Dandalin shawara: Wanda na sani a matsayin uba ke ƙoƙarin yi min fyaɗe

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Salam. Ina yini. Don Allah wanga shi ne karo na uku Ina turo mi ki da tambayata, sai dai ban ji ke ce komai ba. Allah ba da wasa ni kai ba. Don Allah ki taimaka. Tun Ina da shekara tara, akwai wani ɗan’uwan babana da bai tava haihuwa ba, sai matatai ta nemi a bata ni ta riƙe. Ita lauya ce, kuma tana aiki. Tun da suka ɗauke ni, ba su tava nuna ba su suka haihe ni ba, ba ma kamar matar, saboda ni kaina wani lokaci har shagala ni kai kamar ita a uwata, don irin kulawa da ta ke mani. To yanzu na girma, kuma ita ma ta samu haihuwa har da yawa, amma bata taɓa canza min ba. To yanzu shi mai riƙon nau ne kamar kar in balaga, ya fara jawo ni jikinshi sosai, ya ce in ma shi tausa, ko in dinga shafa mai ƙafafu da hannuwa. Tun abin bai damu na har na fara. Bayan na gaya ma abukiyata ta ce ko ya ce in ƙi yi, to daga nan idan matar bata nan sai ya dinga shigowa ɗakina, yana yi min baganar tambaa, ni ko sai in ta kuka, ranan ma riƙe ni ya yi, ya cire min riga, qarar motar matar ta cece ni. To kullum sai ya ta yi min daɗin baki. Kuma shi babana idan ya zo kullum cewa yakai kar in sava mai. To ni yanzu ban san yadda zan yi ba, matar bata gane ba, saboda kullum ni ɗiyarta ta ta ke gani. Mamata ta rasu, kuma gidanmu kullum yabon irin riqon da sukai min akai. Kuma har ga raina Ina ma matar kallon uwa da ba ni da irin ta. Kuma Ina tsoron ta tsane ni in na faɗa mata. Ki taimaka min da shawara don Allah.

AMSA:

Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa riƙo ya yi wuya a wannan zamani, ko in ce a tsakanin Hausawa shi ne, duk yadda ka riqe yaron da so da kulawa, mutane za su yi amfani da wasu ababe da ka yi masa da cewa, don ba yana ɗan cikinka ba. Sau da yawa wannan kan hana wasu ɗaukar ‘ya’yan ‘yan uwansu su riƙe, musamman ma waɗanda suke raye, domin sai a je neman danƙon zuimunci a samu lalacewar sa.

Wannan bai tsaya iya iyayen da suka bada riƙon ba har su kansu yaran, sau da yawa sheɗan na yin tasiri wurin yawan tunatar da su ba iyayensa ba ne, don haka sai ya samu wani abu da suka yi masa ya danganta da riqon, wanda sheɗan ɗin ba zai bari ya manta ba. Wannnan ke sa kaga ka yi wa yaro riƙo daidai da iyawarka, sai ya girma kaga sauyi daga gare shi, musamman ma idan ya yi arziki kai kuma ba ka da shi.

Ba wai na ce ba a samun iyayen riƙo da ke cin zarafin yaran da suka ɗauko ba, akwai su da dama, kuma suna bada gudunmuwa babba wurin samar da gurɓatacciyar al’umma ta hanyar cin zarafin yaran da kuma rashin ba su tarbiyyar da suke buƙata don zama manyan gobe nagari.

A na ki ɓangare kina da zaɓi guda biyu, ko in ce ɗaya cikin biyu, ya danganta da yadda ki ka fahimci uwar ɗakin taki. Idan kina ganin tana layin matan da suke bin mazajensu ido rufe, ma’ana bata yarda da duk abinda aka sanar da ita game da mijinta, ko yana da baiwar iya janyo ta ga nasa ra’ayi akan komai, to dole sai kin samar da hujja da zata sa ta amince da kalamanki, ta kuma hana maganganun mijinta tasiri, domin duk a cikin mutanen da ki ke kewaye da su, Ina so ki sani, ba ki da mafita idan ba ita ba.

Idan hakan ta kasance, a matsayinki ta mai ƙarancin shekaru, zan ce ki samar da naɗin sautin muryarsa a lokacin da yake ma ki irin waɗannan kalamai, ma’ana ki yi amfani da wayarki cikin dabara ki yi ‘recording’ ɗin kalaman nasa da yake furta ma ki bayan matarsa ta fita, sai ki je ki yi mata bayanin komai, daga biri har wutsiya ki fere mata, ba ƙarya ba kuma ragi, sannan ki gabatar mata da hujja da zata hanata kokwanton kalamanki.

Matuƙar soyayyar da ta ke maki ta kai yadda ki ka ce, za ki sha mamakin irin kariyar da zata ba ki, zata ɗauki matakin da zai hana ki faɗawa tarkon shi, wanda ba wanda zai iya ba ki kamar nata, don ta fi kowa sanin sa, kuma ba macen da ta ke son mijinta ya yi wa wata fyaɗe, ko kishiya ma ya aka kaya bare fyaɗe, ko fyaɗen ga ‘yar da ta ɗauka tata.

Idan kuwa kin san mace ce mai fahimta, kuma ta yarda da gaskiyar ki, ma’ana bata shede ki da ƙarya ba, kuma tana iya bambance gaskiyar mijinta da ƙaryar sa, to zan ce ki tunkare ta gaba-gaxi ki sanar da ita halin da ki ke ciki.

Daga ƙarshe zan so in tunatar da ke cewa, a halin da ki ke ciki jinkiri ba na ki ba ne, a bari ya huce shi ke sa rabon wani ya shiga, kamar yadda hausawa ke faɗa, a na ki ɓangare idan ki ka bari ya huce, rabon wani da zai shiga, zai taɓa rayuwarki har abada.

Fyaɗe abu ne mai matuƙar muni ga wadda aka yi wa, munin sa a tsakanin Hausawa kuwa ya fi yawa, domin sau da yawa suke tattara laifin su ɗaura ga ita wadda aka yi wa, alhali ba ta da dama ko ƙarfin hanawa. Don haka ki yarda da ni idan na ce ma ki duk wanda zai ga laifinki ko zagin ki, mai sauƙi ni idan kin kwatanta shi da halin da za ki shiga bayan ya ɓata rayuwarki.

Zance na rufewa kuwa shi ne, ki riƙe addu’a, ki nemi tsari daga wanda Ya yi shi, Ya yi ki, ki nemi taimonSa wurin kawo sauƙi yayin warware wannan matsala. Tabbas zai ba ki kariya, kuma zai kawo ƙarshen lamarin cikin sauƙi.

(Ina kira ga maza masu ɗabi’ar fyaɗe da su ji tsoron Allah. Komai zai iya faruwa yayin da ka zo yi wa mace fyaɗe, za ka iya yi mata illar da zai hanata yafe ma a gaba ko ka yi nadama, ko ma ta rasa ranta ba ta inda za ka ganta ka bata haƙuri. Kuma kamar yadda ku ka sani, Allah ba ya yafe wa wani laifin da ya yi wa ɗan’uwansa, sai dai shi ɗan’uwan nasa ya yafe masa.

Kuma shi wannan abu ƙaiƙayi ne da yake komawa masheƙiya, yaya za ka ji a lokacin da aka yi wa ƙanwarka ko ‘yar cikinka abinda ka yi wa ‘yar wani? Wallahi ba ka da wata hanyar iya ba wa iyalanka kariya a lokacin da irin wannan sakaya ta dawo ramuwa, ko da kuwa za ka adana su cikin tandun kwalli.

Me zai kai ka ga tursasa wata mace ba ka kanta, alhali duniyar cike ta ke da matan da ke zubar da ƙimar su, wasu ma su ke neman mazan. To me zai hana idan ma zinar za ku yi, ku nemi irin waɗannan mata da suka zubar da mutuncinsu, cikin amincewar su, ku ƙyale salihai da ke ƙoƙarin kame kansu.

Wallahi Allah ba ya barin azalumi ya ci bulus, kuma fyaɗe na ɗaya daga cikin manyan zalunci da za ku iya aikatawa. Kuma ku sani rana na zuwa da Allah zai kamaku akan abinda ku ka aikata ga bayinSa mata, kuma kamun Allah ya wuce duk wani tunani na ku).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *