Dalilin bayyanar layukan abubuwan hawa a gidajen mai – NNPCL

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), ya alaƙanta layukan abubuwan hawa a gidajen mai da ake gani a Abuja da wasu sassan ƙasar da hana harkokin kasuwanci da zirga-zirga a lokacin zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da ya gudana ran 25 ga Fabrairu.

Hukumar NNPCL ta ce, defo da manyan motocin ɗaukar mai sun ci gaba da aikin rarraba mai zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan don daidaita lamurra.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakin NNPCL, Garba Deen Muhammad, ya ce bayanan baya-baya sun nuna kamfanin na da mai a tanade da ya kai lita biliyan 2.1.

Muhammad ya ce wannan na nufin ana da mai lita biliyan 0.9 defo da ake su a kan tudu, sannan lita biliyan 1.2 a madanan mai na kan ruwa.

Ya ƙara da cewa, wannan adadi na fetur da ake da shi zai wadaci ƙasa na tsawon kwana 35 daga 4 ga watan Maris da ake ciki.

Daga nan, Muhammad ya bai wa ‘yan ƙasa tabbacin NNPCL zai samar da wadataccen mai, yayin da kamfanin ke ƙoƙarin tanadin fetur lita biliyan 2.8 ya zuwa ƙarshen Maris, kwatankwacin man da zai wadaci ƙasa na tsawon 47.

Ya ce lallai bayyanar layukan abubuwan hawa a gidajen man Abuja da wasu sassan ƙasa, na da nasaba da hana harkokin kasuwanci da taƙaita zirga-zirgar jama’a a lokacin zaɓen da ya gudana.

Wanda a cewarsa gwamnati ta yi hakan ne domin bai wa ‘yan ƙasar damar sauke nauyin da ya rataya a kansu game da sha’anin zaɓe.