Dakta Maryam Ibrahim Shettima: A mahangar gwagwarmaya da kishin ƙasa

Daga BASHIR ABDULLAHI EL-BASH

Tun farkon kafuwar Duniya har zuwa yau, a cikin kowane ƙarni, a ciikin kowace al’umma, a kowane zamani, Allah Ya na fito da wasu mata ‘yan gwagwarmaya da su ke taimakon al’umma, Allah Ya bayyanar da Hajiya Maryam Shetty a wannan zamani namu.

A fannin gwagwarmayar siyasa da ba da gudunmawa ga masu mulki, Hajiya Maryam Shetty ta na kamanceceniya da Sarauniya Raziya Shamsuddeen Iltutmish, wacce ta rasu shakaru 780 da suka gabata. Jarumar Mace ce wacce ta gaji mahaifinta a Birnin Delhi lokacin Indiya da Pakistan na haɗe, ta taimaki shugabancin Mahaifinta a sarari da ɓoye, dukkan yaƙoƙin da Mahaifinta ya fita tana tare da shi.

Ta fuskar taimakon al’umma kuwa, Maryam ta na kamanceceniya da Sarauniya Diana, matar da saboda ɗumbin ayyukan alkhairanta ga al’umma a ke kiranta da suna People’s Princess”, (Sarauniyar Al’umma), kamar yadda a ke kiran Hajiya Maryam Shetty da suna (Sarauniyar Arewa) a wannan zamani namu.

A ɓangaren nemarwa mata ‘yanci kuwa, Dakta Maryam Shetty ta na kamanceceniya da Emmeline Pankhurst, ‘yar gwagwarmaya wacce ta yi fafutukar jare ‘yanci da nemo haƙƙoƙin mata a Ƙasar Birtaniya wacce ta yi rayuwa a Shekarun 1858 zuwa 1928.

Yau Alhamis, 29 Ga Watan July, 2021. A wannan rana na ga dacewar na yi rubutu akan nagartattun mata ‘yan kishin ƙasa waɗanda su ke ba da gudunmawa cikin al’umma kamar Hajiya Maryam Shetty da kuma irin tasirin da su ke da shi a cikin siyasa da harkokin mulki. Kafin na kai ga yin bayani akan wacece Hajiya Maryam Shetty da irin ƙwazonta, zan ɗan yi shimfiɗar bayani akan mata da irin jajircewarsu ga cigaban al’umma tun kafin wannan zamani da mu ke ciki.

Idan mu ka fara yin duba da tarihin musulunci, za mu ga cewa mafi yawan shahararrun malaman da su ka tattara hadisan manzon Allah (S.A.W) a farko-farko mata ne su ka karantar da su. Misali: Ibn Hajar ya ɗauki darasi a wurin mata kimanin 53. Shi ma As-Sakhawi ya yi karatu a wurin mata kimanin 68. Imam Suyuti shi ma ya yi karatu a wurin mata kimanin 33.

Maryam

Akwai ɗumbin manyan mata masu daraja waɗanda tarihin musulunci ba zai manta da gudunmawarsu ba. Misali: Ashifa Bint Abdullahi ta kasance mace ta farko da Khalifa Umar Ibn Al-Khattab ya naɗa a matsayin jami’a mai sa ido kan harkokin kasuwanci. Amra Bint Abdurrahma ita ma ɗaya ce daga cikin manyan Malamai masana hadisi da sauran ilimummuka da kuma ba da fatawa kan lamuran addinin musulunci a cikin ƙarni na takwas.

A zamanin Khalifa Umar Ibn Abdul’aziz ana kallonta a matsayin babbar maruwaiciyar hadisai masu alaƙa da Nana A’isha matar Manzon Allah (SAW). Daga cikin ɗalibanta, akwai: Abubakar Ibn Hazim sanannen mai shari’a a birnin Madina wanda Khalifa Umar Ibn Abdul’aziz ya umarce shi da ya tattara dukkan hadisan da ta ruwaito wuri guda.

Ita ma Aisha bint Muhammad Ibn Abdul Hadi ta kasance malama wacce ta karantar da ɗumbin shahararru malamai a birnin Damascus. Daga cikin malaman da ta koyar sun haɗa da Ibn Hajar Al-Asƙalani babban malami a zamaninta. Sai kuma Fatima Al-Batayahiyya babbar mace ce a ƙarni na takwas wacce ta karantar da ɗalibanta ilimin hadisi a sallacin manzon Allah (S.A.W).

A ƙarni na tara akwai Fatima Al-Fihriyya a Fez na ƙasar Moroko wacce ta assasa Masallacin Al-Ƙarawwiyya a shekara ta 859. Masallacin Ƙarawwiyya wanda ya sanu a tsakanin Larabawa su ke kuma amfani da shi, a Europe ya zama daɗaɗɗiyar jami’a ta farko a duniya wacce ta ke cigaba da amfani har zuwa yau. Ɗalibai su kan tashi daga sassa daban-daban na duniya su je neman ilimin addinin musulunci da na Harsuna da kuma na kimiyya. Fatima Cordoba mai ɗakunan karatu ce (Librarian) a ƙarni na goma wacce ta samar da ɗakunan karatu na jama’a guda 70 masu littattafai 400,000.

Bayan su sai kuma wasu matan waɗanda su ka haɗa da: Abidah Al-Madaniyya, Abdah Bint Bishir, Umma Umar Ath-Thaqafiyya, Zainab jikar Ali Ibn Abdullahi Ibn Abbas, Nafisa Bint Al-Hassan Ibn Ziyad, Khadijah Ummu Muhammad, Abdah Bint Abdurrahman, tare da sauransu waɗanda su ka gabatar da darusan koyar da hadisan manzon Allah (SAW). Tunda farko Abida ta kasance baiwar Muhammad Ibn Yazid. Ta koyi ilimin sanin hadisai sama da guda 10,000.

Zainab Bint Sulayman ‘yar Sarki ce, Mahaifinta ɗan uwan As-Saffah ma’assasin masarautar Abbassid, sannan kuma gwamnan Basrah, Omen da Bahrain a zamanin Khalifancin Al-Mansur. Zainab ta kasance mace wacce ta samu kykkyawan horo da sanin sanin Ilimin hadisi. Sannan kuma ta na daga cikin manyan mata malamai sanannu waɗanda su ka koyar da manyan mashahuran malamai maza.

A ƙarni na goma sha biyu akwai Shuhadah Bint Ahmad Al-Ibri wacce ta yi karatu a Baghdad tare da shahararrun malaman hadisi. Sannan ta kasance babbar malama masaniyar hukunce-hukuncen shari’a wacce ake yi mata laƙabi da “Alfaharin mata”.

Zainab Bint Kamal ta koyar da hadisai sama da guda 400 a wasu daga cikin manyan shahararrun makarantun gaba da sakandire a birnin Damascus. Kuma ta samu ƙauna daga ɗalibanta. Akwai Fatima Bint Muhammad Al-Samarƙandi, masaniyar ilimin hukunce-hukuncen shari’a wacce ta ba wa sananne mijinta shawarwari akan yadda ake yin fatawa.

A baya-bayan nan kuma, a cikin ƙarni na 19, tarihi ya ba mu labarin tashi da nasarar Nana Asma’u a Nageriya; mawaƙiya, malama, sannan kuma mashawarciya ga mahaifinta.

Wasu daga cikin manyan mata waɗanda su ka ba wa al’umma gudunmawa ta fuskar likitanci a tarihin musulunci. Tun farkon zuwan Addinin Musulunci, mata sun samu damar sanin ilimin likitanci da kuma yi wa marasa lafiya maza da mata magani musamman ma a wurin yaƙi.

A zamanin Manzon Allah SAW an samu mace likita mai suna Rufayda Bint Sa’ad Al-Aslamiyya. A lokacin yaƙin Badar ranar 13 Ga Watan Mach, 624 CE ita ce ta yi wa musulmai mayaƙa magani kan raunukan da su ka samu. Rufaida ta samu mafi yawan iliminta na likitanci a wurin mahaifinta Sa’ad Al-Aslami wanda masanin kiwon lafiya ne.

Sai kuma Al-Shifa Bint Al-Ƙuraishiyya Al-Adawiyah, ta kasance ɗaya daga cikin wayayyun mata a wancan lokacin wacce ta ke da ilimin magunguna. Sunanta na asali Layla, amma ta samu laƙabin suna “Shifa” (Waraka).

Bayan ita sai kuma Nusayba Bint Ka’ab Al-Mazneya wacce ta gudanar da aikinta na Likitanci a lokacin yaƙin Uhud. Da kuma Ummu Sinan Al-Islami wacce ita ma ta nemi izinin Manzon Allah SAW ta je wurin yaƙi ta gudanar da aikin yin magani ga waɗanda aka ji wa raunuka da kuma ba da ruwan sha ga mayaƙa.

Sai Ummu Warƙa Bint Harith wacce ta ba da gudunmawa wajen haɗa Alƙur’ani wuri guda, ita ma ta yi aikin likitanci a lokacin yaƙin Badar.

Daɗi da ƙari, akwai Nusayba Bint Al-Harith wacce aka fi sani da Ummu Al-Athia, ita ma likita ce har kaciya ta ke yi sannan kuma ta ba da gudunmawa wajen ba da agajin gaggawa ga mayaƙa a filin daga da kuma tallafa musu da ruwan sha.

Bayan fannin ilimin lafiya, sauran fannonin ilimi ma ba a bar mata a baya ba. Sutayta Al-Mahamili gogaggiyar masaniyar ilimin lissafi ce da adabin Larabci da hadisi da sanin hukunce-hukuncen shari’a.

Sutayta ta taso a gida na ilimi a birnin Baghadad ta rayuwa a tsakiyar ƙarni na 10. Ta samu yabo daga manyan malaman tarihi kamar su: Ibn al-Jawzi, Ibn al-Khatib Baghdadi da kuma Ibn Kathir.

Ayesha ‘ya ce ga Prince Ahmed na Andulus wacce ta rayuwa a ƙarni na 11 gwana ce a fannin Ilimin Rhyme da Oratory. Sannan Labirare ɗinta ya kasance ɗaya daga cikin ƙayatattun labirare cikakku a masarautar Andulus.

A fannin fasaha da zane mai kyau akwai Thana, baiwa a gidan Ibn Ƙayyum. Sai kuma Rasa a ƙasar Indiya wacce ta wallafa littafi kan magunguna da kulawa da mata. Sai kuma Mariyah Al-Ƙibtiyya ‘yar ƙasar Masar wacce ita ma ta yi wallafa a ƙarni na bakwai. Wata ƙwararriyar a fannin ilimin kimiyya ita ce Al-Ijiliyyah Bint Al-Ijili Al-Asturlabi wacce ta bi sahun aikin mahaifinta na kimiyya a birnin Aleppo a Arewacin Siriya a ƙarni na 10. Kaɗan kenan daga cikin manyan mata masana da aka taɓa yi a tarihin Duniya.

Hatta Manzon Allah (S.A.W) ya samu nasarar yaɗa addinin musulunci da gudunmawar mata iyalinsa. Matarsa Nana Khadija gawurtacciyar ‘yar kasuwa ce wacce Allah Ya azurta da tarin dukiya. Nana Khadija ta taimakawa manzon Allah (S.A.W) da gudunmawar kuɗin gudanar da da’awa da gudunmawar shawarwari da gudunmawar kykkyawar ɗabi’a tare da ƙarfafa masa gwiwa kan aikinsa na isar da saƙon Allah (Manzanci).

Daga cikin mata waɗanda su ka yi sarauta kuwa, tarihi ba zai manta da :Arwa Al-Sulayhi a Yemeni ba, wacce ta shafe tsawon shekaru 71 akan karagar mulki a (ƙarni na 11) ana yi mata laƙabi da “Noble Lady”.

Sai Sultana Shajarat Al-Durr wacce ta karɓi jagoranci ƙasar Egypt bayan rasuwar mijinta a (ƙarni na 13).

Da kuma Dhayfa Khatun wacce ta ke mata ce ga ɗan gidan Salah Al-Din Al-Ayyubi. Ta zama Sarauniyar birnin Aleppo na tsawon shekaru 6 bayan rasuwar ɗanta Sarki Abdul’Aziz.

Sarauniya Dhayfa ta fuskanci yaƙoƙi daga rukunonin mayaƙan addini waɗanda su ka haɗa da: Khuarzmein, Mongols da kuma Seljuks. Daɗi da ƙari a tsarin gudanarwarta ta al’umma da siyasa, ta ɗauki nauyin Ilimi a Aleppo inda ta gina makarantu guda biyu.

Sai kuma Sitt Al-Mulk ‘yar Sarkin Fatimid daga ƙasar Egypt ƙwararriyar mai gudanar da harkokin mulki bisa tafarkin addinin musulunci.

Sai kuma Razia Sultana mace ta tarko da ta taɓa zama akan karagar sarautar India a birnin Delhi har tsawon shekaru 4 a cikin (ƙarni na 13).

Firishta wani marubucin tarihi ne a ƙarni na 18 ya bayyana Sarauniya Raziya da cewa “mace ce mai kan maza da zuciya irin ta maza wacce ta fi ‘ya’ya 20”.

Bayan waɗannan sai kuma Hurrem Sultan (1500CE) wacce ake kira da suna Roxelana, asali baiwa ce wacce aka bautar a (Crimean Turks Raids) a ƙasar Ukraine a zamanin Yazuz Sultan Salim sannan aka gabatar da ita a fadar Ottoman ga sarki Suleyman wanda daga baya kuma ya aure ta.

Maryam

Sarauniya Hurrem Sultan ta assasa manyan makarantu da dama waɗanda su ka haɗa da masallatai da gidajen wanka na maza da na mata da makarantu guda biyu da asibitin mata a birnin Istanbul sai kuma wasu makarantun guda huɗu a birnin Makkah da kuma masallaci a Jerusalem.

Sai kuma Amina A Nageriya wacce ta yi sarautar birnin Zazzau a (ƙarni na 16) a lokacin ta na ƴar shekaru (16).

Sarauniya Amina ta zaɓi ta koyi dabarun yaƙi da kuma jagorantar rundunar mayaƙa a ƙasar Zazzau. A tsawon mulkinta na shekaru 34 ta faɗaɗa ƙasarta ta zama babbar ƙasa mai girma da faɗin gaske.

Sarauniya Amina ta ba da umarni an gina katangun kariya a duk sansanin sojoji. Daga baya garuruwan da ke wurin katangun sun samu cigaba da bunƙasa kuma har yau wasu daga cikinsu su na nan su na cigaba da kasancewa ana kuma kiransu da Katangun Amina.

Tarihin gwagwarmayar rayuwar Emmeline Pankhurst, ‘yar gwagwarmaya wacce ta yi fafutukar kare ƴanci da kuma haƙƙoƙin mata a ƙasar Birtaniya wacce ta rayuwa a tsakanin shekarun (1858 zuwa 1928).

An haifi Emmeline Goulden Pankhurst a birnin Manchester na ƙasar Ingila a ranar 14 ko 15 ga watan Yuli, 1858. Bayan da ta taso, Emmeline ta yi karatunta a ƙasar Faransa. Mahaifanta gaba ɗaya ‘yan siyasa ne, kuma mutane ne masu ra’ayi da gwagwarmayar nemowa mata ‘yanci da damar yin zaɓe a ƙasar Ingila. Tun ta na ‘yar shekaru (14) da haihuwa a duniya mahaifiyarta ta taɓa zuwa taron tattauna nemawa mata ‘yancin yin zaɓe da ita.

A shekarar 1903, Emmeline ta kafa wata ƙungiyar siyasa ta mata zalla mai suna (Women’s Social and Political Union), kan nemowa mata ‘yanci da damar kaɗa ƙuri’a a zaɓe, wanda kuma a sanadiyyar wannan gwagwarmaya tata an sha kama ta a lokuta daban-daban ana tsare ta a gidan kurkuku. Sannan kuma a sanadiyyar wannan gwagwarmaya tata, majalissar Birtaniya ta samar da taƙaitacciyar dokar ba wa mata damar kaɗa ƙuri’a a shekarar (1918)

Emmeline ta faɗa harkokin siyasa bayan da mijinta ya nemi zama ɗan majalissa wanda bai kai ga yin nasara ba, a wannan lokaci ta yi wa mijinta yaƙin neman zaɓe inda ta kasance ta na haɗa gangamin taron siyasa a gidanta.

A shekarar 1905 ‘yar Emmeline mai suna Christabel da kuma wata memba a ƙungiyar WSPU mai suna Annie Kenny sun shirya wani taro na musamman domin duban jam’iyyar Liberal ko za ta goyi bayan ba wa mata damar yin zaɓe. Amma bayan arangama da su ka yi da jami’an tsaro na ‘yan sanda sai aka kame mata masu yawa daga cikin ƴan fafutukar. Wannan kamu ne kuma ya ƙarawa Emmeline ƙarfin gwiwar cigaba da ƙarawa ƙungiyarta ƙarfi domin cigaba da gwagwarmayar nemawa mata ‘yancin yin zaɓe.

A shekarar 1910 an daƙile samar zartar da dokar ba wa mata ‘yancin yin zaɓe, inda kuma mata da dama su ka shiga yajin cin abinci a cikin gidan kaso ciki har da Emmeline sannan kuma a shekarar 1913 aka ba da damar fitar da fursunoni masu fama da rashin lafiya tare da dawo da su bayan sun warke daga bisani kuma aka sake su bayan yajin cin abinci. Inda a shekarar 1914 Emmeline ta ziyarci ƙasar Amurka domin gabatar da jawabi.

A lokacin yaƙin duniya na ɗaya Emmeline ta ƙarfafi gwiwar mata wajen shiga yaƙin, kamar yadda ta ke cewa “mun zo wannan wuri ba wai don mun kasance masu karya doka ba, sai domin mu kasance masu tsara doka”.

Wannan gudunmawa da mata su ka bayar a yaƙin duniya na ɗaya, shi ne ya ja hankalin gwamnatin Birtaniya ta zartar musu da taƙaitacciyar dokar da ta ba su damar yin zaɓe ga mata ‘yan shekaru 30 kawai inda daga bisani kuma aka sake basu cikakkiyar dama da kuma damar tsayawa takara a zaɓe su a matsayin ƴan majalissun dokoki na Birtaniya.

Princess Diana wacce ta rayu a tsakanin shekarun (1961–1997), matar da ta yi ƙaurin suna ta kuma shahara a ƙasar Birtaniya da Duniya gaba ɗaya kan ayyukan jin ƙai da taimakon yara ƙanana da al’umma gaba ɗaya.

An haifi Diana a yankin Sandringham na ƙasar Ingila a ranar 1 ga watan Yuli, 1961. Ta fara karatunta a makarantar Riddlesworth Hall, daga nan ta wuce zuwa makarantar West Health. Princess Diana ta kasance ma’abociyar son kaɗe-kaɗe da raye-raye, ta samu laƙabin Lady Diana Spencer bayan da mahaifinta ya gadar mata da laƙabin a shekarar 1975.

Princess Diana ta kasance mai matuƙar ƙaunar yara, wanda hakan ne ma ya sanya bayan da ta kammala karatu a makarantar Alpin Videmanette a ƙasar Siwizland, ta wuce zuwa birnin Landan na ƙasar Birtaniya ta fara aiki da yara, sannu a hankali ta zamto mai hidima da taimakon yara a masarautar Ingila.

Princess Diana ta rasu da sanyin safiyar ranar 31 ga watan Ogas na shekarar 1997 a asibitin birnin Faris na ƙasar Faransa a sanadiyyar haɗarin mota biyo bayan jikkatar da ta samu a ya yin hatsarin. Ta rasu ta na da kimanin shekaru 36 da haihuwa a Duniya.

Mutuwar Princess Diana ya yi matuƙar jijjiga al’umma a duk duniya, saboda ɗumbin ayyukan da ta ke yi na taimako da jin ƙan mutane.

A cikin jawabin jimamin rasuwar da ta gabatar a gidan talabijin, sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth ta II ta bayyana alhininta da cewa “babu wani mutum da ya san Diana da zai iya mantawa da ita. Miliyoyin al’ummar da ba su taba ganinta a zahiri ba, amma su na jin labarinta ba za su taɓa mantawa da ita ba. Rayuwarta abar koyi ce ga sauran al’umma”. Inji Sarauniyar Ingila.

Bayan rasuwar Diana, an yi mata laƙabi da “People’s Princess”, wato ma’ana (Sarauniyar Al’umma), saboda ɗumbin ayyukan alkhairin da ta yi na taimakon al’umma wanda kuma ya game duniya gaba ɗaya a lokacin rayuwarta.

A wani rahoton bincike da aka fitar, tsakanin Maza da Mata su waye su ka fi cancanta su shugabanci Al’umma a tsarin shugabancin Siyasa ?

Idan mu ka yi nazarin waɗanda mata da ɗumbin gudunmawar da su ka bayar ga al’umma za mu fahimci cewa ba shakka mata sun cancanci samun kowacce irin kujerar siyasa. Kuma ko da a sakamakon wani rahoton bincike da aka fitar ya nuna cewar kashi shida (6%) na mutane (2,250) da aka ji ra’ayinsu sun bayyana cewa mata sun fi cancantar su zama shugabannin siyasa fiye da maza.

Sannan mutum ɗaya cikin mutane biyar, kashi (21%) sun bayyana cewa maza sun fi mata cancantar zama shugabannin siyasa. A ra’ayi na bai ɗaya kuma, kaso sittin da tara (69%) sun bayyana cewa babu bambancin kwaliti ta fuskar cancantar shugabancin siyasa a tsakanin maza da mata, gaba ɗaya ƙwalatinsu ɗaya ne maza ba su fi mata ba, mata ma ba su fi maza ba. Ba shakka mata sun yi an ga irin ƙoƙarinsu kuma an tabbatar da za su iya, kamar yadda mu ke ganin ƙoƙarin Hajiya Maryam Shetty a wannan zamani a Nijeriya.

Hajiya Maryam Shettima wacce aka fi sani da (Maryam Shetty) jajirtaccjyar ƴar siyasa ce, maca ce mai kamar maza, shahararriyar ƴar gwagwarmaya wacce ta yi fice akan temakon al’umma da ƙoƙarin sanya ƙwarin gwiwa da kishin ƙasa a cikin zukatan ƴan Nageriya.

A fannin ilimi kuwa, (Maryam Shetty) ta yi fafutukar neman ilimi tun daga tushe a fannoni daban-daban na ilimi inda ta kai ga samun nasarar kammala karatun digirin-digirgir a (Jami’ar East London) a ƙasar Ingila. Ta samu ƙwarewa ta ƙololuwa a fannin kula da lafiyar mutanen da su ka samu raunuka (Physiotherapy). Ta yi aiki da tawagar ƙwararru masu kula da lafiyar ‘yan wasa na tawagar ‘yan wasa Olamfic na ƙasar Ingila tare da gogagge, kana babba wanda ya taɓa riƙe kambun ƙwarewa na duniya Jamaica’s Usain Bolt.

Hajiya Maryam ta kuma samu takardar shaida zama jami’a mai wayar da kan al’umma dangane da zaman lafiya da kaucewa tarzoma bisa turbar Dakta Martin Luther King Jr daga Jami’ar Emory ta ƙasar Amurka. Ta kuma samu nasarar lashe gasa da takardar shaida akan tsare-tsaren ayyukan gwamnati a ƙarni na 21 daga jami’ar Virginia. Kuma ƙwararriya ce masaniya akan harkar yanar gizo da na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Hajiya Maryam ta na kuma da gogewar aiki da asibitoci da cibiyoyin samar da cigaba na duniya shirin lafiya na gidauniyar UKAID da kuma asibitin fadar shugaban ƙasa da tsarin kula da lafiyar yara.

Maryam

Hajiya Shetty ta kuma gudanar da ayyuka da dama na jinƙai da temakon al’umma da cigaban ƙasa. Ta jagoranci aikin sabunta makarantu a Jihar Kano a ƙarƙashin manhajar tallafi ta (#GivingBack initiative).

A saboda himma da ƙwazonta na kishin ƙasa, Hajiya Shatty ta samu damar wakiltar Nageriya a zauren majalissar ɗinkin duniya a ƙarƙashin kwamitin daidaito da adalci gami da yaƙi da cin hanci da rashawa. Sannan kuma a siyasance an saka ta a kwamitocin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa a shekarar 2019. Daɗi da ƙari, memba ce a ƙungiyar matasan jam’iyyar APC na ƙasa.

Hajiya Maryam Shetty, yanzu haka ta na da ƙungiyar da ta samar da kanta mai suna mun yi imani (#Weblieve) domin ƙoƙarin ganin ta sanyawa ƴan ƙasa kishin ƙasarsu da fatan samar da shugabanci nagari da ‘yan ƙasa nagari da ɗabbaƙa zaman lafiya da haɗin kai da temakon al’umma musamman matasa da raunana tare da sanyawa mutane ƙwarin gwiwa su ji cewar za su iya zama nagartattu manyan mutane a wannan ƙasa ta fannoni daban-daban. A saboda wannan himma tata ta kishin ƙasa da cigaban al’umma mutane da dama su ke kiranta da suna “Sarauniyar Arewa” (North’s Princess).