Dandalin shawara: Matana sun zame min ɓeraye a gida

Manhaja logo

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Malama Aisha sannu da ƙoƙari, ya kwana biyu. Ina ta bibiyar links ɗin da ki ke ɗorawa a ‘status’ na shawarwari da mata ke biɗa da ma ‘yan rubutun shawarwari ga mata. Shi ya sa na ce bari na neme ki don Allah ki yi amfani da damar da ki ke da ita ki ba wa mata shawara kan yi wa mazajensu sata da suka maida ba komai ba. Ai kin san matana biyu ne, amma sun zame min yadda ki ka san ɓeraye, ba halin in aje wando ko riga da ‘yan canji, sai a yi masu rabtau. Kuma an rasa zakara cikinsu, har rige-rige suke yi wurin wawushe ni, kuma kowacce ka tambaya sai ta nisanta kanta da laifin ko ta ɗora abin kan abokiyar zamanta. Wallahi ta kai yanzu indai Ina da kuɗin kirki a jikina, sai na samar masu makwanci kafin in shiga gida. Wani lokacin har sai na koma har gidan Innah na bata ajiya, sannan da safe idan na je dubata in karɓa. Don Allah ki ja masu kunne sosai, ki kuma nuna masu illar aikatawa, don na lura ba su san hukuncin abin ba, saboda abokanaina biyu na ƙorafi irin wannan duk da cewa nasu bai kai irin na nawa gidan ba, su tasu matar ɓerar gida ce, irin ɓeran nan ƙanane masu shegen tsoro da sun ga mutane su ɓace kamar walƙiya. Amma ni nawa sai dai a kira su da ɓeran Chana, manyan nan masu mugunyyar ɓarna.

AMSA:

(Dariya!!!!) Kai jama’a! Allah mai iko!! Abu na farko da zan ce gare ka ne, yallabai, kalamanka ga matanka sun ɗan yi tsauri, kamar yadda aka so mata su tauna halshe wurin faɗin abinda ya shafi mazansu, haka aka so mazan ma game da sha’anin matansu, ma’ana, a mutunta juna akan kowanne lamari.

Abu na gaba, za mu yi tambaya kan hukuncin wannan lamari na ɗaukan kuɗin miji ba tare da yardar sa ba, shin menene hukuncin sa a Musulunce? Idan mata ta ɗau kuɗin mijinta ko mijin ya ɗau na matarsa ba tare da amincewa ba hakan ya halasta ko ya haramta?

Malamai sun tabbatar da cewa, ya haramta mace ta ɗau kuɗin mijinta ba tare da amincewar yin hakan ba. Kuma ya halasta miji ya ɗauka daga dukiyar matarsa koda bata ba shi ba. Sai dai ku dakata daga tsayawa cak! kan wannan hukunci, domin hukunci ne mai iya juyawa ga wasu, ma’ana, akwai inda mace zata iya ɗaukan kuɗin mijinta ba tare da amincewar sa ba kuma su zama halas gare ta. Haka kuma ɗaukan kuɗin mace ga mijinta zai iya zama haramtacce gare shi. Ta yaya hakan zata iya kasancewa?

Idan miji ya kasa sauke haƙƙin da ya rataya kansa na daga ciyarwa ga iyalinsa, kuma ba bisa ga rashi ba, sai don son rai. To, Musulunci ya halasta mata idan ya ajiye ta ɗiba daga ciki don ci da kanta da kuma ‘ya’yanta. Sai dai ba a bata dama ta yi son rai ba, ko kallon wasu buƙatu da ba su shafe shi ba yayin ɗaukar kuɗin kamar ankon biki, ko siyen waya da makamantan su. Ma’ana na abincin da ta san yake daidai ƙarfin arzikinsa.

Anan dole ta ji tsoron Allah a wannan saka hannu aljihu da zata yi, domin Shi masani ne akan abinda yake zukatan bayinSa.

A ɓangaren miji kuwa, idan miji ya zama maƙetaci, bai da fata sai na ganin matarsa ta zama kwalin ashana, ta zama gaba ba ni, baya sai da taimako, ma’ana ya ganta kullum tsiya-tsiya, da wannan ne sai ya ɗaura aniyyar wawashe tanadinta don cikar burinsa.

Ko kuma irin mazan da suke sallama ragamar hidimar gida ga matansu, su ne ci da sha na ‘ya’yansu wani lokacin har da su, amma duk wannan bai ishe su ba, a kullum harin ɗan abin da suke samu suke yi tamkar mage ga ɓera. Da sun ga kafa, sai su yi ram da ɗan abin da matan ke ɗan lailayawa suna samun na rufa wa kai asiri.

Ko kana da mata biyu, ɗaya na samu, ita kuma ɗaya bata neman, sai ya kasance wadda bata neman ne ka fi so, sai ya kasance kana kwaso dukiyar waccan kana ba wa wannan a ƙoƙarin wadata ta tare da karya ɗaya matan. A taƙaice dai sanya ƙeta yayin ɗibar dukiyar matarka zai sauya hukuncin daga halas zuwa haramun.

Abu na farko da za ka fara tambayar kanka, shin ka sauke haƙƙin matanka dake kanka?

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.