Dalilin da ya sa sojoji ba su ɗauki mataki kan Asari-Dokubo ba – Hedikwatar Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Alhamis ne Hedkwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce ta zaɓi ƙin ɗaukar mataki ne akan tsohon shugaban mayaƙan yankin Nija-Delta, Mujahid Asari-Dokubo don kar a zarge ta da saɓa wa ƙa’idar demokraɗiyya.

Daraktan Labarai na Hedikwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana hakan wa manema labarai a lokacin da ya ke tsokaci game da zargin cewa Asari-Dokubo ya yi barazanar kakkaɓo wani helkwaftan sojoji da ya gitta ta yankin gidansa.

Saidai, kakakin rundunar ya bayyana hakan da Asari-Dokubo ya yi a matsayin abin dariya inda ya ƙalubalance shi da ya tunkari sojoji a filin yaƙi idan ya isa.

Ya cigaba da cewa, ba sojoji kaɗai ba ne a ɓangaren tsaro saboda akwai hukumomi da dama da ke da alhakin kula kowane irin laifi.

Ya kuma ce, sojoji a halin yanzu sun mayar da hankali ne wajen ganin an daƙile ayyukan ta’addanci a dukkanin sassan Nijeriya wanda kuma su na cigaba da samun nasara a ƴan kwanakin nan.

Nazari da aka yi game da atisayen jami’ansu na sati guda ya nuna cewa, sun kashe ƴan ta’adda guda 165 yayin da suka kama 238 da kuma ceto mutane mutane 188 da aka yi garkuwa da su.