Dalilin da ya sa mawaƙan bege mata suka zama taron tsintsiya – Fantimoti

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano.

A wannan lokacin masu yabon Annabi, wato sha’irai, musamman mata su na samun ƙalubale a wajen jama’a wajen yadda su ke gudanar da harkokin waƙar tasu ta yadda a ke yi musu kallon suna shigo da wasu abubuwa da dama waɗanda suka sava wa yabon Manzon Allah (SAW), kamar abin da ya shafi yawon majalisi, haɗuwarsu da maza da sauran abubuwan makamantansu. Wannan ya sa Manhaja ta nemi jin ta bakin ɗaya daga cikin fitattu a cikin waƙoƙin Yabon Annabi, wato Hajiya Maryam Saleh, wacce aka fi sani da Maryam Fantimoti, domin ta yi mana bayani akan matsalolin da suke cikin harkar da kuma irin matakin da su ke ƙauka a matsayinsu na shugabanni. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Kin daɗe a cikin harkar waƙa, wacce kin haɗa ɓangare biyu ne; da waƙoƙin yabon Manzon Allah (SAW) da kuma waƙoƙin fim, wanda aka fi sani da waƙoƙin Nanaye. Ko za mu iya sanin tsawon lokacin da ki ka shafe a cikin harkar waƙa?
FANTIMOTI: To alhamdu lillahi, ka san ita waƙa, ni’ima ce daga cikin ni’imar Allah. Idan ƙudirar Allah ta ba ka damar yin waƙa. To mutanen da su ke ji kuma su ke sauraron ka sun san waƙa ka ke yi. Don haka shi yabon Manzon Allah (SAW) na fara shi ne tun lokacin da aka saka ni a makarantar Islamiyya, don a lokacin ban fi shekara takwas ba, to daga nan na fara, ina yi har aka yi mini aure. Allah ya sa aka fara yin fim ɗin Hausa, ya ba ni sha’awa na fara, na zo na shiga waƙoƙin fim ɗin Hausa. Kuma sai Allah ya nufa zan yi suna duniya ta san da ni. To daga nan kuma Ungulu sai ta koma gidan ta na tsamiya, sai na ce ni fa mai waƙoƙin yabo ce, don haka sai na fantsama na koma. Sai ya zama shi ma yabon Allah ya sa jama’a sun karɓe shi. To wannan shi ne yadda harkokin yabo da waƙoƙi na suka samo asali.

Tsawon lokaci da ki ka shafe kina yin waƙoƙin Nanaye, da ki ka dawo harkar yabon, sai mutane su ke cewa daman kin iya waƙar Yabon Annabi.?
E gaskiya ne mutane da dama sun yi ta tambayar cewa daman Maryam Sha’ira ce? To amsar da zan bayar ni Sha’ira ce tun ina ƙarama, tun ma ban san menene duniya ba, na ke yin yabon Manzon Allah (SAW). To da na shigo waƙoƙin Nanaye ne sai na ɓoye tafiya ta a Manzon Allah (SAW), saboda ka san shi yabon Manzon Allah (SAW) bigiren sa daban ne, ba kamar tafiya ce ta waƙoƙin Nanaye ba. Kuma da Allah da Manzon sa suka so ya fita sai na ga bari na rera. Domin ba zan manta ba, waƙar da aka fara kawo mini na rera ba ma a nan Kano aka ƙirƙire ta ba, an ƙirƙire ta ne a wata babbar makaranta a garin Zaria, Malaman suka rubuta, sai suka buƙaci Maryam Fantimoti ta rera, sai ɗaliban su su rinƙa bi su na yi kamar su suka yi. Duk wanda ya ke Kano zai san wannan yabon nawa ne ya fara ratsa kunnen masoya Annabi suka ji, wanda za ka ji ina cewa, “Manzon Allah. Musɗafa Rasulullah. Kai mu ke buƙata a ranar taruwa idan ta zo.”

To a baya gidajen rediyo suna saka ta wanda kuma daga nan sai na ɓalle, kuma sai Allah ya kawo Malam Hafiz Abdullah. Shi ne wanda ya ke ba ni yabo na ke rerawa, daga nan kuma yanzu ana ta yi sai Allah ya haɗa ni da Sharu Ali Anwar, shi ma ya ba mu rundunar waƙe Ma’aikin Allah muna yabo. To daga nan kuma sai Sha’irai da dama suka shigo muna rera musu yabo wanda a halin yanzu ma Almajirin Malam Hafiz Abdullah ne ya ke ba ni yabo na ke rerawa. Shi ne Halifan Ambato kuma akwai Sha’irai da dama da ba za su faɗu ba, don haka ni gaskiya, waƙoƙin da na ke yi na yabon Manzon Allah (SAW), wasu ne su ke rubutawa na ke rerawa, don ita harkar yabon ibada ne kuma aiki ne ba ƙarami ba, don haka duk wanda karan sa bai kai tsaiko ba ya ce zai yi karambani ya ce zai yi rubutu a kan yabon Manzon Allah (SAW) to sai ya yi ba daidai ba. Don haka shugabannin mu ne su ke rubutawa mu ke rerawa, su ne idan suka fatar da alƙalamin sai mu fito mu rera don mun san idan muka rera mutane su ka ji, to za a gane abin an karɓo shi ne daga matatar abin, wannan shi ne dalili.

A can baya masu Yabon Annabi kaɗan ne, ba ku da yawa. Amma a yanzu ana ganin an fi yawa kuma mata su ne suka fi yawa har ana ganin kamar kun karɓe abin daga wajen maza.
Wannan gaskiya ne, ka san ita rayuwa yadda ka ke ganin ta aba ce da take da ƙalubale. A yanzu Sha’irai kam sun yi yawa don lokacin da na fara yabo, mata ba su da yawa, sai maza, duk da cewar da na fara yabon ina a mawaƙiya, ni an sanni a wani ɓangare da aka ji ni a nan ne sai aka ga kamar a wajen nake, duk da yake daga nan ɗin daman na tafi. To yanzu Sha’irai sun yi yawa, babu yadda za a yi ka ce yanzu Sha’irai mata ba su fi maza yawa ba, don a yanzu sun linka maza, kuma zamani ne ya kawo hakan.

Amma ana ganin yawan Sha’iran kamar taron tsintsiya ne babu shara, domin waƙoƙin ba sa isar da saqo kamar yadda ku ke yin naku a baya.
To ka san mutane a yanzu da su ke shigowa harkokin waƙe-wƙe, sha’awa ce kawai. In ki ka kalli mawaƙiya tana kan mumbari tana waƙe, kawai sai sha’awa ta fizgo ki kawai ki shigo. Saɓanin a baya wanda baiwar waƙar ce take shigo da mutane. Ba wani ne ya ke yi ba ka gani ka shigo. Mu Allah ne ya ba mu baiwar a jikin mu take. To a yanzu taro za ka zo mawaƙiya ta hau mambari ta ba ki sha’awa ke ma gobe a ji ki kina waƙa, shikenan kin zama mawaƙiya. To abin da aka rasa shi ne, su masu sha’awar su shiga waƙar su sani waƙa tana da matakai. Wanda ya ke matakin ta na farko murya. Na biyu kuma basira. Na uku kuma shi ne ka yi a rinqa jin abin da ka ke yi. Na huɗu kuma shi ne ka ɗaukaka ana neman ka har da kuɗi a ce ka zo ka yi. Sai na biyar kuma shi ne ka kai matsayin da duk inda aka kira ka a fagen waƙa za ka amsa sunan ka na mawaƙi. Amma Idan ka duba a yanzu ba haka abin ya ke ba. Don sai ka ga wata ma waqar ƙawar ta za ta hau ko ma ba da izinin ta ba, idan an yi mata magana sai ta ce “ai Sha’irar ce ta ba ni na rinƙa yi. Kuma a baya da mu ke yi ba a yin Halifa sai mawaƙi ya mutu, sai a naɗa wani a ce halifan wane, a yi taro a yi addu’a a ce Allah ya ji kan sa.

To a yanzu kana da rai sai ka ga Halifofin ka sun kai goma ko sama da haka. Ana taɓa su sai su ce ai halifan wane ne, sai ka ga mawaƙan suna naɗa halifofin su tun suna duniya. Ni kaina da na ke yin magana da kai, sai na ji an bugo mini waya an ce “ai halifiyar ki ce”. Sai na ce ni ba ni da halifa, don ni ban tava yin naɗi ba, don haka ni ba ni da wani halifa a wajen yabon da na ke yi wa Ma’aiki, don ban ga dalilin da zai sa na naɗa halifa ina da rai ba, to irin abubuwan da su ke faruwa a yanzu kenan. Amma yanzu sai ka ga mutum yana da halifofi bai ma san wasu ba, kuma babu mamaki har ya bar duniya ba zai san su ba. Don haka abubuwan da su ke cikin Hallara, wallahi ba sa cikin waƙoƙin fim na Nanaye. Saboda kowa ya kwana ya tashi da sanin ni Maryam Fantimoti ina cikin harkar waƙoƙin Nanaye, kuma ina cikin Hallara ta yabon Manzon Allah (SAW). To abin da ya ke cikin Hallara ta yabon Manzon Allah (SAW) ba ya cikin harkar fim ta Nanaye. Saboda a Nanaye babu yadda za a yi ka je ka ɗauki waƙar mutane ka je kana rerawa bai ɗaure ka ba. To ban da Yabon Annabi, domin wata ran kana cikin taro za ka ga wata ta hau waƙar ka tana rerawa. Kana taɓa shi sai kawai a ce Annabi ne. To ya za ka yi? Don haka abubuwan da su ke faruwa a cikin Hallara ba abu ne da ya dace ba, don ka ga su a wajen su babu kare haƙƙin mallaka, idan ka yi waƙa, mutane goma za su iya ɗauka su yi, kuma ba ka isa ka yi musu magana ba, sai a ce Annabi ne.

Abin da aka fi magana a kan sa a yanzu shi ne; da matan aure da zawarawa da ‘Yammata kowa waƙa, wanda hakan ya sa a ke ta yin zarge-zarge a kan wasu abubuwa da su ke faruwa.
To wannan ni dai abin da zan iya cewa yawanci idan ka ga matar aure tana waƙa a vangaren yabo na Manzon Allah ko Budurwa ta fito tana waqa, ƙalubale na farko shi ne; Ina mijin ki? Yana son ki? Shi ya ce ki je ki yi? Mataki na farko kenan. Idan Budurwa ce ke, yarinya ƙarama ina iyayen ki? Da izinin su ki ka fito ki ke yi? To ka ga wannan tambaya ce mai ƙwari. Matar aure a ƙarƙashin mijin ta take, ita kuma Budurwa a ƙarƙashin iyayen ta take. To ka ga kenan sai mu ɗauki abin mu jingina shi da zamani. Allah ne ya kawo mu zamani wani iri, wanda idan ka cika magana ma haushin ka a ke ji. Yanzu idan ka ɗauko magana ta gyara, ko kada ku yi, ba  shekaru ashirin da na yi ina waqa ba ko shekaru ɗari na yi wallahi sai wani ya ƙalubalance ni, don me za a faɗa masa gaskiya, an fi so a yi ta tafiya a haka cikin dabaibayi mummunan ƙulli, kafin ka kunce shi ka mutu, don haka zamani ne kawai sai dai a runguma a yi addu’a.

Kamar tafiya wajen Mauludi da mata su ke yi, su je su raba dare ko su kwana, an fi yin magana a kan sa.
To, ni wannan gaskiya ban sani ba. Saboda kowanne tsuntsu kukan gidan su ya ke yi, don haka ni a kan kaina kowanne Majalisi na je ba na kwana, idan har za a kwana ma ba za ni ba. Don zan iya cewa da kai a shekarun da na yi ina waqa a Majalisi ɗaya zuwa biyu na tava kwana har zuwa asuba. Su ma kuma majalisai ne na Annabi Muhammadu (SAW), ɗaya a Nijeriya, ɗaya kuma a Ƙasar Ghana. Kuma kamar na Ghana dole na kwana saboda ni aka gayyata na je taron daga Nijeriya don haka zan iya cewa da kai harkar kwana da a ke yi a wajen Majalisi gaskiya ban sani ba don ni ba layi na ba ne, ni ina gidan mu kullum, ƙarfe goma idan ba ka gabatar da ni ba sha ɗaya zan iya tafiya, na ce maka za a rufe gidan mu ni na tafi, kuma ina da yara, ni na ke kula da ‘ya’yana ban tava bar wa wani ya kular mini da ‘ya’yana ba, to ka ga mai yaro dole ya rinƙa kiyaye wasu abubuwan.

Kamar salon da mata su ke yi irin ’yan mata da za su rinqa shirya mauludi wannan ma a na faɗar magana akansa.
Eh to, ita harka ta alheri, idan mutum zai yi Mauludi ya tara jama’a, ya ba su ruwa, ya ba su abinci, aka ya salatin Annabi, aka karanta Alƙur’ani, babu yadda za ka yi da shi ka san aikin Allah ya ke yi. To shi ya sa da yawa idan za a yi taron ba a cika hanawa ba, saboda duk taron idan an yi sai an yi abubuwan nan guda uku to ka ga a cikin yabon Annabi da karatun Alqur’ani da ciyarwa wanne ne ba shi da kyau? In dai an yi abin cikin tsari ai ka ga babu laifi. Don haka za ka ga tun da aka fara yin Mauludi kullum gaba a ke ci ba baya ba, don haka shi aikin Mauludi ibada ne in dai an yi abin da ya dace.

A yanzu ta ɓangaren Gwamnatin Jihar Kano, Hukumar tace fina-finai ta samar da wani tsari na tantance masu harkar yabon Manzon Allah (SAW) da kuma neman izinin yin Majalisi, ko ya ki ka kalli wannan tsarin?
Gaskiya tun da aka fara yabon musamman lokacin da abin ya bunƙasa a tsakanin Matasa a ke tafiya cikin rashin tsari, sai a yanzu lokacin da Shugaban Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano Malam Ismaila Na’abba Afakallahu, ya samar da wannan tsarin wanda sai Sha’irai sun yi rajista kuma an yarda kai mawaqi ne sannan sai an yarda da wajen da ka ke tsayawa kana yin yabon, sannan ana ƙoƙari wajen tsara majalisin yadda maza su yi na su mata su yi nasu, to ka ga wannan ƙoƙari da Afakallahu ya yi abu ne mai kyau wanda ya kamata a yaba masa, kuma wannan tsarin an bar shi a ƙarƙashin shugabancin Sidi Abba a ɓangaren maza. Sai kuma ɓangaren mata aka bai wa Malama Hauwa, saboda tsayawar ta, domin ita ma abin yana yi mata rashin daɗi yadda abubuwan su ke tafiya a haka kara zube, don ka san fa Malaman su kan su ba daɗi su ke ji ba, sun fi so waƙa idan ɓangaren ka ne kawai a bar maka, idan kuma ba naka ba ne sai a yi maka gyara, wannan su ne abubuwan da a ke kai a yanzu, wanda a yanzu Sha’ira in dai ba da izinin mai waƙar ki ke yin waƙa ba, to za a kama ki kuma kowa yana zuwa ya yi rajista da Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano.Kuma mun ji daɗin wannan kawo gyaran, fatan mu Allah ya sa abin ya ɗore, kuma Allah ya sa ya yi tasiri, saboda jin daɗin gidan Manzon Allah (SAW). Allah ya kawo wa abin gyara. Don haka ina kira ga Sha’irai mata, ya kamata duk abin da za mu yi a duniya mu rinƙa sanin mu mata ne. Domin ita mace da namiji akwai bambanci, domin su maza daman abin na su ne, su ne suka fara. Na san a fadar Manzon Allah akwai mace da take yabon Annabi to don haka mu ma mata akwai mu, don haka mu kula, mu rinƙa kiyayewa a matsayin mu na mata. 

To, madalla, mun gode. 
Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *