Dandalin shawara: Shekara tara da aure, mijina bai taɓa kusanta ta ta sananniyar hanya ba

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Don Allah ki taimaka min da shawara. Ni dai daga ƙauyen……..na aiko da wannan saƙo. Ina da shekara 13 aka yi min aure, kuma ni ban san komai da ake yi da namiji ba. Da ya zo kusanta ta ta farko sai ya yi ta baya. Ban gane ba don na ɗauka haka ake yi. Haka ya yi ta yi har muka yi shekara shida, uwaye na ta ƙorafin ban haihuwa. To sai ya zamana na fara samun matsala a ta kashi na, idan tusa ta zo min nai ƙoƙarin hana ta fita sai na kasa, kuma Ina yin ƙoƙarin matse ta. Da abin ya dinga sani kunya sai na gaya ma shi, sai ya ce, ai basiri ne zai samar min magani. Bayan wasu shekaru kamar uku zuwa huɗu sai kuma na ƙara samun wata matsala. Idan Ina ciwon ciki, Ina gudawa, sai in ta yin sa a jikina, saboda Ina kasa riƙe shi idan ya taso. Ranar dai sai na fara tunanin ko dai wani ciwo ke tare da ni. Ba na mu’amala da mutane sosai don ba ya so, don haka ba ni da ƙawaye, sai dai muna hulɗar mutunci da wata maƙwabciyarmu ta yamma da mu mai suna……….don ita kan shigo idan ba ya nan. Ranar dai da batun zuci ya yi min yawa, sai na tambaye ta ko ita tana fama da irin matsalar da nake da ita, sai ta ce a’a. A nan ta ce na hanzarta zuwa asibiti don kar ya zame min irin matsalar masu kwana da maza ‘yan’uwansu. To abin sai ya sha mun kai, tsayin kwanaki Ina tunanin abinda ya haɗa ni da waɗannan mutane. Bayan kwanaki na kasa samun sukuni, sai rannan na tambaye ta wai ta ina ake kusantar mace. Ta yi dariya ta shiririce maganar har bayan kwanaki na sake tambayar ta, da taga da gaske ne, shine ta min bayyani wanda ya sava wa inda yake min. Ban voye mata komai ba na gaya mata. Ita ta taimaka min na saci jiki bayan ya fita muka tafi asibiti don ba ya barina zuwa asibiti. Nan ne fa likita ta min ƙarin bayani. Da na yi masa bayani ya hau ni da faɗa, har da barazana. To ita wannan makwabciyata ce ta ce na neme ki a Fesbok tunda wayata tana yi, ita ma ta yi yadda ake yin magana da mutane don ban tava yi ba. Ta gaya min za ki ba ni shawara don ita ma tana turowa. (Allah Ya sa na samo rubutun yadda ya kamata, kasancewar rubutun da aka turo ya ɗan yi wuyar karantawa).

AMSA:

Idan mun koma ta ɓangaren lafiya, wannan ɗabi’a mahalaka ce ga ‘ya mace, domin babu tantama tana lalata ta kashin mace, tana raba wurin da ƙarfinsa, tamkar dai misalin wandon roba ne, idan mai jiki sosai ya jure saka shi, za a wayi gari ya buɗe daidai da girman mai sa shi, saɓanin baya da yake a matse sai an buɗe. Wannan zai sa idan abin ya yi ƙamari a koma saka nafkin na manya, sakamakon rashin iya ja wa kashi birki idan ya yunƙuro.

Baya ga wannan, an tabbatar mace za ta iya haɗuwa da cututtuka da dama daga wannan ɗabi’a, wasu daga cikinsu alamomin su kan fara ne daga yawan jin wari na fita daga wurin, sanadiyyar maniyin da ke zama muhallin da ba na shi ba. Ko wannan kawai zai iya haifar da matsala ta yawan jin ƙaiƙayi a wurin, wani lokacin har da fitar tsutsa lokaci-lokaci.

Shi kansa namiji wannan ɗabi’a na haifar masa da matsaloli da dama da za su iya zama barazana ga lafiya ko rayuwarsa bakiɗaya.

Ya ke ‘yar’uwa mai tambaya, Ina so ki fara da sani kan wannan mummunar ɗabi’ar da mijinki ya kwashe shekaru yana yi maki, don ga dukkan alama kina da ƙarancin ilimi, ki sani an hallaka al’umma sukutun don aikata irin wannan laifi. Labarinsu na cikin ayoyi da dama na cikin Ƙur’ani mai tsarki; Suratul Aaraf:80-84, Hud:77-83, Hijr:57-77, Anbiya:74-75, Shuara:160-175, An- Naml:54-58, Ankabut:28-35, Saffat:133-138 da kuma Suratul Ƙamar:33-39.

Idan mun koma ɓangaren neman shawara da ki ke yi, lamarinki mai sauƙi ni, da ace kin nemi sanin ilimin addininki. Babbar musibar da ta fi komai damun kaso mafi yawa na Musulmai ita ce, rashin sanin addini, da kuma ƙin damuwa da tambayar malamai kan wasu sha’anoni da suka shige mana kai, domin addinin Musulunci wayayyen addini ne, bai bar komai a rufe ba.

Hadisi ya tabbata daga manzon Allah cewa, babu ɗa’a (yin biyayya) ga abin halitta (mutum) wurin saɓa wa mahalicci (Allah).

Idan kin fahimci wannan hadisin za ki gane cewa, zancen yadda za ki yi a bayyane yake, domin Allah Ya haramta zaman aurenki da mijinki matuƙar dai zai ci gaba da kusantar ki yadda yake. To ya addini ya ce, ku rabu? Ya tabbata daga malamai cewa, idan ɗaya daga cikin ma’aurata ya zo da wata alfasha a alaqar aure, ana farawa da yi masa nasiha, don ya san haramcin abinda yake aikatawa.

A nan idan da jahilci yake abin to sai ya samu haske ya dena. Idan har ya sanya wa idonsa toka, ya bijire daga nasiha da lurarwa da malamai ko wani makusanci ya yi masa, sai mataki na biyu, wanda shi ne zai zama hukuncin ƙarshe, wato raba auren, ko ta ɓangaren iyaye ko ta ɓangaren hukuma ta Musulunci.

Kuma yana da kyau ki sani, irin wannan sha’ani na ki ba ya buƙatar biyan kuɗin fansar kai, wato ‘hulu’i (mace ta biya mijinta kuɗi don ya sake ta).

Saboda Allah ne Ya ce a yi, don haka ba ra’ayin ki ne kawai ki ke bi ba, domin da zai dena, za ki iya ci gaba da zama da shi.

Za ki samu wani daga cikin makusantan shi, wanda yake jin maganar shi, ki sanar da shi halin da ki ke ciki, a wannan gaɓar kina da zaɓi biyu, idan kin san zama gidan zai zama wata hanya da zai ci gaba da aikata wannan alfasha da ke, to an ba ki damar barin gidan don kaucewa faruwan saɓon Allah, har zuwa lokacin da za a ji matsaya daga gare shi.

Idan kuwa za ki iya hana shi, zaman gidan zai fi har sai ranar da ya fahimci gaskiya ko kuma ya bijire wa gaskiyar. Wannan zai sa idan bisa ga jahilci yake yi, zai farga, ya tuba, ba tare da asirin ku ya tonu ba.

Abu na ƙarshe, ki sani, yanzu da ki ka sani, amincewa mijinki ya kusance ki ta wannan hanyar zai kasance laifi da ki ka aikata ke ma, domin kin ji hukuncin, don kin wuce zamanin rangwame ta dalilin rashin sani. Allah Ya sa mu a layin bayinSa masu taka-tsan-tsan kan lamarin addini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *