Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi tsohon shugaban qasa, Marigayi Alhaji Umar Musa ‘Yar’Adua a matsayin magajinsa duk da ya san cewa ba shi da lafiya.
Tsohon shugaban ƙasar a wata hira da ya yi da jaridar Yanar Gizo mai suna “TheCable” ya musanta zargin da ake masa na cewa da gangan ya sanya ’yan takara masu rauni don son kai.
A cewarsa, ya ɗauki matakin ne saboda shawarwarin likitoci sun nuna cewa ‘Yar’Adua, wanda aka yi masa dashen ƙoda, ya cancanci zama Shugaban Ƙasa.
“Na kafa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Dakta Olusegun Agagu, mai albarka, domin neman wanda zai gaje ni. Sun yi la’akari da sunaye da yawa kuma suna da yaƙini sosai a kan dukkan mutanen. Sun bayar da shawararsu. Umaru ne kan gaba a jerin sunayen”.
“Babbar hujjar da suka bayar ita ce yana da gaskiya kuma ba zai yi sata ba. An tabo batutuwan da suka shafi lafiyarsa kuma na ba da rahoton likitansa ga ƙwararre don jin ra’ayi. An canza sunan Umaru don kada gwani ya san ko wane ne kuma dalilin da ya sa nake neman ra’ayinsa.
“Bayan tantance rahotannin, ya ce majinyacin da alama ya yi dashen ƙoda kuma idan haka ne, babu wani abin damuwa kuma zai kasance cikin ƙoshin lafiya kamar kowane mutum. Shi ke nan.
“Dukkan zage-zage da na san zai mutu kuma shi ya sa na goyi bayansa ya zama shugaban ƙasa ƙarya ne. Wannan shi ne ainihin labarin da na ba ku,” in ji Obasanjo.