Dandalin shawara: Wanda na sani a matsayin uba ke ƙoƙarin yi min fyaɗe

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Salam. Ina yini. Don Allah wanga shi ne karo na uku Ina turo mi ki da tambayata, sai dai ban ji ke ce komai ba. Allah ba da wasa ni kai ba. Don Allah ki taimaka. Tun Ina da shekara tara, akwai wani ɗan’uwan babana da bai tava haihuwa ba, sai matatai ta nemi a bata ni ta riƙe. Ita lauya ce, kuma tana aiki. Tun da suka ɗauke ni, ba su tava nuna ba su suka haihe ni ba, ba ma kamar matar, saboda ni kaina wani lokaci har shagala ni kai kamar ita a uwata, don irin kulawa da ta ke mani. To yanzu na girma, kuma ita ma ta samu haihuwa har da yawa, amma bata taɓa canza min ba. To yanzu shi mai riƙon nau ne kamar kar in balaga, ya fara jawo ni jikinshi sosai, ya ce in ma shi tausa, ko in dinga shafa mai ƙafafu da hannuwa. Tun abin bai damu na har na fara. Bayan na gaya ma abukiyata ta ce ko ya ce in ƙi yi, to daga nan idan matar bata nan sai ya dinga shigowa ɗakina, yana yi min baganar tambaa, ni ko sai in ta kuka, ranan ma riƙe ni ya yi, ya cire min riga, qarar motar matar ta cece ni. To kullum sai ya ta yi min daɗin baki. Kuma shi babana idan ya zo kullum cewa yakai kar in sava mai. To ni yanzu ban san yadda zan yi ba, matar bata gane ba, saboda kullum ni ɗiyarta ta ta ke gani. Mamata ta rasu, kuma gidanmu kullum yabon irin riqon da sukai min akai. Kuma har ga raina Ina ma matar kallon uwa da ba ni da irin ta. Kuma Ina tsoron ta tsane ni in na faɗa mata. Ki taimaka min da shawara don Allah.

AMSA:

Lafiya lau ‘yar’uwa. Ina mai ba ki haƙuri kan shiru da ki ka ji, hakan ba zai rasa nasaba da vatan da wayata ta yi ba, watakila saƙon naki na ɗaya daga cikin waɗanda ban samu amsawa ba kafin rabuwata da wayar.

Idan na fahimce ki, uban riƙon ki ne ke neman ɓata rayuwarki, yayin da uwar riƙonki tuni ta sauya kallon da ta ke ma ki na ɗiyar riƙo zuwa fiyar cikinta, wanda watakila ya rufe mata ido daga ganin yuwar mijinta ya yi ma ki irin wannan kallon, saboda tana tunanin yadda ta ɗauke ki, shi ma haka ya ɗauke ki.

A ɓangare ɗaya, ya shimfiɗa kyakyawar fuska ga dangi da zai iya yiwa su ƙaryata ki idan kin sanar da su nufin shi, a wani ɓangare ma, zai iya kasancewa matar tasa ta bi bayan mijinta ba ke ba, watakila idan nasa kalaman sun fi tasiri, wanda hakan zai sa ki samu matsala da ita, wataƙila ma ta yi ma ki tsanar da ba zata so ci gaba da zama da ke ba.

Ɓangare na ƙarshe kuwa, idan kin yi gum da bakinki, ba ki sanar da kowa ba, ba za ki samu kariyar da za ta hana shi cika burinshi kanki ba, kuma idan kere na yawa zabo ma na yawa, wata rana za a haɗu, ma’ana zai iya yin nasara kanki, ya ɓata mi ki rayuwa, wanda hakan ne ya fi duk ababen da na ambata a baya illa, domin bayan faruwar hakan.

Uwar riƙon naki zata iya ƙin naki kamar na farko da na faɗa ko ma fiye, danginki ba lallai su yi ma ki adalci ba, domin za a iya juye abin ya koma kanki, musamman idan aka yi rashin sa’a ciki ya shiga, wanda hakan zai iya faruwa, ga uwa uba rayuwarki da zata samu tabo da ba zai iya gogewa ba.

Dalilin dogon bayanin nawa shine, in sanar da ke yin shiru kan wannan lamari ba inda zai kai ki face ga danasani, don haka duk tsoron ki ga vata alaƙarki da uwar riƙon ki ko dangi, to ki linka tsoron ga rayuwar da za ki yi idan ya yi nasara kanki.

A yadda na fahimta kina da ƙarancin shekaru, don haka zan yi amfani da mafi sauƙin hanyar mafita da za ki iya bi daidai da shekarunki, amma kafin nan zan so tambayar ki wani abu.

Shin da za a ce mahaifiyarki ce ta cikinki, za ki iya sanar da ita mijinta na harin jikinki? Idan kuwa amsar zata kasance za ki sanar da ita, to bai kamata ta sauya ga matar da ki ka ce ta yi ma ki riƙon tsakani da Allah ba.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.