Tare Da AISHA ASAS
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Sunana……….daga……….. Na samu number daga hannun……..Dalilina na neman ki dai shi ne, abokina ne shi, na sanar da shi matsalar da nake tare da ita, sai ya ba ni number ki ya ce, na ma ki magana, wai kwanaki ma ke kin ka kashe matsalarsa da mai dakinsa.
Wato mata nake da ita, kuma har ga Allah Ina masifar san ta, wannan ya sa nake kishinta ƙwarai da gaske. Ban rage ta da komai ba, duk abinda na mallaka zata iya iko da shi.
Kuma ta ɓangaren kwanciyar aure daidai gwargwado ina duba buƙarta, har littafai da videos da ake yi na yadda za a gamsar da iyali nake ɗan bibiya duk saboda ita. Ina kula da ƙarfin gabana dan kar na gaza mata. Amma a ‘yan watanni uku baya, na dawo gida ba zata, dan lokacin tashi kasuwa bai yi ba, shi ne na tarar da matata da wani abokina suna kwance a gadona yana amfani da ita.
Da idona biyu na gan su hajiya Aisha ba wani ya sanar da ni ba, amma abinda ya ba ni mamaki duk zafin kishin da nake da bai sa na hau kansu ba, Ban shaƙe wuyan shegen abokin nawa ba.
Asalima har ture ni ya yi lokacin da yake ƙoƙarin guduwa daga ɗakin. Dalilin nemanki dai shi ne, yanzu haka matata na cikin gidana, duk da cewa zuciyata ta yi mata tsana mai tarin yawa, na qyamace ta, ko hannunta ba na son riƙewa, kai in kai zancen ƙarshe har raina na tsani zama da ita, na cire ta a layin matan da nake so, ba ni da buri sai na ta bar min gidana, Dan ba zan iya zaman aure da ita ba, amma fa na kasa sakin ta, na kasa yi mata masifa kan abinda ta aikata.
Abinda ya ƙara ɗaure min kai jiya shi ne, ta same ni ɗakina ta nuna buƙatar na kusance ta, duk da zuciyata ta tsani haka, amma haka na yi, amma cikin tursasawa, yanda na ji tamkar wanda aka aza wa bindiga ko ya yi, ko a harbe shi.
Abin kullum damuna yake yi, wallahi na tsani zama da ita, kuma har yanzu da nake turo miki wannan ‘audio’ na tsani zama da ita, kuma Ina so na sake ta ko raina zai daina raɗaɗi, sai dai wallahi na kasa.
Jiya fa bayan mun gama har takarda na ɗauko da biro, wai tunda ban iya furtawa, na rubuta, sai na nemi abin rubutawar ma sama da ƙasa na rasa.
AMSA:
Na gaba kuwa shi ne, yawaitar faɗuwar gaba yayin da ka haɗu da wanda sihirin naka ya shafa. A wannan ya shafi sihiri na dasa ƙiyayya ko soyayyar da babu ta a can baya.
Akwai rashin kwanciyar hankali marar dalili, ta yadda za ka nemi natsuwarka ka rasa, ba wai don wani abu ya same ka na tashin hankali ba ko don kana tare da wata damuwa ba.
Akwai mugayen mafarkai, waɗanda za mu iya cewa suka saɓa wa ire-iren mafarkan da ka saba yi, kuma suna yawan maimaita kansu, ma’ana za ka dinga ganin kusan abu guda a cikinsu.
Sai dai wannan ya fi ga waɗanda aka yi wa turen aljanu don su zauna tare da shi.
Alamomin suna da yawa, domin sihirin ya karkasu da dama, kamar yadda buƙatar mai yin sihiri ta bambanta, kamar na neman soyayya ko ƙiyayya, rabuwar aure, mallaka, na hassada wanda ake illata mutum, kishi wanda yakan iya kai ga hauka ko rabuwar aure da makarantan su. Don haka wuri da muke da shi ba zai ba mu damar zayyano su daki-daki ba tare da musababbinsu, sai dai da ɗan guntun bayyanin da aka yi za ka iya samun amsar ko shi ne ka ke tare da shi.
Idan ka samu tabbacin sihiri ne, to kana da hanyoyi biyu; ko dai ka nemi malami na ƙwarai ya ba ka magani, wanda a halin yanzu yake da matuƙar wuyar samu a ɓangarorin masu bada taimako irin na magani, domin da yawa kwaɗayin abin duniya ya rufe masu ido, suna amfani da ƙuncin wasu wurin samun abin duniya ta hanyar shirya ƙareraki da zai sa ka yi ta narkar kuɗi ba biyan buƙata.
Amma idan ya kasance ka san wanda ka yarda da shi, to shi ne zai yi amfani da ilimin addini da yake da shi wurin samar ma abinda zai karya asirin bisa turba ta sunna.
Hanya ta biyu kuwa ita ce mafi sauƙi, kuma mai saurin rugujewa idan ba ka yi yaƙini da ita ba. An ruwaito cewa, za a iya amfani da ganyen magarya, tsaftaccen ruwa irin na rijiya da kuma ayoyi daga littafi mai tsarki wurin karya asiri. Ta yaya?
Za a samu ganyen magarya guda bakwai, a tanadi ruwa mai tsafta kuma mai tsarkakewa. Za a daka wannan ganyen sama-sama, sai a zuwa ruwan wanda kwatankwacin su zai iya kai ƙaramin botiki.
Za a zauna a riƙe mazubin da hannu, idan da hali a kalli gabas, amma ba dole ba, sai a sunkuyar da kai ga ruwan, ta yadda numfashin mai karatu zai iya isa ga ruwan, sannan a karanto waɗannan ayoyin; suratul Fatiha, Suratul Baqara aya ta ɗaya zuwa ta biyar, da kuma aya ta 102-103, da aya ta 163-164, aya ta 255 – 257, sai 285-286. Suratul Al’Imraan aya ta 18-19. Suratul A’araf aya ta 54-56, sai aya ta 117-122. Suratul Yunus, aya ta 81-82. Suratul Taaha, aya ta 69. Suratul Mu’umineen, aya ta 115-118. Suratul Namli, aya ta 50-53. Suratul Furqaan, aya ta 23. Suratul Saffaat, aya ta 1-10. Suratul Ahqaf, aya ta 29-32. Suratul Rahman, aya ta 33-36. Suratul Hashri, aya ta 21-24. Suratul Jinn, ayah ta 1-9. Suratul Yaseen. Suratul Fill. Suratul Ikhlaas. Suratul Falaƙi. Suratul Nas.
Kowacce sura idan za a canza ana farawa da isti’aza da kuma basmalla. Sannan numfashin na shiga a ruwan. Bayan kammalawa, za a dinga ɗibar ruwan ana sha, sannan a yi wanka, kuma wankan tun daga kai, har ƙafa su samu, ba lallai sai ka jiƙe jikin sosai ba, sai dai za a yi wankan ne a wuri mai tsafta ba bayi ba, idan an gama, sai a zubar da ruwan a wuri kamar ga itatuwa ko makamantansu, wurin dai da babu najasa.
Ana maimaita wannan ne tsayin sati biyu, kuma da yardar mai dukka matsala ta sihiri da ke jikin zata zama tarihi, matuƙar an yi da yaƙini. Allah ne masani.