Dandalin shawara: Ba na sha’awar namiji sai mace ‘yar’uwata

(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Good morning, my darling aunty Asas. How was your night? Sorry na yi kiran ki tun da safe, daga baya ƙawana ta ce, ai saƙo zan tura. Mun tava haɗuwa da jimawa, but I think you will not remember, saboda an jima, kan case na wata ƙawata da har ki ka je gidansu about her been raped. Yanzu ma wurinta na samu your number. Matsalata gaskiya I will be honest with you tunda mafita nake nema, wallahi ba na sha’awar namiji gabaɗaya, irin na fi feeling Ina buƙatar mace idan na yi sha’awar abin, amma fa ban tava yi ba, kawai irin ko a mafarki da mace nake gani na, kuma idan na yi tunanin aure matuƙar na tuna da namiji zan zauna sai auren ya fice daga raina. Ki taimaka min da shawara please don na fahimci kina da fahimta tun ma ga yadda kin yi dependiing friend ta a gaban iyayenta a nata case. What can I do, Aunty Asas?

AMSA:

Addinin Musulunci ya ce, idan mace ta balaga, daga gwiwarta zuwa sama ya haramta ganin shi ko da ga mace ‘yar’uwarta, mahaifiyarta ce kawai bai zama haramun da ta ga cinyarta ba, wasu malamai suka ce ita ma bisa ga dalili.

Kuma idan balagagun mata za su kwanta a tare, to su bada tazara da juna, kada su dinga kwanciya irin ta ma’aurata. Akwai fa’ida babba akan wannan hukunci na addini idan muka yi duba da cewa, ita sha’awa abu ce dake motsawa ta sanadiyyar wasu dalilai da yanayi, kuma kamar yadda muka ce a baya, kusanci na ɗaya daga cikin ababen dake iya motsa ta.

Idan muka nisanci juna, muka rufe ido daga kallon tsiraicin juna kamar yadda Musulunci ya tanada, ta yaya sha’awa za ta kutso a tsakanin jinsi ɗaya. Wannan fa bayani ne kan sananniyar hanyar da sha’awar jinsi ke samuwa.

Idan mun koma ɓangare na biyu, wanda shi ma ba abin so ba ne, akwai wasu na’uin aljanu da aka ce wai ana kiransu da ‘Ashiq’, su waɗannan aljanu suna auran ɗan Adam ne kamar yadda aka faɗa, ma’ana mata cikin su na auran mazan bil adama, su ma mazan na auran mata daga cikin mu.

Aka ce, sun kasu kashi biyu zuwa uku. Akwai waɗanda za su hana waɗanda suke tare da su aure na daga mata da maza, wanda aka ce shi ke sa kaga mace ko namiji na gudun aure ba tare da rashin lafiya ba. Sai kuma na biyu na dasa ma sha’awar jinsin da ya zama naka ne kawai, don su ne basa kishi da su.

Aka ce a wannan gaɓar sukan yi qarfi sosai ne idan ka biye wa abin da suka raya ma, wato ka fara kusantar wani daga jinsin naka. Baya ga haka, an ce kana iya haɗuwa da matsaloli da dama ta fuskar abinda za ka iya yin sha’awa a gaba, sakamakon ra’ayin aljanin ne ka ke bi.

Sai na ƙarshe daga ciki waɗanda ba ruwansu da wanda za ka yi tarayya da shi matuƙar ba ta hanyar aure hakan ta kasance ba, ma’ana sun aminta da yin zina. Dukka waɗannan suna da sauƙin magancewa ne idan baka biye wa ra’ayin da suka dasa ma ba.

Sai dai a sha’anin sha’awar jinsi, kaso mai yawa na daga masu yi tsabar son rai ne kawai, ko kwaɗayin abin duniya, ta hanyar tsafi ko biye wa wani don kuɗi, wasu kuma musamman mata suna yi ne a matsayin rage zafi, sakamakon iyayensu sun qi amincewa da su yi aure, a nasu tunanin za su yi ne kawai kafin su yi aure, sai dai abinda ba su sani ba, idan har sheɗan ya yi nasarar ɗaura ki kan wannan hanyar zai yi wuya ya bar ki ki kuvuce, hakan ke sa ga wasu ko bayan aure su ci gaba.

Duk da cewa, akwai matan auren da ke shiga wannan ɗabi’a bisa hujjar mazajensu basa ba su haƙƙinsu. Wannan ma wani aiki ne da sheɗan ke kitsa ma ki a ƙwaƙwalwa da ba shi da maɓulla. Domin shi dai aure na da mafita akan kowacce irin matsala.

Idan ba za ki iya haƙura da raunin mijinki ta wannan fuska ba, ki nemi rabuwa, ki auri daidai ke, domin babu ta inda bin ‘yan hanyoyi za su zama mafita.

Haka ma ta vangaren lafiya, sanannen abu ne akwai cutuka da dama da mata masu irin wannan ɗabi’a ka iya haɗuwa da su, wanda kowacce cuta na da alaƙa da wani abin da suke yi a mu’amalar.

Idan mun koma kan sanadin wannan rubutu, wato shawara da ki ka nema, zan fara da cewa, sai kin fara da canza tsarin ƙwaƙwalwarki tare da horar da zuciyarki kan wannan lamari.

Dama dai an ce, ƙwaƙwalwa da zuciya ne jagaban lamuran gangar jiki. Idan muka bar wa zuciyarmu akalar rayuwarmu, za a wayi gari har ƙwaƙwalwa a ƙarƙashin ikonta ta ke komawa. Kuma idan haka ta kasance, zai zama tamkar ka miqa ragamar rayuwarka ga maƙiyinka ne, duk abinda ya san zai ji daɗi shi zai sa ka, ba ruwansa da halin da za ka shiga bayan ka aikata.

Sheɗan na amfani da waɗannan makamai biyu ne wurin janyo ki ga wannan varnan, ba don komai ba wata ƙila don ya ga ba wata hanyar sai wannan. Kina mafarki da mace ki ka ce, wannan kuma ba abin mamaki ba ne ko kafa hujja, malaman mafarki da na ƙwaƙwalwa sun yi tarayya kan cewa, lokuta da dama mukan yi mafarkai ne daidai da abin da ya dasu a ranmu.

Wasu lokuta mafarki na zama wata hanyar tunatar da mu abinda muke tunanin tuni mun manta da shi. Sau da yawa mukan yi mafarkin wani abu, a zahiri muna ganin ya wuce ko mun fitar da shi daga tunaninmu, sai dai wata alama ce da ke nuni da yana nan lave a wani wuri da zuciya ta kasa hango shi, amma dai yana nan kenan.

Ki tsarkake zuciyarki kan ƙazantar da ta ke raya ma ki, ki dinga tunatar da kanki illa da inda abin zai iya kai ki, sannan ki sanya addu’a a gaba, domin ita ce maganin duk waɗannan dalilan dake janyo irin wannan tunani da ki ke yi.

Addu’a makamin mumini ce, kuma waraka ga kowacce cuta.