Dalilan sirri ne – Martanin Ƙasar Kanada bisa ƙin bada biza ga jagororin tsaron Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI

Babbar Hukumar ƙasar Kanada a Nijeriya ta yi tsokaci game da rahotonnin da ke yawo na cewa ta hana bada bisa ga jagororin tsaron Nijeriya ciki har da Janar Christopher Musa, Babban Hafsan Tsaron Nijeriya.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, hukumar ta ce tana sane da lamarin, saidai ba za ta yi bayanin dalilin hakan ba kasancewar abu ne na sirri.

Rahotonni sun bayyana cewa an gayyaci jagororin tsaron ne don karrama wasu daga cikin tsofaffin sojojin da suka halarci yaƙe-yaƙe.

A yayin da wasu daga cikin tawagar suka samu bisa, wasu kuwa hana su aka yi wanda hakan ya sanya suka fusata saboda ganin hakan a matsayin rashin mutunci.

Janar Musa ya koka game da al’amarin a yayin taron Cibiyar Nazarin Tsaro ta ƙasa a Abuja, wanda hakan ya sanya shi yin kira da babbar murya ga ƙarfafa ikon Nijeriya a idon duniya da tsayawa da ƙafarta.

Haka ma Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu, ya nuna damuwa game da lamarin tare da goyon bayan kalaman Babban Hafsan Tsaron.

Ya bayyana abinda Kanada ta yi matsayin rashin mutunci, ya na mai jaddada buƙatar faɗaɗa hanyoyin inganta ƙasa ga Nijeriya.

Hukumar ta Kanada ta ce kasancewar matsala ce ta sirri, ba za ta ce komai ba game da batun.