Dalilin da ya hana mu koma wa aiki – ASUU

DALILIN DA YA SA HAR YANZU ASUU BA SU JANYE YAJIN AIKI BA

DAGA AYSHA ASAS

Kungiyar malaman jami’a ASUU sun bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba su janye yajin aikin da suka kwashe watanni takwas suna yi ba.

Jagororin kungiyar sun ce gwamnatin tarayya ta kasa cika musu alkawuran da ta dauka, inda kungiyar ta bayyana cewa gwamnati ta rike wa membobinsu albashi na tsawon watanni duk da alkawuran da ta yi musu na kwana-kwanan nan wanda suka yi yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin amma ta kasa cikawa.

A yarjejeniyar, gwamnati ta yi alkawarin bai wa kungiyar ASUU Naira Bilyan 40 kudin alawi, sai kuma wata Naira Bilyan 30 domin gyara wasu tsare-tsare na Jami’o’in, wanda gabadaya ya kama Naira Bilyan 70.

Sannan kuma Gwamnati ta amince za ta biya albashin malaman jami’an wadanda ba a biya su hakkokinsu ba kafin watan Disemban da muke ciki, amma duk da haka suna ta tuntubar gwamnati amma shiru.

Bayan haka nan, gwamnati ta amince da bukatun kungiyar ASUU na cire tsarin IPPIS wajen biyansu hakkokinsu da kuma UTAS domin yin gaskiya da adalci a tsarin.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*