Dalilan da ke cusa yawan damuwa da baƙin ciki ga matasa a yau (II)

 1. Ta hanyar cognitive behavioral therapy:

A wannan hanyar likita kan kula da halayyan mutum ne (mara lafiyan) ta hanyar ƙoƙarin fahimtar yadda mutum ke tunanin da kuma yadda zuciyarsa ta ke aiki. Sannan kuma zai duba irin negative emotions da ke tattare da wannan mutum. Bayan haka, sai likitan ya shirya jinya ta musamman da ya cancanci damuwan wannan mara lafiyar.

Wai shin me ke faruwa ne da ke haifar da ciwon damuwa (anxiety)?

A dai yadda abin yake a yanzu, kusam mutum miliyan shida da digo takwas (6.8 million) ne a qasar Amurka aka same su suna da ciwon damuwa. A cikin waɗannan mutane da ke ɗauke da wannan matsala duk yawancin su matasa ne da ke a makarantu sakandare da kuma jami’o’i.

Ana alaƙanta ciwon damuwa ne da yanayi da ke hana mutum shiga cikin jama’a ko zuwa wajajen bukukuwa. Mutane da ke fama da ciwon damuwa da ake kira da general anxiety kan shiga cikin tsaka mai wuya (panic attack) da zaran sun tuna za su fita cikin jama’a da ba su saba da su ba (outside of their comfort zone).

Wasu dalilai ne kan jawa wannan ciwon na damuwa?

Matsala na rashin kuɗi (financial stress).

 1. Matsatsi a wurin aiki, ko gida ko kuma wajen wani alaƙa na daban.
 2. Dalilan shan wasu magunguna (side effects of medical aid or illness).
 3. Shiga wani yanayi da ya girgiza mutum (emotional trauma).
 4. Tsoro na mutane da baida wani dalili.
 5. Rashin sanin darajar kai (low self-esteem) ko tsangwama (bullying)
 6. Dalilin shan miyagun ƙwayoyi, kamar hodar iblis da makamatanshi.

Alamun ciwon damuwa (sign and symptom of anxiety):

Mutum ya riƙa jin yana cikin ƙunci, da rashin jin daɗin da saurin fushi.

 1. Rashin iya natsuwa da rashin iya sa hankali a wajen abu ɗaya, misali idan karatu mutum ya ke yi ba zai iya fahimtar abinda ya ke karantawa ba.
 2. Jin tsoro mai tsanani (panic attack) ba tare da wani dalili na azo-a-gani ba.
 3. Rashin son shiga jama’a.
 4. Rashin iya isar da saƙon da ya dace idan ana magana (poor communication skills).
 5. Tsoro na babu-gaira-babu-dalili.

Yaya za a yi a rabu da wannan matsalar ta damuwa?

Cin abinci mai lafiya kamar kuma mai gina jiki mai ɗauke da sinadarai irin su omega 3 fatty acids da kuma abincin da ake kira fermented food zai taimaka wajen rage ciwon damuwa.

 1. Rage abinci mai sinadarin caffeine. Sannan rabuwa da shaye-shaye kamar su tabar wiwi da su giya na taimakawa kwarai ainun wajen rage damuwa.
 2. Yin meditation da kuma yoga na amfani sosai wajen rage wannan matsala.

Mai ya sa yara ’yan makaranta suka fi fama da wannan matsaloli na depression da anxiety?

A bisa bayanai na bincike da dama sun nuna cewa matasa ’yan makarantun jami’a sun fi shiga matsalar ciwon baƙin ciki da damuwa. Dalilai da dama sun haifar da wannan lamari. Ga kaɗan daga cikinsu:

Social media (kafafun sada zumunta):

Social media ya zame wa matasa wajen yin hira da faɗin albarkacin bakunansu. Baicin wannan, matasan na tsere-tsere wajen saka shahararrun hotunansu da kuma wasu kyawawan ɓangaren rayuwarsu a waɗannan kafa don burge abokansu. Wannan gasa da ake yi ya sa matasa da dama suna kwatanta kawunansu da wasu. Sai su riƙa ganin ai su kam basu da sa’a saboda irin ganin abinda su waɗancan abokan nasu ke nunawa duniya suna da shi.

Amma abinda su waɗannan matasa basu gane ba shi ne, shi wannan social media ba wai gaba ɗaya rayuwar mutum ya kunsa ba, a’a wani ɓangare ne ƙalilan kowa ke nunawa na raruwarsa.

Saboda haka wannan lamari in ba a yi hankali ba sai ya zama ciwon baƙin ciki da damuwa. Matasa su sani kowa na da matsalarsa!

Shaye-shayen miyagun kwayoyi:

Matasa a har kullum sukan dau ɗabi’u da yawa a wurin a bokansu. A wannan zamani shaye-shaye ya yi yawa cikin al’umma saboda haka a makarantu ma abin ya ta’azzara.

Wannan lamari na shaye-shaye, kamar yadda kowa ya sani, yana illata ’yan makaranta. Kaɗan daga cikin illolin shine ciwon baƙin ciki da damuwa wadda hakan kan iya kai su ga rashin sanin darajar kai, wato low self-esteem, a Turance da ma matsaloli da dama wadda ciwon damuwa da bakin ciki ke haifarwa.

Yanayi na gasa a yau (career pressure):

Kasancewar rayuwar wannan zamani ya ta’allaƙa ne kacokan a kan gasa da nuna isa, inda za ka ga kowa ƙoƙari ya ke ya ga ya kere ɗan uwansa, hakan ya sa matasa na shiga tsaka mai wuya wajen matsi da suke fuskanta daga wajen iyayensu harma da malamansu. Iyaye da malaman na tursasa yaran shiga a dama da su, don ganin suma nasu yaran ba a bar su a baya ba. Saboda irin wannan matsi wasu matasa kan shiga cikin damuwa, musamman in har ba su (matasan) yi sa’a da yawan samun nasara ba a rayuwa.

Matsi na wajen abokai (peer pressure):

Yawacin matasa na tsintan kansu a cikin matsi da tsangwama na abokai a makarantu, wato abin nan da aka fi sani da suna bullying a Turance. Kuma mafi yawan lokuta su waɗannan abokai masu bullying ɗin suma kansu suna fama ne da damuwa amma sai su sauke shi ga wadda suka renawa hankali a makaranta. Wannan halayya na bullying na haifar da ciwon damuwa da kuma bakin ciki ga ’yan makaranta.

Saboda haka matasa ’yan makaranta su lura da kyau da irin abokansu don kare kawunan su daga shiga irin wannan matsala na bullying.

Mene ne abin yi don ganin an rage wannan matsaloli a wurin matasanmu:

Da yawa da ga cikin matasa ’yan makaranta sukan ɓoye damuwarsu don kar a musu dariya ko kuma a ce sun ƙasa. Wannan ɓoye matsala na damuwa kan iya jefa su cikin halin ha’ula’i.

A ƙarshe, muna iya fahimtar cewa fama da ciwon baƙin ciki ko damuwa abu ne mai wuyan sha’ani, amma idan mutum ya mai da hankali ya bi hanyar da ya dace, za a rabu da shine kamar ba a yi ba. Allah Ya kawo mana ɗauki da zaman lafiya!

Wassalm. Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *