Dalilin da ya sa muke yi wa Gwamnatin Filato zanga-zanga – Ƙungiyar Ɗalibai

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Talatar da ta gabata ne, ɗaliban jihar Filato na Kwalejin Fasaha ta Barkin- Ladi suka gudanar da wata zanga- zangar lumana don nuna ƙin jininsu a kan yadda hukumar gudanarwar makarantar take yin watsi da shakulatin ɓangaro a kan al’amuran ilimi abin da suka ce yana kawo musu tasgaro a harkar karatunsu.

A cewar ɗaliban saboda sakacin hukumar gudanarwar a yanzu haka sun biya kuɗin shekara uku cur, a matsayin kuɗin zangon karatu guda kacal!

A cewar wani shaidar gani da ido, kuma wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, ya bayyana cewa, a yayin da ya doso makarantar, ya tarar da cincirindon ɗalibai a ƙofar makarantar sun kuma garƙame ƙofarta sun hana shige da fice a makarantar.

Waɗansu daga cikin ɗaliban suna riƙe da kwalaye waɗanda ke ɗauke saƙonni kamar: “A dawo mana da Naira 5500 ɗinmu”, “Hukumar gudanarwa ba ta yi mana adalci ba”, ” Ba wanda ya isa ya cinye mana kuɗaɗenmu” da dai sauransu.

Mai magana da yawun ɗaliban, Rengtu Longkat, ya bayyana wa majiyarmu cewa, a shekarar 2016 hukumar makarantar ta nemi ɗaliban HND na kwalejin da su biya N5,550 saboda daidaita jarrabawar cigaba da ilimi (JAMB). Sannan aka sake umartarsu da su sake biyan N11,500 duk a kan JAMB ɗin. Inda hukumar makaranta ta yi musu alƙawarin dawo musu da kuɗinsu N5,550 da suka fara biya, matuƙar sun biya wannan N11,500 ɗin da aka umarce su da su biya.

Don haka suka shirya wannan zanga-zangar domin sanya hukumar makaranta ta cika wancan alƙawarin da ta ɗaukar musu. Domin a cewarsa, sun gaji da jiran gawon shanu ne. Sun cika duk wasu sharuɗɗa da aka umarce su, amma shiru kake ji. Shi ya sa suka fito zanga-zanga.

Ya ƙara da cewa ba wai waɗancan kuɗaɗe ne kawai suka biya ba, har da wasu kuɗaɗe kamar na amfani da kwamfuta da kuɗin magani da suka biya duk sun sha ruwa a cewarsa. Bugu da ƙari, makarantar ma ba ta da isassun malamai. Waɗanda ake da su kuma, aiki ya yi musu yawa, ba sa iya aikinsu da kyau.

Haka nan, Longkat ya tuhumi hukumar makaranta da ko-in-kula da take nunawa wajen kula da ɗakunan kwanan ɗalibai mata da ya yi gobara. Tare da cewa har yanzu hukumar ma ko bi ta kansa ba ta yi ba. Abin da ya ce ya yi sanadiyyar barin wasu ɗalibai makarantar, domin mazaunansu sun ƙone ƙurmus.

A cewarsa, hukumar makaranta ta fi damuwa da yadda za ta tattara kuɗaɗen shiga a kan ɗaliban da suke samar da kuɗaɗen.

Duk wani ƙoƙari na jin ta bakin Daraktan makarantar, Dauda Gyemang a kan batun, ya ci tura. Domin ya ƙi amsa kiran da aka yi masa ta waya.

Sai dai wata majiya daga manyan jami’an makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, waɗancan kuɗaɗen N5,500 an ba wa hukumar JAMB su. Kuma ita ma hukumar makarantar har yanzu jira take yi JAMB ɗin ta maido mata da kuɗin do ta biya ɗaliban. Sasi dai ya ƙaryata batun cewa makarantar tana tatsar ɗalibanta kuɗi.

Inda ya ƙara da cewa, duk wani abu da suka nema a wajen ɗalibai, akwai dalilin da ya sa. Ya ce don matsalar ƙarancin malamai kuma, akwai ta, ba wai babu ba. Amma hukumar makaranta ta mima kokenta a kan haka ga gwamnatin jiha.