Dalilan tsaro sun tilasta wa Masarautar Zazzau soke hawan Sallah

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna

Masarautar Zazzau a Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Maimartaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu, ta bayyana soke hawan Babbar Sallah yayin bikin Idul Kabir na bana.

Masarautar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun Sakatarenta, Alhaji Barau Musa Aliyu (Sarkin Fulanin Zazzau).

Tana mai cewa an soke hawan ne saboda dalilai na halin tsaro da kuma al’amarin cutar korona.

ASanarwar ta ce an cim ma matsayar soke hawan ne yayin wani taro da majalisar masarautar ta gudanar.

Sai dai masarautar ta bai wa jama’arta damar gudanar da Sallar Idi a dukkanin masallatan idi na ƙasar Zazzau kamar yadda aka saba.

Tare da yin kira ga ‘yan masarautar da a ci gaba da kiyaye dokikin yaƙi da cutar korona da kuma yi wa ƙasa addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa.