Dalar Amurka, kaskar da ke shan jinin tattalin arzikin duniya

Daga LUBABATU LEI

Domin neman daƙile matsalar hauhawar farashin kayayyaki a gida, babban bankin ƙasar Amurka (FED) ya ƙara ruwan kuɗin ajiya da kaso 0.75% a kwanan baya, sau uku a jere ke nan da ya ƙara ruwan da wannan kaso a shekarar da muke ciki.

Sakamakon matsayin dalar Amurka a tsarin harkokin hada-hadar kuɗi ta duniya, matakin da FED din ya ɗauka ya sa darajar dalar Amurka ta ƙaru a kan sauran kuɗaɗe, baya ga kuma farashin kayayyaki ya ƙaru a duniya, matakin da kuma ya juya matsalar hauhawar farashin kaya da take fuskanta a gida zuwa sauran ƙasashe da shiyyoyi.

An ce, tun bayan ƙaruwar darajar dalar Amurka a wannan shekara, darajar kuɗaɗe 36 a sauran ƙasashen duniya ta ragu da a ƙalla kaso 1/10. Misali a nahiyar Afirka, darajar kuɗin Rand na ƙasar Afirka ta Kudu ta ragu da kashi 9.4%, yayin da darajar Pound na ƙasar Masar ta sauka da kashi 18%.

A ƙasar Ghana ma, ko da yake ta riga ta daga ruwan kuɗin ajiya zuwa kashi 22% don tinkarar matakin ƙasar Amurka, duk da haka, darajar kuɗin ƙasar na ci gaba da raguwa.

A Nijeriya da ta fi ƙarfin tattalin arziki a Afirka, yawan hauhawar farashin kayayyaki ya kai kaso 19.64% a watan Yuli, baya ga kuma adadin ya hau kaso 20.52% a watan Agustan da ya wuce, wanda ya kai wani matsayin ƙolin tun bayan watan Satumban shekarar 2005. Abin da kuma ya biyo bayan matsalar hauhawar farashin kayayyaki shi ne dakushewar tattalin arziki, bisa rahoton hasashen tattalin arzikin Afirka na shekarar 2022 da bankin raya Afirka ya fitar a kwanan baya, an yi hasashen bunƙasuwar tattalin arzikin Afirka da kaso 4.1% a wannan shekara, wanda ya faɗo ƙasa kwatankwacin kaso 6.9% da aka samu a shekarar 2021.

Ta hanyar saka matsalar hauhawar farashin kaya ga sauran ƙasashe, matsalar da Amurka ɗin take fuskanta a cikin gida ta sassauta, duk da cewa hakan ya faru ne sakamakon hasarorin da sauran ƙasashe suke biya ta fannonin matsalar hauhawar farashin kaya da taɓarɓarewar tattalin arziki, lallai abin da mai iya magana kan ce, “Amurka ke ciwo, amma ta sa sauran ƙasashe su sha magani.”

A haƙiƙa dai, tun bayan ƙarshen yakin duniya na biyu, Amurka ta sha yin amfani da ƙaƙƙarfan matsayin dalar Amurka a duniya wajen kwatan arzikin sauran ƙasashe da ma saka matsalolinta gare su.

Tamkar dai wata kaskar da ke jinin tattalin arzikin duniya ne, yadda Amurka ke amfani da dalarta wajen kwace dukiyoyin al’ummun sauran ƙasashe.

Hanya mafi kyau wajen daidaita wannan matsala ita ce, a rungumi manufar kiyaye kasancewar ɓangarori daban daban, wato kamata ya yi ƙasa da ƙasa, musamman ma ƙasashe masu tasowa su tsaya kan aiwatar da hadin gwiwa a tsakaninsu, wajen kafa wani tsarin hada-hadar kuɗi mai inganci da ke ƙunshe da kuɗaɗe na ƙasashe daban daban.

Mai Zane: Mustapha Bulama