Dalilin da ya sa salon Amurka na yaƙi da annoba ya zamo mummunan matakin kare haƙƙin bil adama

Daga CMG HAUSA

Kafar watsa labarai ta NBC dake Amurka, ta bayyana cewa, yaɗuwar cutar COVID-19 a Amurka, ya kai wani sabon matsayi mai muni, inda adadin mutanen da suka rasa rayuka sakamakon harbuwa da annobar ya zarta mutum miliyan 1.

Duk da kasancewar ta kasa mafi karfin faɗa a ji a duniya, ko me ya sa Amurka ta kasance ta farko a duniya da ta gaza shawo kan wannan annoba? Amsar ita ce sanya buƙatar kashin kai sama da rayuwar bil adama, da mayar da manufar danniya sama da kare haƙƙin dan Adam.

Wata ƙila hakan ne dalilin da ya sanya salon yaƙi da annobar a Amurka, ya kasance mummunan matakin kare haƙƙin bil adama.

Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa