Dalilina na ƙin karɓar takardar shaidar cin zaɓe a NNPP – Sanata Shekarau

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana dalilinsa na ƙaurace wa taron miƙa wa  zaɓaɓɓun sanatoci takardar shaidar lashe zaɓen da aka gudanar a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, a makon nan.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Malam Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Tsakiya da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a ƙarƙashin jtsohuwar jam’iyyarsa ta NNPP maimakon jam’iyyarsa ta yanzu, PDP.

Sai dai ɗan majalisar mai ci bai halarci taron miqa takardar shaidar lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun sanatocin ba a ranar Talatar da ta gabata.

Mai magana da yawun Malam Ibrahim Shekarau, wato Sule Y. Sule, ya shaida wa manema labarai cewa, ya riga ya sanar cewa, ba zai karɓi kujerar sanatan ba.

“Mun riga mun bayyana matsayinmu kan lamarin. Sanata Shekarau ba shi da sha’awa kuma ba zai karɓi takardar shaidar lashe zaɓen ba,” inji shi.

Bayan bayyana Malam Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Tsakiya, Shugaban Jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Farfesa Rufa’i Alkali, ya ce Shekarau ya fice daga jam’iyyarsu amma abin takaici sai INEC ta ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen Sanatan Kano ta Tsakiya a maimakon sunan Rufai Hanga.

Tun da fari an shiga ruɗani bayan da INEC ta sanar da Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Amma jam’iyyar NNPP ta bayyana cewar ta aike wa da INEC a rubuce cewar Shekarau ya fice saga jam’iyyar.

Shi ma da kansa tsohon gwamnan na Kano, ya ce, ya sanar da INEC a hukumance game ficewarsa daga jam’iyyar ta NNPP.