Dalilin kafa jaridar Manhaja

Dalilin kafa jaridar Manhaja

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai.
Yau sama da shekara tara, a watan Mayu, 2011, aka kafa jarida mai suna Blueprint. Da farko ta riƙa fitowa ne mako-mako, to amma cikin wata huɗu kacal sai ta koma mai fitowa kullum-kullum. Yin hakan babbar nasara ce da ke alamta ƙarfin ƙudirin waɗanda suka kafa ta, da sadaukarwar su ga manufofin da suka sa a gaba. Cikin jajircewa da rashin gajiyawa, ba a daɗe ba Blueprint ta kai matakin da ake lissafawa da ita a jerin manyan jaridun Nijeriya da ake bugawa cikin harshen Ingilishi.

Cikin ikon Allah kuma yanzu sai ga jaridar Hausa an kafa, Manhaja! Wannan jarida, kamar yadda yayar ta ta Turanci ta soma, ita ma za ta riƙa fitowa ne a kowane mako, nan gaba kuma ba a san abin da Allah zai yi ba. Ita ma, kamar dai yayar tata, haihuwar ta da aka yi a wannan marra wata babbar alama ce ta irin hoɓɓasan da kamfanin buga jaridu na Blueprint Newspapers Limited ya ke da shi wajen ganin ya fito da sabuwar kafar yaɗa labarai mai nagarta da inganci, yardajjiya, cikin harshen Afrika, domin ci gaba da yaɗa ƙudirin sa da manufofin sa kamar yadda ya shata su tun a cikin 2011. Fito da jaridar a daidai lokacin da kowa ke kokowa da halin matsin da ake ciki shi ma ƙarin alama ne na jajircewar kamfanin.

Manufofin mu ba masu wuyar ganewa ba ne. Na farko, aikin kowace jarida ne ta sanar, ta ilmantar, kuma ta nishaɗantar da jama’a. Mu ma da wannan burin muka zo. To amma kuma ba kawai za mu yi wannan aikin ba tare da zurfafa kowace daga cikin waɗannan manufofin ba. Mun ƙudiri aniyar duk abin da za mu kawo maku domin sanar da ku ko wayar maku da kai ko nishaɗantar da ku, to za mu ɗora shi ne kan wani sikeli na inganci da sadaukarwa.

A ƙoƙorin gudanar da aikin, halin da talaka ke ciki ne a ran mu domin muna sane da cewa har yanzu Nijeriya tana cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi a dukkan sassan cigaban ta a matsayin ’yantacciyar ƙasa. Koma-bayan ta ya sa da yawa mutane suna tunanin cewa shekaru sittin bayan samun mulkin kai bai tsinana wa ƙasar mu komai ba. Duk da yake mu mun san akwai ɓangarorin rayuwa da ƙasar ta samu cigaba, to amma ya ci a ce mun fi haka. Ɗimbin matsalolin mu sun sa ana ganin har yanzu lalube ake ta yi a cikin duhu, an kasa kamo bakin zaren.


Duk wani sashe da ka duba, za ka tarar akwai babban naƙasu. Idan aka dubi batun samuwar ingantaccen ilimi, kiwon lafiya, tsaro, hanyoyin mota, aikin gona, ruwan sha, aikin yi ga matasa, masana’antu da dai sauran al’amura na cigaba, za a ga har yanzu mu neutal. A yau, Nijeriya ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe mafi koma-baya ta fuskar waɗannan al’amura da muka lissafa. Babu ma kamar a ɓangaren tsaro, inda a kullum za ka ji an ce an kashe mutum kaza, an raunata mutum kaza, an sace mutum kaza, an yi wa kaza fyaɗe, an ƙwace dukiya kaza; zaman ɗarɗar ya zama abin da kowa yake kwana yake tashi da shi – ba yaro ba babba.

Haka kuma tattalin arzikin mu ya karye. A yanzu haka Nijeriya ta shiga gangarar fatara da yunwa, ta doshi wagegen rami mai zurfi da duhu, kuma ba mu ga burkin da za a ja a tsaya ba.


Farashin kayan abinci da na masarufi na ta tashin gwauron zabo; noma isasshen abinci ma an kasa yi saboda rashin tsaro da rashin jari ko kayan aikin noma na zamani. Harkar ilimi na neman durƙushewa baki ɗaya a yayin da malaman jami’a ke zaman dirshan na yajin aiki; samun ingantaccen ilimi a mataki na can ƙasa kuma ya zama sai wane da wane. Tursasa talaka da yi masa rashin adalci abin ya kai intaha.

A yayin da ake fama da waɗannan matsaloli kuma, cin hanci da rashawa ya yi wa Nijeriya katutu. Hakan na faruwa ne saboda yawancin masu riƙe da madafun iko sun maida hankali wajen azurta kan su. Ba fa yau aka fara ba, matsala ce da ta faro tun shekaru aru-aru, to amma kuma an kasa magance ta. Duk da ƙoƙarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari take yi wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, har yau dai abin jiya i yau.

A matsayin mu na ’yan jarida, aikin mu ne mu faɗa wa shugabanni da mabiya gaskiya. Don haka Manhaja ta ƙudiri aniyar za ta riƙa hasko wa masu karanta ta labarai da zantuka kan halin da Nijeriya ke ciki, ta hanyar fayyace gaskiya komai ɗacin ta. Za mu yi amfani da alƙalamin mu mu yaƙi masu yaƙar ƙasar mu ta muggan hanyoyin da suka fito da su na ganin bayan mu don su gina kan su. Haka kuma za mu kare dukkan haƙƙoƙi da ’yancin da kundin tsarin mulki da sauran yarjeniyoyi na ƙasa da ƙasa suka ba kowane ɗan’adam a duk inda yake. A yayin da muke yin hakan, za kuma mu nishaɗantar da ku saboda an ce rai dangin goro ne, ban-iska yake so. Haka kuma za mu kawo maku nasihohi na addini da tunatarwa ta tarihi domin mu riƙe darajar mu da al’adun mu. A kan wannan, ba za mu gaji ba.


Muna roƙn ku da ku ba mu goyon baya ta hanyar karanta wannan jarida da ba ta talla domin ta ɗore, da ba ta shawarwari nagari, da kuma uwa-uba yi mata addu’ar alheri. Allah ya ba mu sa’a, kuma ya bar mu tare da ku, amin.