Dalilinmu na naɗa hadimin Gwamnan CBN sarautar Ɗan Amanan Bauchi – Sarkin Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu, ya bayyana amana a matsayin wani babban nauyi ne wanda ya jiɓanci kowane bani adam, amma kuma kaɗan ne daga cikin mutane a cikin al’umma suke iya riƙewa.

Sarkin Bauchi ya bayyana cewar, fadar sa ta ɗauki tsawon lokaci tana jimamin wanda ya kamata ya ɗauki ko riƙe wannan matsayi na sarautar Ɗan Amanan Bauchi daga cikin masarautar, sai yanzu da Allah ya bayyana Dokta Ahmad Shehu a matsayin mutumin da ya dace ya riqe amanar, ba masauratar Bauchi kaɗai ba, har ma da jiha, Nijeriya da duniya baki ɗaya.

Mashahurin Basarake Rilwanu Suleiman Adamu yana jawabi ne a ƙarshen makon da ya gabata lokacin da yake karɓar tawagar iyalan Malam Adama, haɗe da ɗimbin masu sarautun gargajiya, ‘yan uwa, abokai, majiɓanta da sauran su suka kai caffar godiya wa sarkin Bauchi bisa naɗi da ya yi wa Dokta Ahmad Shehu a matsayin Ɗan Amanan Bauchi na farko a masarautar.

Sarkin na Bauchi ya kuma nuna matuƙar farin cikin sa da ire-iren rawa da masu riƙe da sarautun gargajiya a masarautar sa suke takawa na wanzar da zaman lafiya tsakanin al’ummai daban-daban da kyakkyawan zamantakewa a tsakanin juna, kana ya yi wa sabon Ɗan Amana murna da samun wannan matsayi, tare da addu’ar Allah ya yi masa jagoranci bisa wannan babban nauyi da ya rumguma.

Da yake yi wa manema labarai jawabi, jim kaɗan bayan ziyarar godiyar ta zuwa fada, Ɗan Amanan Bauchi, Dokta Ahmad Shehu ya bayyana cewar, karimcin ɗaukar wannan nauyi da aka ɗora masa ba ƙaramar ɗaukakawa da darajanta wa ba ce, domin kamar yadda ya ce, ita kalmar amana ta samu asali ne daga harshen larabci ƙarƙashin shara’ar addinin Musulunci, sai ya yi wa sarkin Bauchi godiya bisa wannan zavi da ya yi masa.

Dokta Ahmad Shehu, wanda a halin yanzu yake riƙe da matsayin mai bai wa gwamnan babban bankin tarayya (CBN) shawara akan lamuran asibiti da tallafi wa kiwon lafiya, ya bayyana cewar, sarautar Ɗan Amana wani babban ƙarin nauyi ne aka ɗora masa akan wacce yake da ita na sana’ar sa ta likitanci, yana mai addu’ar Allah ya ba shi zarafin ɗaukar wannan nauyi.

Ɗan Amana ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar cewa, da goyon bayan masu ruwa da tsaki, ‘yan uwa, abokai majiɓanta da ɗaukacin jama’a, haɗi da zage damtse, Insha Allahu zai kai ga sauke wannan nauyi bisa sadaukar da kai, lumana, da yakana.

Ya kuma bai wa sarkin Bauchi tabbacin cigaba da darajanta bani-adam, masarautar Bauchi, da kuma riƙe amanar da aka ba shi, ya ƙara da cewar, ‘Ina son qara wanzar da haɗin kai, aiki tuƙuru wa jama’a, da kuma girmama masarautar Bauchi.

“Akwai buƙatar dukkan mu, mu jingina jikin tawali’un sarki, tare da ba shi dukkann goyon bayan da ya dace, mu goyi bayan masarautar sa, da zummar ganin an ƙarfafa matasa da nusar da cigaban masarautar Bauchi fiye da yadda take a baya, haɗi da share duk wata tankiya da rashin fahimtar juna a tsakanin mu domin mu yi wa masarutar aiki.

Daga nan sai Ɗan Amana ya nemi haɗin kan jama’a su mara wa sarkin Bauchi ta yadda zai sauke nauyi da Allah ya ɗora masa, haɗi da ƙarfafa matasa ta yadda za su samu sana’o’i da ayyukan yi, la’akari da cewar, shiyyar Arewa maso Gabas ita ce mafi koma bayan shiyyoyin ƙasar nan.

Ɗaya daga cikin makusantan Ɗan Amana, Malam Mohammed Bose ya shaida wa manema labarai cewar, Ahmed Shehu mutum ne mai riƙon amana, haziƙi, kuma jajirtacce akan dukkan abinda ya sanya a gaba.

Bose ya bayyana cewar, la’akari da kamanta gaskiya, riƙon amana, da amincewa ne ya sa sarkin Bauchi ya ba shi wannan matsayi ko sarauta ta Ɗan Amanan Bauchi, wanda shine na farko a cikin tarihin masarautar Bauchi, sai ya yi masa murnar samun wannan muhimmiyar sarauta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *