daga limanci bisa dalilin bai nuna sassauci ko nadama da matakin dakatar da shi da a ka yi ba. Takardar korar Halid na nuna kalaman martani da ya yi a kafar labaru bayan dakatarwa na nuna ba shi da niyyar sauya matsaya don haka kamar ba amfanin cigaba da bin sa a hankali ko biyewa batun tattaunawa zuwa sulhuntawa. Aikin gama ya gama kwamitin ya tsige Khalid.

Bayanan bayan fage na nuna akwai zarge-zarge da ba a bayyana ba da a ke tuhumar Khalid da aikatawa. A bakin Ɗansadau dai ya ce ba batun sukar shugaba Buhari ko gwamnatinsa ya sa ɗaukar matakin ba, don Halid ya daɗe ya na sukar gwamnatin. Shi kan sa tsohon sanata Dansadau ya ce akwai kalaman sukar shugaba Buhari da ya furta waɗanda ko shugaban ’yan suka Buba Galadima bait aba fadar irin su ba.

A nan dai Ɗansadau bai kowa misalign sukar shugaba Buhari da ya yi da har ya shallake na Buba ba. Kuma tsarin sa da na Buba ma daban ne. Shi Buba ya tallata Buhari kusan fiye da kowa da lokacin su ka ya yi kuma don aba za a yi tsammanin zai ragarwa shugaban ba. Ɗansadau kuma ya yi majalisar dattawa da kasancewa ɗan siyasa daga jiharsa ta Zamfara. Abun da zan iya tunawa da shi akwai lokacin da Ɗansadau ya nemi shugaba Buhari ya ayyana dokar ta vaci a jihar Zamfara don inganta lamuran tsaro. Hakan zai sa kawar da tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari daga kujerarsa. A gaskiya shugaba Buhari bai amsa wannan kira ba.

Abun da kuma sam yabo ne ba su ka ba ya faru a masallacin na APO a sallar idin azumi na bara inda Ɗansadau ya karɓe abun magana daga Imam Ibrahim Auwal Usama ya musanta cewa gwamnatin Buhari ta gaza inda ya yaba wa gwamnatin da nuna cewa ta ba da lamuni da ya amfani matasa fiye da kowace gwamnati a baya. Ɗansadau ya ce, ko buge shi da gora za a yi a wajen a kashe shi bai damu ba don dama sunnar annabawa ce ko haka a ka yi wa annabawa. Don haka in an hallaka shi kan wannan ra’ayin a lokacin ya yi sunnar annabawa yayin da su kuma tarin masu sallah da su ka yi matuƙar fusata da ra’ayin sa su ka yi ɗabi’ar kafurai irin na zamanin Annabi. Wannan dai ai ba suka ba ne don ko Garba Shehu da Lai Muhammed iya kariyar da za su iya yi kenan.

Wasu masu sharhi da kan bugi jaki su bugi taiki na cewa kwamitin masallacin bai zaɓi lokacin da ya dace na dakatar da limamin ba, wato da kwamitin ya jira batun hari kan jirgin ƙasa ya lafa zuwa bayan azumi sai ya ɗauki matakin don gudun raba kan jama’a mai muni da hakan ya jawo. Hakanan shi kuma Imam Khalid da ya dace ya riƙa tauna irin kalmomin da zai riƙa amfani da su wajen isar da saƙo kasancewar sa malami ko a mumbarin masallaci ya ke magana ko mumbarin kamfen ɗin siyasa ba.

A martanin bayan dakatar da shi Nuru Khalid ya ce, da ya daina furta irin waɗannan kalmomi da ya ce na neman a inganta tsaro ne to gara ya koma yin dako. Da alamu ba sai Nuru ya zama ɗan dako a kasuwar Garki ba don an gan shi a wani faifan bidiyo ya na duba wani babban masallacin da a ka ba shi ya ƙaura can ya cigaba da limancin sa. Kun ga kai tsaye zai cigaba da gashi tuya sai ranar sallah kan kalaman da jagororin masallatai na Apo ke ganin  ba daidai ba ne. Wannan mataki a zahiri ya ma ƙara bunkasa mabiya Halid ne da sanya sunansa ya ƙara tambari. Wanda a baya bai damu da shi ba ma don wataƙila a irin tsarinsa na kowa ya zo a tafi a addini bai kwantawa wasu a rai ba sun dawo su na magana a kansa. Gobarar titi kawai matakin na anguwar Apo ya haddasa don za ka ga har wasu na sanya hoton malamin a shafukan su na yanar gizo da nuna ai gwanin su ne. Kai har raɗeraɗi a ka fara yi a nan anguwar ta Apo cewa a na shirin tsige Ɗansadau daga wannan muƙami don dawo da Halid ɗin na sa kan limanci.

Ta ka iya yiwuwa wani ya yi tunanin ai kwamitin Apo ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa don haka duk abun da ya biyo baya ba komai. Gaskiya da komai don da an yi dogon nazari da ba a buɗe wannan ƙofa ta ƙara shaharantar da malamin da wasu ’yan uwansa ’yan Ahlussunnah ke ganin ya sake hanya da daidaita sahu da ’yan bidi’a. Na taca jin inda marigayi Sheikh Auwal Albanin Zaria ke zaiyana Malam Nuru da rubebben malami a aƙida. A gaskiya Nuru ya sani abokansa na asali mabiya babban surukinsa da ya yi sanadiyyar zuwansa Abuja wato marigayi Sheikh Bawa Maishinkafa sun jingine shi da ɗaukarsa wani garma-garma.

Wannan abun da ya faru yanzu ya karawa Borno dawaki ne ga da’awar Halid kuma da alamu magoya bayan sa za su bi shi duk inda ya koma kuma za su saurari bayanan sa da yin aiki da bayanai fiye da gabanin fatattakarsa daga masallacin na Zone E. Kun ga a baya wasu na sauraron sa ne kaɗai ba tare da sake nazartar abun da ya ke faɗa ba, amma yanzu ba haka ba ne. Shahara ta lamuran dama ko hagu na jiran wani dalili ne qiris shikenan sai duniya ta ɗauka.

Duk wanda ya shiga shafin yanar gizo na Halid zai ga dubban mutane da ke sauraron sa da amincewa da abun da ya ke yi har ma da ma sa addu’ar ‘ALLAH YA KARA LAFIYA’ don ya yi ta zaƙulo kalamai gaba-gadi.

Kammalawa;
Ɗaya daga limaman masallatan anguwar ’yan majalisa a Abuja Imam Ibrahim Auwal Usama ya ce sun yi iya bakin ƙoƙarin su don hana korar babban limamin anguwar Imam Nuru Khalid amma abin ya gagara.

Imam Usama wanda ke tabbatar da labarin sallamar Sheikh Khalid bayan tun farko an dakatar da shi, ya ce kwamitin masallatan ya zauna inda sulhun ya juye zuwa matakin kora daga limanci.

Usama ya ƙara da cewa, da alamun wata waya da Malam Nuru a ka ce ya bugo ya na mai cewa in ba a bar shi ya ja sallah a masallacin a Juma’ar nan ba za a samu tashin hankali, hakan ne ya tunzura kwamitin su ka ɗauki matakin mafi tsauri.

Da alamun dama akwai abubuwa da dama da a ke zargin Malam Khalid da aikatawa da kuma a ke neman dalilin sallamarsa daga limancin.

Duk da haka Ibrahim Usama ya ce, ba za a ce bakin alƙalami ya bushe ba bisa ƙara yunƙurin sulhu amma dai kwamitin ya riga ya yanke hukunci.