Dalilin da ya sa gwamnatin Sin ta samu goyon baya daga al’Ummun ƙasar

Daga CMG HAUSA

Kamar yadda aka saba a ƙarshen manyan taruka biyu na ƙasar Sin, firayin ministan ƙasar Li Keqiang, ya sanar da wasu sabbin matakan da gwamnatin ƙasar za ta dauka domin kyautata rayuwar al’ummun ƙasar, wadanda ake kira da “babbar tsaraba ta taruka biyu”.

Firaministan ya sanar da matakan ne a jiya Juma’a, yayin taron ganawa da manema labarai da aka kira bayan kammala tarukan.

Daga cikin matakan, akwai samar da guraben aikin yi, wanda ke da muhimmanci sosai ga rayuwar al’ummun ƙasa. Idan ana son kyautata rayuwarsu, akwai buƙatar goyon bayan kamfanonin da aka kafa, musamman ma ƙananan kamfanoni da ‘yan kasuwa masu zaman kansu, saboda adadinsu na da yawan gaske a ƙasar.
Kuma suke samar da yawancin guraben aikin yi ga al’ummun ƙasar. Sakamakon ƙididdigar da aka samar ya nuna cewa, a halin yanzu adadin ‘yan kasuwa masu zaman kansu a ƙasar Sin ya kai miliyan 100, waɗanda ke samar da guraben aikin yi kusan miliyan 300 ga al’ummun ƙasar.

A bana, gwamnatin ƙasar Sin ta tabbatar da cewa, kafin ƙarshen watan Yunin dake tafe, za ta rage harajin da ƙananan kamfanoni za su biya, kuma za ta ɗauki wasu sabbin matakai domin taimakawa sana’o’in ɗakin cin abinci da yawon shakatawa da jigilar fasinjoji da sauransu, ta yadda za a cimma burin kyautata rayuwar al’ummun ƙasar.

Fassarawa: Jamila