Dalilin da ya sa ɗan gidan Ganduje, Abdulazeez ya haɗa mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje da EFCC

A makon da ya gabata ne hukumar EFCC ta gayyaci matar Gwamnan Kano, Hajiya Hafsat Ganduje, zuwa ofishinta da ke Abuja don ta amsa mata tambayoyi masu alaƙa da zargin rashawa, amma ta ƙi amsa gayyatar.

A cewar jaridar Premium Times, Abdulazeez Ganduje, ya haɗa mahaifiyarsa Hafsat Ganduje da EFCC ne bisa zargin tana amfani da dukiyar ahalinsu wajen azurta kanta.

A cewar wata majiya wadda ta samu zarafin leƙa takardar ƙorafin da Abdulazeez ya rubuta a kan mahaifiyarsa, ta ce Abdulazeez ya nuna yadda wani ɗan kwangila ya same shi a kan ya taimaka masa wajen sayen wasu filaye a Kano a kan dubban daloli wanda har ya rigaya ya biya mahaifiyarsa Naira miliyan N35 a matsayin kamisho.

“Amma bayan watanni uku, sai ɗan kwangilar ya fahimci filayen da yake son saye ɗin an sayar wa wasu daban, don haka ya buƙaci a maida masa kuɗaɗensa”, cewar majiyar.

Da aka buƙaci jin ta bakin mai magana da yawun Gwamnatin Jihar Kano, Mohammed Garba, kan wannan batu sai ya ce, “Ba ni da masaniyar haka”, daga nan bai ƙara cewa komai ba.

Haka shi ma mai magana da yawun
EFCC, Wilson Uwujaren, ya ƙi cewa komai kan lamarin yayin da aka nemi jin ta bakinsa a ranar Litinin.

Sai dai, wata majiya ta kusa da EFCC ta ce akwai yiwuwar EFCC ta kama Hafsat Ganduje muddin ta ƙi amsa mata gayyatarta. Tana mai cewa, saɓanin maigidanta da yake sanye da rigar kariya albarkacin ofishin da yake riƙe da shi, Hafsat Ganduje ba ta da irin wannan dama.

Idan dai ba a manta ba, a can baya Gwamna Ganduje ya faɗa wata badaƙalar zargin rashawa bayan da mawallafin jaridar Daily Nigerian ya saki wasu hotunan bidiyo da suka nuna lokacin da gwamnan ke karɓar kuɗaɗe daga hannun wani ɗan kwangila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *