Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin kuyanga da ya siya

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Anti Aysha Asas ina yini, ya lamura? Don Allah kar ki ambaci sunana, ko garin da nake. Wallahi na matsu ne, shi ya sa zan fallasa wannan sirrin don Ina son na samu mafita, saboda yanzu kaina ya yi zafi kan lamarin, ban san inda zan fuskata ba.

Ina da shekara sha uku, uwata da kawuna da mai unguwarmu da wanda uwata take zaune gida nai, tana taya matansa aiki, suka shirya da ni, muka taho cikin garin………….da kayana da komai nau. Muka taho gidan wani babban mutum da yake da mata huɗu, sai a gidan wanda uwata take zaune wurin sa ya ce, wai ni baiwa ce, kuma mutumin ne ya siye ni daga hannunsa. Kuma zan zauna da shi matsayin matarshi.

Nan na zauna cikin tsangwama, ba mai shiga sha’anina daga matanshi ko dangi, suna ƙyama ta, ko shi kamar yana voye ni a wajen mutane, bai cika faɗa wa mutane ko ni wacce ce ba. Haka na haihi ɗiya har guda huɗu, sannan kuma Ina zuwa makaranta ta Allah, ana mana karatun Ƙur’ani da sauransu. To shi ne kwanaki mallam yake bayani sai ya yi maganar babu bayi, ɗiya ne ake ta saye, ana zaman zina da su.

Abin ya sha min kai, kuma na rasa wa zan nema da maganar, shi mutumin ya ce karya mallam ke yi, ni kuma na san mallam bai ƙarya. Shi ne na ce bari na nemo ki, saboda neman inda zan kalla cikin rufin asiri. Na gode Anti. (Wannan saƙo ya zo ne ta murya, wato audio).

AMSA:

Daga farko dai zan so mu fara da bayanin bayi; asalin su da matsayinsu, sahihancin ajiye su ga maza har a haifi ‘ya’ya da su, kafin mu kai ga tambayar ko akwai bayi a wannan zamani namu.

Sahihiyar hanyar da ake samun bayi ita ce ta hanyar yaƙi, wato yayin da al’umma biyu suke da saɓani ta fahimta kamar misalin addini, ko suke da hammaya a tsakanin su, ko suke ƙoƙarin ganin sun mallake guraben da abokanen gabar su ke zaune, sukan yi amfani da ƙarfin makami, ta hanyar yin aike, ku fito a kara, wanda ya yi galaba shi ne ke da rinjaye.

A Musulunci, ana ware wurin haɗuwa ne, yayin da abokanin karawa za su nufi filin dagar, su bar ‘ya’ya da mata a cikin muhallansu, waɗanda ya haramta a kai masu farmaki a ciki, wato ko bayan yaƙi bai halasta a bi na gida a kama ko a kashe ba.

Idan aka kara tsakanin alqaryar biyu, dole ɗaya zai yi nasara kan ɗaya, ta hanyar kashe mafi yawa daga ɓangaren da yake karawa da shi, yayin da hakan ta kasance, ragowar masu rai za su yi ƙorafin guduwa don tsiratar da ransu, a daidai gavar ne ake samun bayi, waɗanda suka yi nasara na da damar bin su, su kama, tun daga mayaƙan, zuwa matan da suka ɗauko don kula da waɗanda aka ji wa rauni, zuwa dukiyar da suka zo da ita fagen daga, na daga makamai zuwa kadarori.

Waɗannan da aka kama, za a raba su ga waɗanda suka ciwo wa ƙasarsu nasarar. Mata daga cikinsu mamallakan su za su iya mayar da su masu yi masu hidimar su da iyalansu, ko idan sun so su mayar da su mallakinsu, abinda Ƙur’ani ya ke cewa “abinda damanku suka mallaka,” ma’ana za ku iya kwanciya da su, su haifa ma ku ‘ya’ya, kuma ba tare da kun sanya su a jerin adadin matanku ba.

Daga ƙarahe za ku iya daɗa bayinku mata aure da bayinku maza, sai su haifa maku bayin da za ku iya siyarwa ko riƙe su a matsayin bayin. Ma’ana su tara maku bayi masu yawa. Kuma wannan tsarin zai haifar da halastattun bayi, wato idan bawa ya auri baiwa, to za su haifi bayi ne. Savanin idan ‘yantacce ya yi tarayya da baiwa, suka haihu, domin shi wannan ɗa ne ba bawa ba ne.

Ina ƙara nanata wa, bawa da bawa ne kawai za su iya samar da ɗa bawa, shi kuma mai ‘yanci da baiwa zai haifi mai ‘yanci ne. Dalili kuwa shi ne, dukka zancen mu zai zama bisa motar wannan bayani.

Abu na farko da za mu fara tambaya shi ne, shin yaushe rabon al’umma da sahihantaccen yaqi? Daɗewar shekarun ne zai iya ƙara yiwar vacewar bayi. Domin idan kaso sittin bisa ɗari na bayi mata sun haifi ‘yantattu, arba’in suna haifar bayi, idan sittin ɗin farko suka mutu, kuma an daina yaƙi, adadin bayin zai ragu.

Yayin da kaso arba’in ɗin ko hamsin suka haifi bayin, a cikin kaso ɗarin da suka haifa daga bayin, za a samu wani kaso mai nauyi da za su zama kuyangu, wato su zauna da masu ‘yanci, su rage adadin masu sake haifar bayi. Idan aka juri zuwa da tulu rafi, aka ce wata rana zai iya fashewa. Wato dai bayi za su iya zama tarihi idan aka ci gaba da hakan.

Za mu ci gaba mako mai zuwa.