Dalilin da ya sa na cancanci zama Shugaban APC na Ƙasa – Al-Makura

Daga IBRAHEEM HAMZA MUH’D a Lafia

Sanata Umaru Tanko Al-Makura shi ne tsohon Gwamnan jihar Nasarawa kuma yana ɗaya daga cikin ’yan takarar kujerar Shugaban Jam’iyyar APC ta Ƙasa. Ya zanta da Wakilin jaridar Blueprint Manhaja, Ibraheem Hamza Muhammad kan takarar tasa. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

MANHAJA: Jam’iyyar APC za ta yi zaɓen fitar da sabbin shugabannin jam’iyya. Mene ne manufarka?
Maƙasudin yin takarata ita ce, Ina ɗaya daga cikin iyayen jam’iyya, don daga Jam’iyyar CPC aka samar da ACP. Wato a turance ‘Merger’ kenan. Kuma mu na son ganin an ciyar da jam’iyyar gaba da mutumci. Na yi kyakkyawan shiri don ganin an samar wa jama’a romon demokuraɗiyya. Ba mu tava samun inda jama’a suka haɗa kai duk da sun fito ne daga ɓangarori daban-daban kamar yadda aka samu a yanzu ba. Na dace da wannan kujera domin ina da sanin buƙatar mutane da mutuntasu. Kuma ina farin cikin yadda hoɓɓasa da ni da wasu aka yi a 2013. Na kuma yi ɗamara domin tunkarar abokan takara domin na faɗaɗa kamfen don jagorantar jan’iyyar da ke da farin jini. Kuma ina son ta ci gaba gadan-gadan domin ta jima tana jagoranci.

Ko ya ka ga yadda ’yan jam’iyyarku ta APC suka tarɓe ka a wuraren da ka je don neman ƙuri’a?
Na yi farin ciki matuƙa, yadda mutane daban-daban daga matasa, mata, gwamnoni, tsoffin gwamnoni, sanatoci, ’yan majalissu da shahararrun ’yan siyasa suke ta nuna goyon baya da kuma yin fatan aljhairi, ya nuna lallai lokaci kaɗai ya rage in yi nasara sannan a rantsar da ni da yardar Allah.

Me ka ke son ganin ka cimma a matsayin shugaban APC?
A matsayina na shahararren ɗan siyasa da na yi shugaban matasa a Jam’iyyar NPN a tsohuwar Jihar Filato, na yi sakataren Jam’iyyar NRC, na yi taron fasalta tsarin mulki da kafa PDP, da kafa CPC har na zama gwamna yanzu ina Sanata, wanda kullum ina hulɗa da jama’a, ai ba wanda ya yi kusa balle ya haɗa kafaɗa da ni dangane da cancantar hawa wannan kujera. Sannan Gwamnoni za su fi sakewa da ni domin sun san cewa ni a cikin nake. Sannan zama na Sanata ya ƙara kusanta ni da ’yan majalissun qasa daga dukkan faɗin ƙasar nan. Haka kuma a matsayina na Tanko, ai lallai ne in tabbatar an san da zama da darajar mata iyayen gida. Nan ba da daɗewa ba, lokacin ina gwamnan jihar Nasarawa, ina ganin ni ne gwamna na farko a faɗin ƙasar nan ɗungurungun da na fara kanbama, don na ba mata biyar muƙaman Kwamishinoni daga cikin 17. Waɗanda ba su sani ba, ina da nakasa, domin bana ji magana sosai don bina da kurumta, don haka na ke tafiya da nakasassu ba za su ce idan ka game waɗanda na ke mu’amala da su, za ka ga cewa, Umaru TankoAl-Makura na kowa ne.

Me ya sa ka yi wa sauran ’yan takara fintinkau?
Ba wanda ya ke da gogewa kamar ni. Tun ina ƙarami na tafi makarantar boko na kwana, na yi karatun samun shaidar zama malami a garin Uyo ta jihar Cross River, a da amma a yanzu tana Akwa Ibom. Na yi karatun digiri ɗina a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, na yi bautar ƙasa a Makurɗi ta jihar Benuwai, na yi aikin koyarwa, na yi kasuwanci sannan na tsunduma siyasa. Kuma na mun kafa jam’iyyar CPC har na zama gwamna sannan ta yi gamayya da ta kai ga haɗewar CPC da wasu jam’iyyu inda muka kafa APC a 2013, don haka na fi duk ’yan takarar cancanta. Na san ɗawainiyar da kowa ya yi da waɗanda suka yi da kuma kowane ɓangaren ƙasa mutum ya fito. Ba na son nuna kaina, amma ina shaida wa sauran ’yan takarar cewa, na fi su cancanta matuƙa, domin Juma’a mai kyau, tun daga Laraba ake gane ta.

Kai ka fara zama gwamna na farko a Jam’iyyarka, shin ko ana iya ce maka ɗan gatan Shugaban Ƙasa Buhari?
Lallai na kafa tarihin zama zakaran gwajin dafi, don ni na fara zama gwamna har ya sa aka kafa tuta a gidan gwamnati. Hangen nesan Buhari ya sa aka kafa CPC, sannan waɗanda suka yarda da aƙidarsa ta son gina ƙasa suka yi masa mubayi’a. Lokacin ina cikin Jam’iyar PDP amma na qi shiga zaɓen share fagen tsayawa domin takarar gwamna don na ga ba za a yi adalci ba a 2010, duk da a lokacin akwai wasu jam’iyyu. Don ban ga jam’iyyar da ta dace da aƙidojina ba kamar CPC da kuma dattako fari da kuma kwarjinin Muhammadu Buhari. Don ana da gaskiya da riƙon amana tun tale-tale. Na shiga CPC, sannan na kayar da gwamnan jam’iyyar PDP daga kujera. Sannan APC ce jam’iyyar da ke kan mulki a jiha ta.

Shin ko sanata zai ba ’yan Jam’iyyar APC shawarar yadda za a gudu tare a tsira tare?
A gaskiya yin magana sai an ji a kafafen yaɗa labarai na amintattu. A girmama juna, a jajirce don gina ƙasa, kuma kowa ya daraja ra’ayin da ta banbanta da tasa. Ra’ayi ai ba gaba ba ne.