Dandalin shawara: Mijina ya ba ni zaɓi; ko gidan da na mallaka ko igiyar aurena

Daga AISHA ASAS 

TAMBAYA:

Assalamu alaikum warahamullah. Sunana…….don Allah Ina neman shawara. Gidan yawa muke, na yi aure da mijina yana da mata biyu, na zama ta uku, kuma bayan ni sai ɗaya ta zaka, mun koma huɗu kenan. Ya’yan gidan gari guda, don su 44 na. Babu zaman lafiya a gidan. Kullum ta sahiya daban da ta marece. Shi ko maigidan in ka kai qara ma ba wani katavus ya ka yi ba. Sai dai idan ta yi masa daɗi ya tara ya yi ta wa’azin da iya bakinshi ne. Ɗiyanshi har sun san ko sun ci mutuncin matar ubansu bai komai, kuma babba sai ya dinga sauke haushin uwar ƙarami kan ɗanta ƙarami ta hanyar zalunci. Matsalolin masu yawa ne shi ne ma ya sa na ke so na tahiya ta wani gida ni da ɗiyana. Ɗan’uwana ya sai muna gida, ya ce mijina sai ya dinga zuwa ran kwanana. Amma fafur ya ce bai yarda, kuma wallahi Asas sauqi ne dukka gare mu, saboda gidan ma matsatse ne, ko isa bai yi, shi ya sa zaman ganin laihi ya yi yawa. To ya ce ba zai bari ba, kuma duk yadda na yi ƙoƙari ya ƙi, wai sai ma cewa ya kai, sai dai ya sake ni. Ki ba ni shawara don gaskiya ban iya barin ɗiyana gidan, don ta tau sakin ne na fi so, albarkacin ɗiyana nika haƙuri. Na gode da saurare na. Sai na ji amsa.

AMSA:

Waalaiki Salam wa rahmatullah. Da farko mu fara da sanin halasci ko haramcin zama gidan mata ga mijinta. Babu ayya ko hadisi da ta haramtawa miji ya zauna a gidan matar da ta kasance tasa, ma’ana matarshi ta aure, don su yi rayuwar aure a ciki. Abin lura a nan shi ne, muhalli haƙƙin miji ne ya ba wa matarsa, yana ɗaya daga cikin wajibban aure, sai dai bai zama wajibi ba dole sai a gidan da miji ya mallaka ne zaman zai kasance ba.

Bari in ba da misali da sadaki da za a fi ganewa, wajibi ne bada sadaki yayin aure, amma sauƙi irin na sha’anin aure, aka ce za a iya yi bisa bashi, kuma matar da za a aura tana da damar ta ce, ta yafe sadakin kwata-kwata kuma auren ya yiwu tamkar na wadda ta karvi sadakinta ta yi amfani da shi.

Haka ma ta ɓangaren muhalli, shi ma wannan sauƙi zai iya kasancewa kuma ba wani abu da zai taɓa sahihancin auren. Don haka zama a gidan mace, wanda wasu Hausawa ke kira da ‘dangana sanda’ bai zama haramun ba, kuma bai zama mai wata illa a Musulunci ba.

Idan mun koma a ɓangaren kallon da ake yi wa ‘dangana sanda’ a Ƙasar Hausa, za mu iya kiran sa da abun qi, musamman a tsakanin alƙaryar da ba ta da wayewa ta addini da kuma zamani. Idan namiji ya tare a gidan da yake mallakin matarshi, mutane na masa kallon wanda zuciyarsa ta mutu, ko makwaɗaici, don haka a idon mutane da yawa wannan zai iya zubar masa da ƙima da darajar da a baya yake ba shi.

Wannan ke sa a wasu ko sun so yin rayuwa a gidan matansu, suke ja baya, don gudun kallon da al’ummarsu zata yi masa. Sai dai a ɓangaren wasu, su da kansu ke hana kansu, dalilin kallon yin haka a matsayin gazawa, ko matan nasu za su rena su idan suka waye gari suna rayuwa a gidan da suka mallaka. Da wannan za su iya hawa dokin na qi koda kuwa ba sa cikin rashin ilimi kuma ba su a jerin waɗanda ɗabi’ar al’ummarsu ta yi wa dabaibayi.

Da wannan za mu tafi kan sanadin wannan dogon sharhi, wato rashin amincewar mijinki ga buƙatar komawa gidan kanki. Abu na farko da nake so ki sani, ko in ce in hankaltar da ke shi ne, babu inda ya zama dole ko wajibi mijinki ya amince da buƙatarki, dalili kuwa biyu ne, na farko babu wata yarjejeniya da ke tsakanin ku tun kan aure na ba za ki zauna a gidanshi ba, don haka babu cin amana ko rashin cika alƙawari tsakaninku.

Abu na biyu, idan ya amince da yin hakan, to ya kyautata, ya tausaya, kuma hakan abu ne da addini ya so ya aikata matuƙar dai ba wata illa ko ɓarna ta bayyana ga yin haka ba. Kuma rashin yin bai zama laifi ba. Idan kuwa haka ta kasance rarrashi ne kawai hanyar warware wannan matsala.

Shawara ta ta farko ita ce, kada ki bari wannan matsala ta zama sanadin da ki ka kashe aurenki, idan kin yi hakan, tamkar kin yi butulci ga ni’imar da ya mallaka miki. Tambayar da za ki yi wa kanki, da ba ki samu gidan ba, za ki kashe auren?

Ba kowanne lokaci saki yake zama mafita ba, asali ma lokuta da dama saki na yin varna fiye da gyara, don haka zan so ki janye saki daga cikin zavin da ki ke da su. Aure ibada ne, kuma abinda muka sani, ibada bata cika zo wa da daɗi ba, kasancewar kewaye ta ke da ababen da zuciya bata cika so ba.

Idan ka ɗauki rayuwar aure ga mata, kaso mai yawa na matan jarrabawar duniyar su na gidan aurensu, kaɗan ne daga cikinsu ake jarrabtawa kafin aure, don haka sai rayuwar aure ta zo masu da sauƙi. Za ku iya amincewa da zance na idan kun yi duba da cewa, ko a taron biki mata ke bajekolin matsalolin gidan aure, za ku tarar kowa da irin ta ta, zai yi wahala kiga wadda bata da ta faɗa. 

Don haka matsalolin gidan aurenki ruwan dare ne, har akwai waɗanda suka fi ta ki, amma ba na ce, dole sai kin yi haƙuri ba, domin ita rayuwar aure bata da tilas. Amma dai haƙurin shi ne ya fi, idan har lahira ki ke duba ba duniya ba.

Abu na biyu, tunda dai bai zama dole ba, zan ba ki shawarar ki kwantar da kanki don kina neman abinda bai zama wajibi ya amince ba, don haka ki yi guzurin haƙuri da rarrashi wurin neman biyan buƙata, sannan ki yi tunanin saka waɗanda yake jin maganar su idan har ‘yan dabarun matan sun bada ke. A yi ta yi, ana tushi tare da addu’a har a kai ga nasara.

Daga ƙarshe, Ina so ku sani mata, lokuta da dama mu mata da kanmu mu ke zame wa ‘yan uwanmu mata matsala, ta yadda muka yi wani zaman aure ne zai taimaka wurin hana wasu samun irin damar da ku ka samu, sanadin sun kasa shanya garinsu daidai a lokacin da suka samu rana, don haka sai su zama izna ga maza da ke sa su hau dokin na ƙi ga matansu sakamakon sun ga wasu sun yi ba su sha da daɗi ba.

Allah Ya kawo ma na mafita.