An bayyana dalilan da suka sa Shugaba Bola Tinubu ya sauke ministoci biyar, amma ya bar Ministan Tsaro Bello Matawalle, duk da zarge-zargen goyon bayan ‘yan bindiga da ake masa. Ministocin da aka cire sun haɗa da Uju-Ken Ohanenye (harkokin mata), Lola Ade-John (yawon buɗe ido), Prof. Tahir Mamman (Ilimi), Dr Jamila Bio Ibrahim (matasa), da Abdullahi Gwarzo (gidaje).
Mai ba shugaban ƙasa shawara, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa sauya ministocin ya biyo bayan yadda jama’a ke kallon yadda suka yi aiki da kuma bayanai kan tasirinsu. Wata majiya daga APC ta ce rashin tasiri a siyasarsu a jahohin da suke wakilta ya taimaka wajen cire wasu ministocin.
Wani jigo a APC ya ce an yi la’akari da ko cire minista ba zai kawo rikici a yankin shi ba, kuma aka tabbatar cewa hakan ba zai janyo matsala ga shugaban ƙasa ba. Ya ƙara da cewa wasu an cire su ne saboda rashin tasiri a siyasa da kuma halayensu.
Haka zalika, majiyoyin sun nuna cewa Tinubu ya rike wasu ministocin don kare burin sa na wa’adi na biyu, tare da la’akari da rawar da za su taka. Amma zarge-zargen tallafa ‘yan bindiga da aka yi wa Matawalle sun ci gaba da janyo cece-kuce, inda Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ikirarin cewa gwamnati tana kare Matawalle daga bincike.
Onanuga ya ce an bar Matawalle ne saboda rahoton NSA ya bayyana cewa zarge-zargen siyasa ne kawai. Duk da haka, mai magana da yawun Lawal ya musanta hakan, yana mai cewa ya dace Matawalle ya sauka don a gudanar da cikakken bincike ba tare da tasirinsa ba.