Dalilin da ya sa NBC ta garƙame wasu gidajen rediyo da talabijin a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabin ta Ƙasa (NBC) ta ba da sanarwar rufe wasu tashoshin rediyo da talabijin a faɗin Nijeriya.

Darakta Janar na hukumar, Balarabe Shehu ne ya ba da sanarwar rufe tashoshin, yana mai cewa an ɗauki matakin haka ne saboda ƙin sabunta lasisinsu da tashoshin suka yi.

Shehu ya bai wa rassan hukumar a jihohi umarni kan su haɗa kai da hukumomin tsaro wajen tabbatar da kafofin da lamarin ya shafa sun daina aiki cikin sa’o’i 24 masu zuwa.

Ya ƙara da cewa, gwamnati na bin tashoshin da abin ya shafa bashin kimanin Naira biliyan 2.6.

Kuma ya ce kafin ɗaukar wannan mataki sai da aka sanar da kafofin tare da ba su wadataccen lokaci don su yi abin da ya kamata amma duk da haka sun gagara. Wanda a cewarsa, hakan ya saɓa wa dokar hukumar.

Ga jerin gidajen rediyon da talabijin a lamarin ya shafa kamar haka:

Silverbird TV (Silverbird Communications Co. Ltd) Network
Rhythm FM (Silverbird Communications Ltd)
AIT/Ray Power FM (DAAR Communication Itd)
Greetings FM (Greetings Media Ltd)
Tao FM (Ovidi Communications Ltd)
Zuma FM (Zuma FM Ltd)
Crowther FM (Crowther Communications Ltd)
We FM (Kings Broadcasting Ltd)
Linksman International ltd
Bomay Broadcasting Services Itd
MITV (Murhi International Group Ltd)
Classic FM (Pinkt Nigeria Ltd)
Classic FM (Pinkt Nigeria Ltd)
Classic TV (Pinkt Nigeria Ltd)
Beat FM (Megalectrics LTD)
Cooper Communications Itd
Splash FM (West Midlands Ltd)
Rock City FM (Boot Communications Itd)
Family FM (Kalaks Investments Nig. Ltd)
Space FM (Creazioni Nig. Ltd)
Radio Jeremi (Radio Jeremi ltd)
FM Abuja
FM Lagos
FM Yenagoa
FM Port-Harcourt
FM Jos
Wave FM (South Atlantic Media Itd)
Kogi State Broadcasting Corporation
Kwara State Broadcasting Corporation
Niger State Broadcasting Corporation
Benin
Network
FM Network
FM Okene,
FM Suleja
FM Abuja
FM Benin
Breeze FM (Bays Water ltd)
Vibes FM (Vibes Communication Itd)
Family Love FM (Multimesh Broadcasting Co. Ltd) Port-Harcourt
Port-Harcourt
Gombe State Broadcasting Corporation
Lagos DSB
Lagos State Broadcasting Corporation
Osun State Broadcasting Corporation
Ogun State Broadcasting Corporation
Ondo State Broadcasting Corporation
Rivers State Broadcasting Corporation
Bayelsa State Broadcasting Corporation
Cross River State Broadcasting Corporation
Imo State Broadcasting Corporation
Anambra State Broadcasting Corporation
Borno State Broadcasting Corporation
Yobe State Broadcasting Corporation
Sokoto State Broadcasting Corporation
Zamfara State Broadcasting Corporation
Kebbi State Broadcasting Corporation
Jigawa State Broadcasting Corporation
Kaduna State Broadcasting Corporation
Katsina State Broadcasting Corporation

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *