Dalilan da suke jawo matsalolin aure a yau

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Fatan kowa ya san wannan kalma ta ‘aure’. Duk inda aka shiga aka fita, magana ce dai ƙwaya ɗaya da ake ta yin ta shekara da shekaru. Ba kalma ce ta wasa ba, kuma ba kalma ce ta riƙon je-ka-na-yi-ka ba. Kalma ce mai muhimmanci da amfani. Kalma ce da dukkan Musulmi yake daraja ta da girmamawa. Saɓanin yanzu da aka yi wa kalmar riƙo na sakainar ɗiban kashi ba.

Da yawa yanzu an mai da auren abun wasa ko wani abu kawai na son rai. Ana ganin ma’aurata na cin karensu babu babbaka. Yara sun ga juna suna so, su tashi hankalin juna da iyayensu sai an bar su sun yi aure. Ba sa duba nasiha da hangen da iyaye ke musu. Ala kulli halin gani suke ba a son su. Haka daga yaro ya samu kuɗi, sai ya fitini kan  aure zai yi, bai ma gama gina rayuwarsa ba. Su kuma iyaye kawai don kada ran yaransu ya ɓaci, sai su amince ba tare da hangen me gaba za ta haifa ba.

Nema:

Daga neman auren ake fara samun tangarɗa. Wani auren ba bincike ake gudanar da shi. Wala alla son rabuwa da ‘yar ne, ko kuma kawai abun da take so ake son mata, ba a hangen rashin iliminta a harkar. Kawai uwa na ganin dama ta zo da za ta fita kunyar mutane ɗiyarta ba ta yi kwantai ba, ko ta samu gidan hutu da dai makamantan abubuwa na mata. sai daga baya uwa ta zo tana cizon yatsa. Auren yanzu dai cikin kaso ɗari, bai fi kaso sittin ke iya riƙonsa ba.

Idanun yara duk ya rufe ba su damu da karatu ba, ko aikin yi. Kawai burinsu, su gina gida babba, a hau mota a cika kuɗi a aljihu da manyan waya. Ita kuma a cika mata ɗaki da kayan kece raini, a gyara mata falo da kicin, a cika mata sito da kayan abinci. Yadda kowacce ƙawa ta zo ta gani, za ta san ta girmi ƙaranta. Shi ma abokansa su san ya kama ƙasa. Babu jimawa kuma, sai labari ya fara canjawa. Abubuwan da take hangowa a gurinnsa ba haka ba ne. Shi ma abun da yake hangowa, ba haka ba ne.

Daga nan, sai ma’aurata su manta zumuɗin da aka ci buri za a yi wa juna, a fara jin haushi juna. Daga nan komai zai ƙare duk wannan soyayyar da kulawar za ta ja baya sai dai zaman gaba da haƙuri da juna. Idan ma hakan ta samu an auna arziki. wasu ba a kai wa ko ina auren yake ƙarewa. Iyaye su kuma ɗiban takaici da rashin madafa. Ƙaramar yarinya an sako ta, ta koma zawarci. Ina daɗin haka?

Rayuwar aure a yanzu:

ya yi wuya ba ga manyan ba, ba kuma ga yara ba. Kowa cu]awa yake. Amma na yaranmu ya fi wuya. Saboda su ba su san dawan garin ba, kawai suna jin ana faɗa ne. Ba su san daɗinsa da ɗacinsa ba, sai dai godiyar Allah. Wani lokacin idan ba a rabu ba, za a yi rayuwar ba daraja ba mutunci. Ka ɗauki yarinya a gidan iyaye da cewa za ka bata ci da sha da suttura.

Sannan za ka magance mata wasu matsalolinta na rayuwa. Amma sai ta shiga, duk ka zubar da wannan alƙawari da ka ɗiba a gaban iyayenta. Ka kawo ka ajiye kana fallasa mata, wannan ba dai-dai ba ne. Da ma auren da aka gina cikin ƙarya da kame-kame, to ya fi komai hatsari. Saboda waɗannan sharuɗɗan da ka ɗiba ya fi ƙarfinka.

Ita kuma ta san ba haka ka saba yi mata a waje ba. Ka zo ka fara mata haka, ai dole zaman lafiya ya yi ƙaura. Yanzu tubalin ƙarya ake gina auren da shi. Ka ji ana, zan miki kaza zan ba ki kaza, ina da kaza ina da kaza. Ka gama hure mata kunne da ƙarya.  ta gama tsara yadda za ta yi rayuwan jin daɗi.

Waɗanda kuma suke son ta tsakanin da Allah, ta zubar da su. Kawai hangen ta za ku yi rayuwa ta jin daɗi. Ta zo ta ga yadda gidan ma da ka ajiye ta ba irin wanda ka kwaɗaita mata ba ne. kawai ka ƙirƙira ne don wani tunani da hangen ta. Ita kuma ta shigo, ta ga ashe bula ne dole kuwa a ji ba daɗi. Mazan yanzu ƙarya da fariya sun yi musu yawa. Su kuma matan yanzu, kwaɗayi da hangen dala ba shiga birni ba ya rufe musu ido.

Sai a yi auren a zo ana ta sa iyaye tafiya sasantawa. Daga ƙarshe sai kuma rabuwa ta zo. Saboda ba za ta iya ba, kai ma ka suke ka kasa ɗauka. a ilahi ko ma meye matsalar, duk dole a ɗora a kan iyaye. Don su suka yi saken da yaran suke wannan rayuwar. Shi fa auren nan ba a yi wa kowa dole ba. Idan kana da shi, ka yi. Idan babu hali, ka haƙura. Sanda Allah ya yassare maka, sai ka yi kawai. Amma ka zo kana sa kanka a cikin wahala, har ka kai ga zaluntar matar ka da ‘ya’yan da za ka haifa.

Idan har ka san za ka iya aure, to ka shirya tarar kowanne kalubalen dake cikinsa. Shari’a ce ta Allah. Kuma lada ne ba kaɗan ba. Idan ka san da takura, to ka haƙura har lokacin da ka kafa kanka, ka san za ka iya ɗaukar nauyin kanka da na iyalinka. Amma meye amfanin ka ɗauko wa kanka abun da zai zamo maka damuwa, har ka cuci ɗiyar wasu?

Sana’a:

Duk uwa ya kamata a wannan rayuwa da muke ciki ta dage ta koyawa ɗiyarta sana’a. Ko ba ta aiki, za ta riƙe kanta da wani ma nata. Saboda duk yadda muke tsammanin abun ya wuce saninmu. Muddin ba kya sana’a, to za ki yi ta fuskantar rayuwa a bai-bai. A ganin ki miji dole shi zai miki saboda nauyinsa ne. To ki ajiye wannan a gefe, sai ya ga dama.

Kuma yana da shi ma, sai ya ƙi yi, kuma ba yadda za ki yi fa. To amma idan kina da sana’arki, insha’Allahu abubuwa za su zo miki da sauƙi. Ki taimaka masa har ma da wani nasa ko naki. Da ma zaman tare ya gaji haka. Kai kuma namiji Banda mugunta. Wallahi kana ganin ka isa ka yi wa matarka yadda ka so, alhakinta sai ya hana ka samu, ya hana ka jin da]i. komai naka ya toshe, wallahi, ka rasa dalili. To duk rashin kyautata wa iyali ne, bayan kana da shi amma ka hana. Wasu da dama cikin ma’aurata na ɗaukar rayuwar aure, wasa. Ba ta da wasa kuwa. Da]inta kaɗan ne. Idan ba a gina ta a kan madaidaiciyar hanya ba, wallahi sai a zo ana da-na-sani lokacin kuma waje ya ƙure.

Hange:

Yawancin samari da yan mata duk hangen wani abu ne yake sa su shiga mummunan yanayi a rayuwa. Bayan da yaudara aka gina zaman. Sai ai ta jin haushi kuwa. Wanda kuma da kanku kuka yi kirari, kuka daɓa wa kanku wuƙa.

Yana da kyau komai za mu yi, mu yi don Allah. Saboda ba ka san me baya za ta haifa ba. Iyaye kuma su dinga bincike da nuna wa yaran su yadda rayuwar ta koma da yadda kuma za su yi haƙuri a gidan aurensu. Ba daga matsala ta taso ba, ki zaro mayafi ki taho gidanku ba. Da haka ake yi, da duk nan mu ma ba a haife mu ba, wallahi. Mu ma haƙuri iyayenmu suka yi, mu ma ga shi muna koyi. To mu ma, mu koya wa yaranmu abun da mu ka koya a gurin iyayenmu.

Allah sa mu dace. Abun da muka yi na dai-dai, Allah ya amsa, wanda muka yi ba dai-dai ba, Allah ya yafe mana. Kar ku manta,  gyara, shawara ƙofarmu a buɗe ta ke.

Mu tara sati na gaba. A ci gaba da bibiyar Jaridar Manhaja. Wassallam.