Dalilin da ya sa na tsunduma siyasa duk da kasancewa ta limamin coci – Mawaƙi Banky W 

Daga AISHA ASAS 

Shahararren mawaƙin Nijeriya Olubankole Wellington, wanda aka fi sani da Banky W, ya bayyana dalilin sa na shiga siyasa har ya tsaya takara, duk da cewa, a yanzu shi limami ne na Coci.

A cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, mawaƙin wanda a halin yanzu yake jagorantar wata Coci ya bayyana cewa, ya shiga harkar siyasa ne don ya canza ma’anar da mutane da yawa suke yi wa siyasa, inda suke kallon dukka wani ɗan siyasa a matsayin mutumin banza.

Mawaƙin ya ce, shigar tasa siyasa har ya tsaya takara, zai zama wata ishara da za ta ganar da mutane cewa, mutanen ƙwarai ma na shiga siyasa, kuma suna zama wata tsiya a cikin ta.

Bai ajiye numfashi ba sai da ya sako zancen mutuwar mawaƙi Mohbad, inda ya yi kira ga hukuma da ta tsaurara bincike don ganin ta zaƙulo wanda ya yi aika-aikar ga mawaƙi ɗan’uwasa na da.