Dalilanmu na bin Sha’aban Sharaɗa Jami’iyyar ADP a Kano – Rarara

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jam’iyyar ADP a Kano ta bai wa ‘yan wasan Hausa da mawaƙa guraben takara da dama a cikinta.

Idan za a iya tunawa a Asabar ɗin da ta gabata ne Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya ƙaddamar da takarar Gwamnan Kano a cikin jam’iyyar.

Yanzu haka dai jam’iyyar ta bai wa mawaƙi Aminu Ala takarar Majalisar Wakilai ta Nassarawa.

An kuma bai wa Daddy Hikima wanda aka fi sani da ‘Abale’ takarar majalisar a Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

Da yake qarin haske kan dalilinsu na bin Sha’aban Sharaɗa, mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya ce sun bijire wa APC ne saboda hana ‘yan fim da mawaƙa takara.

Rarara wanda shi ne shugaban ƙungiyar 13×13 ya ce sun daɗe suna tallata wasu suma lokaci ya yi da za a rama wa kura aniyarta.

“Mun daɗe a wannna harkar muna tallata wasu, to mu mai zai hana muma a ba mu dama mu yi takara kamar yadda kowa yake yi.

“Ba wai mu zama kamar kyandir ba mu haska wasu mu kashe kanmu,” a cewar Rarara.

A don haka ya ce sun ƙi marawa ɗan takarar gwamna a jam’iyya mai mulki ta APC Nasiru Yusuf Gawuna baya, suka kuma bi Sha’aban Sharada domin cimma murdunsu na siyasa.

Rarara ya ce yana so a mayar da masana’atar Kannywood wani dandali da kowa zai yarda ana samun ci gaba.

Ya ƙara da cewa jama’a ma ya kamata su yarda ‘ya’yansu ka iya shiga domin samun kyakkyawar madogara kamar kowanne irin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *