Dalilin ƙaruwar hare-hare a Nijeriya – Hedikwatar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta bayyana dalilan da suka saka aka samu ƙarin hare-hare a Nijeriya.

Cikin makonnin da suka gabata dai a Nijeriya, an ga yadda Boko Haram da kuma ‘yan fashin daji suka ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a wasu sassan ƙasar.

Lamarin da ya bar al’ummar ƙasar cikin taraddadi kan dalilin faruwar hakan.

Mayaƙan Boko Haram sun kai hare-hare a jihar Borno, waɗanda ya zuwa yanzu ba a kammala tantance ɓarnar da hakan ya haifar ba.

Duk kuwa da cewa rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa jami’anta shida ne aka kashe a harin da aka kai ‘na ramuwar-gayya’ a ƙaramar hukumar Damboa da ke jihar Borno.

Sannan kuma gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa an kashe aƙalla manoma da masunta 40 a harin da mayaƙan Boko Haram ɗin suka kai a ƙaramar hukumar Kukawa da ke jihar ta Borno, duk da cewa wasu rahotannin sun ce alƙaluman sun zarta haka.

A arewa maso yammaci ma an samu ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga, lamarin da ya kai ga cewa rundunar sojin Nijeriya ta kai wani hari ta sama, wanda ya faɗa kan fararen hula a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

A ranar Alhamis ne shalkwatar tsaro ta Nijeriya ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sanya aka samu ƙaruwar ayyukan ‘yan bindiga a ƙasar cikin kwanakin nan.

Lokacin da ya gana da manema labarai, Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai Na Shalkwatar, Manjo-Janar Edward Buba, ya bayyana cewa, babban dalilin hakan shi ne kwararowar baƙin ‘yan bindiga daga ƙasashen waje.

Ya ce “dakarun Nijeriya na tarwatsa da kuma kawar da sake ɓullowar hare-haren ta’addanci a arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas, wanda ke faruwa sanadiyyar kwararowar mayaƙa daga ƙasashen yankin Sahel”.

Ya ƙara da cewa “zai iya yiwuwa dakarun (Nijeriya) su samu koma-baya wajen gudanar da ayyukansu, abu ne da aka saba gani a duk wani wuri da ake yaƙi.

“Babbar manufarmu ita ce karya ƙarfin da ‘yan ta’adda ke da shi na yin yaƙi, kuma muna nan a kan hakan,” inji Buba.

Jami’in na shalkwatar tsaro ya kuma ɗora wani ɓangare na laifin ƙaruwar hare-haren kan wasu mutane a cikin Nijeriya waɗanda ke haɗa kai da mayaƙan da ke shigowa ƙasar.

“Su ne infoma, waɗanda ke bai wa ‘yan ta’adda rahoton ayyuka da zirga-zirgar dakaru. Amma duk da haka, dakarunmu na sane da nauyin da ke kansu na yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a faɗin ƙasa.”

Waɗanne mayaƙa ne suka shiga Nijeriya?

Duk da dai shalkwatar tsaron ta Nijeriya ba ta yi ƙarin haske kan mayaƙan da suka kwarara zuwa Nijeriyar ba, amma a baya-bayan nan ƙasar ta fuskanci ayyukan wata sabuwar ƙungiyar ‘yan bindiga da ake kira Lakurawa.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa ‘yan ƙungiyar sun shiga yankunan jihohin Sokoto da Kebbi ne daga ɓangaren yankin Sahel, wanda ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.

Bayanai sun nuna cewa idan mutanen suka yi wa’azi ko faɗakarwa sukan fassara da Hausa, da Fulatanci, da Abzinanci, da Tubanci, da Barbarci, har ma da Ingilishi.

Dama dai yankin na Sahel ya daɗe yana fama da matsalar ‘yan tayar da ƙayar baya da na masu iƙirarin jihadi.

Misali, yankin ‘Zone de trois Frontieres’ wanda ya ƙunshi iyakokin ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso, ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan mayaƙa masu kai hare-hare.

Sannan a shekarun baya hukumomin Nijeriya sun koka kan kwararowar mayaƙa da makamai daga ƙasar Libya, ƙasar da ke fama da rikice-rikice tun bayan faɗuwar gwamnatin Marigayi Muammar Ghaddafi.