Dalilin cire Naja’atu daga APC – Tinubu

Daga WAKILINMU

Ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, ya cire Hajiya Naja’atu Mohammed daga matsayinta a kwamitin yaƙin neman zsɓensa ne saboda rashin ƙwarewa.

A ranar Asabar Naja’atu ta sanar da ficewarta daga kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na APC.

Naja’atu ta ce ba za ta iya ci gaba da zama a kwamitin neman zaɓen APC ba, tana mai cewa Tinubu yan fama da cutar ‘Alzheimer’ mai alaƙa da ƙwaƙwalwa.

Ta yi iƙirarin hatta kofin shayi ya gagari Tinubu riƙewa a lokacin da ta ziyarce shi a London kwanan baya.

Sai dai kuma, a wata sanarwa da ya fitar, Mai bai wa Tinubu shawara na musamman kan hulɗa da jama’a, Mahmud Jega, ya ce da ma Naja’atu ta riga ta yi murabus tun kafin ma a cire ta “saboda rashin ƙwarewa da rigima da kuma gano za ta zama hanyar jin sirrinmu ga kishiyoyinmu.”

Ya ƙara da cewa, ta yaudari jama’a ne da ta ce ta yi murabus alhali korar ta aka yi.

Ya ce Naja’atu dai ba likita ba ce, amma sai ga shi ta ba da rahoton kiwon lafiya a kan Tinubu bayan haɗuwarsu a London.

Ko ƙungiyar masu maganin gargajiya ba za su ƙyale ta ba saboda shigar burtu da yanke hukunci kan matsalar da ko gwaji ba ta yi ba a kanta.

Jega ya ce ɗan takararsu ya yi zirga-zirgar da dama, ya ziyarci sassan ƙasar domin gudanar da harkokin neman zaɓensa wanda hakan ba zai yiwu ba inda a ce ba shi da lafiya.

Tuni Naja’atu ta gana da ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, tare da bayyana goyon bayanta gare shi.